ASALIN ADDU'AR UMMU DAWUD- Daga Muhammad. Suleman Kaduna

ASALIN ADDU’AR UMMI DAWUD DA AKE YI A RAJAB
Daga Muhammad Sulaiman Kaduna

Ummi Dawuda wata baiwar Allah ce da ta kasance a zamanin Imam Sadik (AS). Asalin sunanta Fadima. Dawud sunan danta ne wanda tare ta shayar da su mama da Imam Sadik (AS), kasantuwar a lokacin, Larabawa suna da al’adar kai ’ya’yansu raino zuwa ga wasu mata. Misali kamar yadda Halimatus Sa’adiyya ta raini Manzon Allah (SAAW). Dawud yana daga cikin jikokin Imam Hasan (AS). To, Halifan Abbasawa na lokacin mai suna Mansur ya sa aka kamo wasu daga cikin jikokin Imam Hasan da ke zaune a Madina a kawo su zuwa Irak. To, daga cikin wadanda aka kamo akwai shi wannan Dawud din. Da aka kai su Irak, aka wuce da su zuwa kurkuku, aka tsare su har lokaci ya tsawaita ba a sako su ba. 

Wani lokaci, Ummi Dawud ta ji labarin cewa, an kashe su, wani lokaci kuma ta ji labarin cewa suna raye. Ummi Dawud ta dukufa da addu’a, kuma ta sa bayin Allah dabam-dabam da su taimaka mata da Addu’a kan wannan al’amari. Tana cikin wannan hali, wata rana, sai ta ji Imam Sadik (AS) bai da lafiya. Sai ta tafi domin gaishe shi. Bayan ta gaishe shi, da ta tashi za ta dawo gida, sai Imam Sadik (AS) yake tambayar ta yaya labarin Dawud? Tana jin sunan Dawud, sai ta fashe da kuka! Ta ce in zamo fansa gare ka ya shugabana, Dawud yana tsare a kurkuku a Iraki. Na kusan debe tsammani da haduwa da shi, saboda haka ka taimaka man da Addu’a. 

Sai Imam Sadik (AS) ya ce mata ki yi Addu’ar “Istiftah.” Addu’a ce, duk wanda ya karanta ta, to Allah zai amsa masa. Har Mala’iku suna albishir ga wanda ya yi ta cewa, Allah ya amsa masa, kuma sakamakon sa Aljanna. Nan take sai Ummi Dawud ta ce ya Addu’ar take? Sai Imam Sadik (AS) ya ce, ya Ummi Dawud watan Rajab ya kusa zuwa, wata ne mai albarka. Darajarsa na da girma, kuma addu’a a cikin sa karbabbiya ce. Idan an shiga watan, to ki azumci 13, 14, 15 na watan. A ranar 15, sai ki karanta addu’ar. 

Ga mai bukatar ganin addu’ar, da ma surorin da ake karantawa gabanin addu’ar, yana iya duba littafin Mafatihul Jinan da sauran littafan Addu’o’i. Imam Sadik (AS) ya ce mata, idan kika yi wannan Addu’a, to Allah zai saukake maki duk wata bukata taki, kuma zai biya maki ita. Duk wanda ya karanta wannan Addu’ar, to Allah zai karba masa Namiji ne ko Mace. Kuma da a ce dukkan Mutane da Aljannu makiya ne ga danki, to Allah Mai iko ne ya tsare shi daga sharrinsu. Sai Imam Sadik (AS) ya rubuta mata Addu’ar, suka yi sallama da shi ta koma gida. 

Lokacin da watan Rajab ya kama, sai ta aikata dukkan wadannan ayyuka na ibada da ya yi mata bayani. A daren 16 bayan ta yi sallar Magrib da Isha’i, sai ta yi bude bakin Azumin da ta yi na ranar 15. Bayan haka ta dan yi wasu ibadodi, sai ta je ta kwanta domin yin barci. To, a barcin nata, sai ta yi mafarki da Manzon Allah (SAAW) yana yi mata albishir da cewa, Allah Ta’ala ya biya mata bukata, kuma ya gafarta mata. Allah Ta’ala zai tsare maki danki, kuma zai dawo da shi gare ki. Ummi Dawud ta tashi daga barcci tana mai farin ciki da yakinin cewa danta zai dawo. 

Ba a dauki lokaci mai tsawo ba, sai ga danta ya dawo. Ya ba ta labarin cewa, an tsare su a wani Kurkuku, mai kunci kuma an daure su da sarka. “Har na debe tsammani da fitowata. A daren 15 ga watan Rajab, sai na yi mafarki da Kakana Manzon Allah (SAAW) Ya kira ni yana cewa: Albishirinka Allah ya karbi Addu’ar mahaifiyarka kan al’amarinka. Ko da na farka barci na samu har Halifan Abbasawa Mansur ya sa a fito da ni daga Kurkuku a mai da ni Madina.”

Lokacin da Dawud ya dawo Madina, sai suka tafi wajen Imam Sadik (AS). To, sai Imam Sadik (AS) yake fada masu cewa, ai dalilin da ya sa Mansur ya sake ka shi ne ya yi mafarki da Imam Ali (AS) ne, ya ce masa “ka saki da na ko kuma in jefa ka cikin wannan Wutar.” Sai Mansur din ya ga kogin wuta karkashi kafafuwansa. Saboda haka ya tashi barci a firgice. Saboda haka sai ya ba da umarnin a saki Dawud daga Kurkuku. 

Ummi Dawud bayan haka, sai ta tambayi Imam Sadik (AS) cewa, zai yiwu a karanta wannan Addu’ar ko ba a watan Rajab ba? Sai Imam Sadik (AS) ya ce mata, na’am za a iya karanta ta a ranar Ar’fa ko ranar Juma’a. Haka nan kowane wata na Musulunci, idan mutum na da wata bukata, yana iya Azumtar ranekun 13, 14, 15 na watan, a ranar 15 sai ya karanta wannan Addu’ar, insha Allah zai samu biyan bukata. 

Akwai darussa masu yawa a cikin wannan kissa ta Ummi Dawud. Kuma daga karshe Imam Sadik (AS) ya ce, za a iya yin wannan ayyuka na ibada, ba lalle sai watan Rajab ba. Misali mutum zai iya yi a watan Sha’aban ko watan Ramadan. Allah Ta’ala ya sa mu dace.

Don haka muna kira ga ’yan’uwa a daidaiku, Halkoki, Da’irori da Lajanoni, su dage don ganin kowa da kowa, babba da yaro an yi wannan addu’a ta Ummu Dawud da azumomin da ke tare da ita na gobe Alhamis, jibi da gata; wato 13, 14 da 15 ga Rajab din. A yi addu’o’in musamman ga Jagoranmu, Shaikh Ibraheem Zakzaky, Mai dakinsa Malama Zeenah Ibrahim da sauran ‘yan’uwa da ke tsare. Allah ya kara musu lafiya da tsawon kwana, ya kwato mana su da gaggawa.

Mun ciro wannan bayanin daga filin TAMBIHI na ALMIZAN da za ta fito ranar Juma’a. Akwai wasu bayanan kafin wannan a cikin filin. Sai a nemi jaridar a saya a karanta.

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky