Posts

Showing posts with the label Daga jaridun mu

SHEKARARSA 70 A DUNIYA...A cikin wannan shekarun ya kwashe da yawansu cikin Ibtila'I na zalumcin azzalumai- Rahama Abdulmajid

Image
SHEKARARSA 70 A DUNIYA... A cikin wannan shekarun ya kwashe da yawansu cikin Ibtila'I na zalumcin azzalumai. 1 Shekara shida kenan da aka daure shi daga shi har matarsa  2 A cikin wannan shekarunsa Saba'in Gwamnatoci suka karar da 'ya'yansa. 3 A cikin wannan shekarun an kashe dubban mabiyansa maza da mata manya da yara har da na goye da suke asalin yan Najeriya masu hakkin tsaro da kare lafiya a wuyan gwamnati. 4 A cikin wadannan shekarun aka rushe duk wani waje da ya mallaka  5 a cikin wannan shekarun ne Kotu ta rika bayar da belinsa gwamnati na take umarnin kotu. 6 A cikin wannan shekarun duka bai kira mabiyansa da su dauki makami kamar yadda inyamurai ke dauka su kwana lafiya, yarbawa ke dauka su kwana lafiya, Fulani ke dauka su kwana lafiya.  7 Laifinsa daya shine ya zabi hanyar da ya ke ganin ita ce addininsa a kasar da kundin tsarin mulkinta  yace kowa na da 'yancin yin addini yadda yake so cikin walwala. DA INA DA DAMAR BAYAR DA AWARD HAKIKA ZAN B...

Ranar:28 November, 1989 (30 Rabius Thani, 1410H)

Image
Ranar: 28 November, 1989 (30 Rabius Thani, 1410H) A wannan ranar ne Shaikh Ibraheem Zakzaky ya fito daga kurkukun Fatakwal na kamun wakiar Kafancan, wanda Janaral Babangida ya yi masa.   Dama an kama Shaikh din ne a ranar 28 ga watan Maris 1987, sannan kuma aka yanke masa hukuncin dauri a ranar 28 ga Nuwambar 1987 din, don haka bayan shekara biyu cur da daure shi a ranar 28 ga Nuwambar 1989 aka sake shi. Shaikh Zakzaky ya fito bayan ya shafe shekaru biyu da wata takwas a tsare kenan. Kuma yana wannan kurkukun ne aka haifa masa yarsa ta biyu mai suna Nusaiba. — Daga littafin *Muhimman raneku 400 a Tarihin Harkar Musulunci*, na Cibiyar Wallafa.

HOTUNAN TARON YAUMUS SHUHADA'U 1442/2021

Image
Hotunan Taron Yaumus Shuhada'u Na Harkar Musulunci a Najeriya, Wanda Ya gudana Yau Lahadi 23 Ga Rajab, 1442 (07/03/2021) a Garin Suleja.

ANYI TARON TUNAWA DA SHAHIDAI A ABUJA 07/03/2021

Image
RANAR SHAHIDAN HARKA ISLAMIYYA Muhd Idris A yau ne aka gudanar da bikin tunawa da shahidan harka Islamiyya da aka saba yi duk shekara a garin Suleja karo na 30. Shugaban Mu'assar ta kasa Sheikh Abdulhamid Bello ne ya kasance babban bako mai jawabi inda ya jaddada ma yan uwa nauyin da ke kansu na sauke hakkin shahidan na harka. Malamin ya ankarar da cewa har kawo yanzu dai abin mamaki ba a sauke shi wannan hakki kamar yadda ya kamata.  Tun kafin haka sai da ya kawo matsayin shahada da kuma shi kansa shahidi a musulunci, da ya dawo ga azzalumai kuma ya ce na da can ma ba su iya hana harka ba bare na yanzu, ya zaiyano yadda azzaluman kasar nan suka rika aukar da waki'a daya bayan daya ana samun shahidai har kawo yanzu. Ya kuma kara kira ga yan uwa wajan kokarin sauke hakkin Jagora a kansu. Farfesa Abdullahi Danladi shi ya gabatar da takaitaccen jawabi tun da fari kan aiyukan ita wannan Mu'assar ya kuma yi godiya ga yan uwa kan kokarinsu gareta. Kamar kowace shekara...

TARIHIN SHEIKH ADAMU TSOHO JOS ATAKAICE

Image
Shaikh Adamu Tsoho Ya Cika Shekaru 59 Masu Albarka Yau 21/2/2021 yayi daidai da zagayowar ranar haihuwar Shaikh Adamu Tsoho Ahmad, wanda aka haife shi a garin Jos ta jihar Plateau, ranar Alhamis 27 ga Ramadan 1382H daidai da 21/2/1962. Yau kimanin shekaru 59 kenan.  Mahaifinsa sunansa Malam Muhammad Sani, amma an fi kiransa da Tsoho. Kakansa kuma Malam Ahmad Kiffa, wanda yana daya daga cikin mutane 14 da aka kwaso su daga Bauchi a wancan lokacin aka kawo su Jos da nufin su raya garin na Jos. Kamar yadda mahaifin Shaikh din ya tabbatar a wani hira da na taba yi da shi a kan tarihin kafa garin Jos a kwanakin baya. Mahaifiyar Shaikh Adamu Tsoho kuwa sunanta Hajiya Amina, ba a fi shekaru 11 ba da Allah Ya mata rasuwa. A yayin da su goma ne a wajen mahaifinsu, sai dai mahaifin nasu ya tabbatar min da cewa Shaikh Adamu Tsoho na daban ne a cikin 'ya'yan nasa ta fuskacin tsayuwa da addini da kuma kula da hakkinsu na iyaye. Shaikh Adamu Tsoho ya yi karatun Allo kamar yadda a...

