TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

Tarihin Shaikh Yakubu Yahaya Katsina A Takaice.
Da sunan Allah mai Rahma mai Jinkai. Tsira Da Amincin Allah Su Kara Tabbata Ga Fiyayyen Halitta, Manzon Tsira Da Iyalan Gidansa Ma'abota Shiriya Da Shiryarwa.

Garin, Shekara Da Wajen Da Aka Haifi Shaikh Yakubu Yahaya Katsina.

An haifi Shaikh Yakubu Yahaya Katsina a ranar 15 ga watan Rajab,1376 Hijiriyya (1955 Miladiyya) a Unguwar Adoro da ke gab da Unguwar-madawaki a tsakiyar birnin Katsina.


Mahaifansa.

Maihaifinsa Alhaji Malam Yahaya, haifaffen  karamar hukumar Rimi ne ta Jihar Katsina. Malama Maryam, mahaifiyarsa, 'yar asalin karamar hukumar Mani din Jihar Katsina ce. Ita 'ya ce ga Malam Zubairu, shi kuma Malam Zubairu da ne ga Malam Aliyu, dukansu haifaffun Karamar hukumar Rimi ta jihar Katsina ne.

Iyalansa.

Yanzu haka Shaikh Yakubu Yahaya yana da Mata biyu da 'ya'ya shatakwas: Tara Maza, Tara Mata. Ya aurar da guda Tara (tsakanin Maza da Mata), Yanzu Saura guda Tara.

Karatunsa.

A farkon farawa Malamin ya fara Karatun Allo a wajen Mahaifinsa Malam Yahaya a matakin farko na Ilimi, daga baya ya koma wajen wasu Malamai abokan mahaifinsa ya ci gaba da karatun nasa na Allo. Malaman da ya yi karatun Allon a wajensu sun hada da: Malam Sani, Malam Adamu Unguwar Sararin Kuka da kuma Malam Alti a Unguwar gidan waya. Bayan rasuwar Malam Alti, Shaikh Yakubu Yahaya ya koma da karatun nasa na Allo kacokaf a wajen Malam Salisu Mutumin Jan-geru wanda yake zaune a Unguwar Sha'iskawa a wancan lokacin, daga bisani ne kuma ya koma da karatunsa wajen Malam Aliyu mai 'Yar Makaranta a anguwar ma-dawaki duk a cikin birnin Katsina. Da karatun nasa ya kara nuna, har wayau shaikh Yakubu Yahaya ya sake komawa da karatunsa kacokaf a wajen Mahaifinsa Malam Yahaya, inda ya dora da karatun Littattafan Addini.

Sana'o'insa.

Ganin cewa karatu ba Sana'a ba ne, sai mahaifinsa ya fara dora shi a kan sana'o'i tare da sauran 'Yan uwansa. Shaikh a janibinsa, ya fara da Sana'ar Dinkin Hula, domin dogaro da kansa.

Daga nan kuma Shaikh ya kara da wasu da yin wasu sana'o'i daban-daban wadanda suka hada da: Saida kwan Zabbi, Saida Yalo/Gauta/Data, Saida Rake, abun birgewa har ma da yin Dako a kasuwa a biyashi. Sana'ar ginin Kasa, Noma, Trader da kuma sana'ar gyaran wuta (Electrician) wanda kuma shi ne sana'arshi baya-baya a samartaka kafin Malanta ta janyeshi a shekarar 1969, shehin Malamin duk ya yi su.

Hazakarsa A Makaranta.

Shaikh Yakubu Yahaya Katsina ya kasance Mutum mai kwakwalwa da hazakar gaske, duba da yadda ya yi karatu na Muhammadiyya tun yana karami har zuwa girmansa, wannan ya sa kwalwarsa ta fi karfin karfin Makarantar Firamare har ma da ta Sakanadare a lokacin, sai kawai kaitsaye ya wuce Makarantar gaba da sakandare (tare da cewa bai yi Firamare da sakandare din ba)

Shaikh ya kasance yana daukar matsayin farko 'Distanction' ne a ajinsu, kuma bai ta6a samun abin da ake cewa 'Carry over' a duk Makarantun da ya yi ba, duk da cewa akwai darussan turanci a cikin tsarin abin da yake karanta. Kai in takaice maku masu karatu, Shaikh Yakubu Yahaya sai da ya rubuta Kamus na turanci da na Larabci nashi na kashin kansa saboda nacewarsa akan Yaruka guda biyu; Larabci da Turanci. Saboda tsananani kaifin kwakwalwarsa da haddace abubuwa nan-da-nan, 'yan ajinsu suka sa masu wani suna, suna kirasa da "Computa".

