TARIHIN SHEIKH ABUL FATHI MAIDUGURI
Wane Ne Sheik Abul Fatahi Maiduguri? Daga Aliyu Ahmad . Cikakken sunansa shine Sheik Ahmad Aliyu Yarwa amma ana yi masa lakabi da Sheik Abul Fatahi. Ya rayu a duniya shekaru 82, kenan an haife shi a shekarar 1919. Da rasuwarsa yau shekaru 17 kenna, domin ya rasu ne a shekarar 2003. . An haife shi a wani kauye da ake kira Sandiya amma an fi saninshi da Shanduwa a yanzu, a gundumar Konduga ta jihar Borno. A nan ya taso har ya iya hawan doki da al'adun kauye. NASABARSA: Sheikh Ahmad bin Aliyu bin Ahmad bin Aliyu bin Muh'd Mustapha bin Muh'd Mukhtar bin Adam bin Dawud bin Abdulganiyyu bin Zubair bin Abbas bin Hussain bin Suleiman bin Ishaq (ta kan wannan suka hada kaka daya da Sheik Ahmad Tijjani) bin Aliyu Zainul Abideen bin Ahmad bin Muh'd Nafsu-Zakiyya bin Abdullahil-Khamil bin Hasanul-Musanna Bin Hassan bin Aliyu wa Fadima Bintu RASULILLAHI SAW. . Ta bangaren mahaifiya kuwa jikan Yarima Zubairu ne Sarkin Adamawa, sunanta Aishatu bintu Alh Muh'd wa Hauwa'...
Comments
Post a Comment