RASHIN ADALCIN DA AKAIWA SHEIKH ABDULJABBAR

Image
BABBAN ZALUNCIN DA AKA WA SHAIKH ABDULJABBAR KABARA Makiyansa na ta jone-jone da yanke-yanke ga karatuttukansa Malamin nan, wanda asalinsa yana bin makarantar Sunnah ne, a tsawon shekaru yana gabatar da karatu a fannoni daban-daban na addini, kuma yana da almajiransa da suke tafiya tare da shi a karkashin wata inuwa da suka kira ta da Ashabul Kahfi. Duk karatunsa a littafan Sunnah yake gabatarwa, bai taba dauko littafin Shi'a ya karantar da shi ko ya ba da hujja a cikinsa ba. Tare da cewa bai wofintu daga karanta littafan Shi'a din ba, kuma har ma yana ikirarin cewa akwai ruwayoyi da yawa a littafan Shi'a wadanda suke rage martaba da darajar Annabi (S) wanda in aka bashi dama ko in ya samu dama, zai waiwaye su ya warware su ya fito da rashin asalinsu da kuma ta inda suka shigo cikin littafan Malaman Shi'a din. Sai dai wannan abin da ya kudiri aniyar yi, in abin ya zo yi ne ba lallai a samu wata matsala da shi a duniyar Shi'a ba, saboda dama Shi'anci bai taba kud...

MUHIMMANCIN MALLAKAR LITATTAFAN HARKAR MUSULUNCI

Image
ME YA SA AKASARIN JAMA'A BA SU DAMU DA KARANTA LITTATTAI BA? Littafai: *SHAWARATA GA 'YAN UWA* Lallai yana da muhimmanci sosan gaske kowane Buraza da ma Sista su muhimmanta sayen Littattafan da ake yinsu wadanda suke da alaka da Tarihin Jagora (H) ko Harkar Musulunci. Ko da muna ganin mu a kan idonmu ake yin abubuwan, kuma marubutan ma kila mun fi su sanin abin da ke faruwa a yanzu, akalla zai taimaki 'ya'ya da jikokinmu (zuriya) da ma al'ummar da za su zo nan gaba.  Gaskiya na kan sha mamaki sosai ace duniyar 'yan uwa wanda ake lissafa miliyoyin mutane, amma in aka buga littafi kwafi 2,000 a kan Tarihin Harka ko wani abu mai alaka da hakan, sai ka ga ya dauki watanni bai kare ba. Tare da cewa ƙimar kudin da ake sakawa littafin ko rabin ƙimar littafin bai kai ba. Ko mene ne dalili? Ni na kan ba da cewa muna ganin ba mu da bukatuwa ga bayanan da ke cikinsa ne a yanzu, don haka ba sai mun mallaka ba, saboda in ma mun mallaka ba mu da lokacin karantawa a yanzun. Ba...

ALKALAMI KAFI REZA KAIFI tare da M.IGamawa

Image
ALKALAMI KA FI REZA KAIFI M. I. GAMAWA 0703 557 7745 Malaman Wahabiyawa: ’Yan mowa a wajen gwamnati, ’yan bora a wajen Allah Malaman Wahabiyawa sun fahinci damfare wa Gwamnati na da nasa natijar a Duniya, musamman Gwamnatin zalunci wacce ba ta da tausayi ko mutumta rayukan ’yan Adam. Da ma kisa a wajensu abu ne mai sauki, kamar kwance kulli. Shi Wahabiyanci ba shi da tushe, in ma akwai shi da tushe, bai wuce Ibnu Taimiyya Baharrane da Abdulwahab wadanda dukkan su daga lardin Najadu suka bayyana. Shi Ibn Taimiyya waren Gwanki ne a cikin Maluma. Domin shi ne wanda ya rayu har ya mutu yana shekaru sittin da bakwai bai yi aure ba. In ka ga dama ka kira shi tuzurun Shehi na Harrana. In Salafanci da Wahabiyanci na da tushe, to ga tushen nan. Kama-kama har wannan muguwar akida ta shigo mana, ko muna so ko ba ma so. Ga shi yanzu ta zama mana jarrabawa mai tsanani. Wani hali na masu wannan muguwar akida ita ce, mannewa masu mulki. Sun mai da masu mulki iyayengijin da suke rayuwa da karfin mulki...