A rayuwar wannan bawan Allah ma'abocin jajircewa, akwai darussa da al'umma musamman Matasa za su koya. Misali: Matasa su kula cewa ba komai ne za su koya ba a aji, domin shi Shaikh Yakubu Yahaya bai zauna a ajin firamare ba amma ya koyi turanci daidai gwargwado, ya iya ya kuma kware da halshen Larabci. Ya samu wannan karatuttuka ne akasari a wajen bincike da yawan Karanta jaridu, Mujallai, jin labarai, karanta littattafai irin na koyi da kanka kamar yadda ya fada da bakinsa.

Fara Wa'azozinsa.
Shaikh Ya jajirce wajen karatu da yada shi duk da a lokacin akwai karancin wadatar kudi da sauran abubuwan da rayuwa ke bukata, domin hatta albashinsa (alokacin yana Malami a ATC kafin a kore shi) bai wuce Naira N150 ba da ake biyansa, amma a haka yake fadi-tashi wajen yin Wa'azi a Masallatai da kuma Makarantu.

A shekarar 1983, Shaikh ya fara daukar lasifika a karan-kansa yana zuwa yin wa'azi ga al'umma shi kadai, a lokacin ma memba ne na Kungiyar Fityanul Islam. Domin a shekarar 1979, a lokacin kungiyar Izala ta kunno kai kuma tana barazana tare da sukar bayin Allah (Waliyyai) da ilimoma na darikun sufaye. Amma a wannan lokaci Shaikh yana cikin wadanda suka bazama wajen bada kariya ga bayin Allah (Waliyya) da kira zuwa ga hanyar Allah tare da hadin kan Musulmi, har zuwa farkon shekarar 1980.

Kar6awarsa Ga Kiran Shaikh Ibraheem Alzakzaky(H)
Haka kuma 6angaren Da'awar Shaikh Ibrahim Zakzaky (H), Shaikh Yakubu Yahaya ya kar6a wannan kira a lokacin kamun da aka yi wa Shaikh Zakzaky (H) a Sakkwato zuwa kurkukun lnugu.

Yadda abin ya faru kamar yadda Malamin ya bayyana da kansa a wata fira da Voice Of Shaikh suka yi da shi yace; "Ina cikin jin rediyo, sai na ji cewa an kama su Malam a Sakkwato. Sai na yi Kabbara nace to yanzu na ga Malami na Allah!"

A haka dai Shaikh Yakubu Yahaya ya yi ta kokarin ganin ya hadu da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) wanda sai a shekarar 19985 wannan burin nasa na ganin Jagora ido da ido ya cika, inda ya hadu da shi a Bayero University Kano (BUK). Daga wannan haduwar ce kuma suka ci gaba da aikin isar da sakon addinin Allah tare a kalkashin "Balligu anni walau ayah."

Alakarsa Da Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky(H)
Alakar Shaikh Yakubu Yahaya da Sayyeed Ibraheem Zakzaky (H) ta yi karfi sosai tun a wancan lokacin, domin hatta kamun da aka yi wa Shaikh Yakubu Yahya a shekarar 1991, Shaikh Zakzaky ya aike ma shi da abaya wacce Shaikh Yakubu Yahaya ya rika rufa da ita tare da suturce jikinsa a Kurkukun Benin, kasantuwar yanayin rayuwar kurkuku hatta bahaya da sauransu a cikin kurkukun ne ake ayi ba tare da an tanadar da waje na musamman domin kebancewa ba, alhali ga Mutane a wajen suna gittawa.To shi Shaikh da wannan abayar ya rika suturce jikinsa.

Haka dai a kurkukun, Shaikh Zakzaky ya kuma aika masa da littattafan karatu, irin su Sahifa da sauran abubuwa wadanda har yanzu suna nan yana amfani da su, kamar Carbi da sauransu.

Shaikh Yakubu ya yi tafiye-tafiye, Ittikafi, Ijitima, Hajji da Umara  shi da Malam(H) tare... "Mun je (Hajji da Umrah) tare da ni da shi (Sayyeed Zakzaky) da Shaikh Turi zai kai sau 7, kuma komi tare muke yi;  hatta da cin abinci da sauransu." In ji Shaikh Yakubu Yahaya.

Shaikh Yakubu ya ce; "Ni na karu da su Malam (H) musamman a karatuttuka, duk da sadda na fahimci kiransu (H) na yi karatu amma ban san yadda zan aikata shi kaitsaye ba, sai haduwarmu da Su Malam. Musamman a 6angaren Ibada, Zikirori, tahajjud, kai har tsafta ma da yadda ake sa tufafi, sai da na hadu da Malam(H)"

"A lokutta da dama za mu je mu yi karatu da Su Malam (H) kuma su ne za su ba mu kudin mota abinci da wurin kwana, wani lokaci ma hadda kyaututtuka daban-daban irin zabba da sauransu."- Ya bayyana irin Karamcin su Malam(H)

Albishirin Da Aka Yi Ma Sa Ma fi Tsada A Tafarkin Allah.

Atakaice dai Shaikh Yakubu Yahaya ya kasance a karkashin jagorancin Shaikh Zakzaky (H) tun wancan lokaci har zuwa yau din nan, kuma yana bada gudummawarsa yadda ya kamata a wajen ci gaban wannan da'awa ta gidan Annabta, kuma ya samu shaida mai karfi daga Jagoran wannan da'awa tun a can baya musamman a Waki'ar 19th April wadda (John Madaki) ya yanke Masa hukuncin kisa saboda Addinin Allah da kariya ga Manzon tsira(S.A.W.A)

A lokacin ne Shaikh Zakzaky (H) ya yi tattaki har garin Katsina domin jan kunnen Madaki akan wannan mummunan kudirin nasa kuma ya gaggauta janyeshi. A nan ne Sayyid Zakzaky (H) ya yabi Shaikh Yakubu kuma ya jinjina masa har ma ya yi masa addu'a yace; "Allah ya maishemu damshenka", sannan kuma ya karanto ayoyi wadanda suke siffanta ayyukan Shaikh Yakub da yin kamanceceniya da irin ayyukan annabawan Allah, har ma kuma ya ambace shi da suna "Gwarzon Kare Martabar Manzon Allah."

Biyayyarsa Ga Jagora(H).

Shaikh Yakubu ya kasance mai biyayya ga Jagoran (H) har zuwa wannan lokaci da aka afka ma Jagoran (H) a shekarar 1437/2015 a zariya, aka kashe dimbin Almajiran Shaikh Zakzaky(H) da 'ya'yansa sannan aka kama Shaikh Zakzaky din da mai dakinsa wanda har yau suna tsare a bisa zalinci.

Saboda tsananin biyayya da girmama Jagora, ko kallonsa su hada Idanu ba ya iya yi, balle ya ba shi hannu su gaisa. Wannan shaida ce wadda duk mai lura da shehin Malamin a yayin ganawa ko haduwarsa Sayyeed Ibraheem Zakzaky zai bada.

Karkarewa.

To, Shaikh Yakubu Yahaya katsina yana cikin wadanda suka tsaya tsayin-daka wajen ba wa harkar nan kariya a bayan Waki'ar nan tare da nusar da 'yan'uwa da dorasu a bisa nizami na wannan da'awar take akai. Kuma kullum fatansa shi ne Allah Ya Gaggauta kwato Jagoranmu Sayyeed Ibraheem Yakubu Zakzaky (H).

Allah ya tabbatar da mu a kalkashin Jwgoranci Shaikh Ibraheem Yaqoub Alzakzaky dun dadi duk wuya, ya sa karshenmu Shahada ce a tafarkin Allah.

Tattarawa: Voice of Shaikhs (Zauren Jawaban Malamanmu)

Comments

Popular posts from this blog

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky