Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky

Haihuwarsa

An Haifi Sayyid Hammad Ibraheem Zakzaky Ne A Rana mai Kamar ta yau 01 ga Sha'aban 1417 Hirari dai-dai da 10 Ga December 1996 Miladiyya. A Cikin Birnin Kadunan Tarayyar Nijeria.

Sunansa Da Laqabin Sa.

Sunan sa Sayyid Hammad Ibraheem Anai Masa Laqabi Da Saajid.

 Nasabarsa Ta Wajan Uba

Nasabarsa  Ta Wajan Mahaifin Sa: Sayyid Hammad, Shine Dan Allamah Ibrahim Zakzaky, na 7, Shi Kuma Dan Malam Yaqoub Shi Kuma Dan Malam Aliy Dan Malam Muhammad Tajuddin Dan Liman Husaini. Shi Liman Husaini Wani Bawan Allah Ne Kuma Babban Malami Da Yake Limanci A Wani Masallaci A Lokacin. Malam Muhammad Tajuddin Yazo Birnin Zariya Ne Daga Sokoto A Cikin Tawagar Amir Na Zariya. Wato Lokacin Da Shaikh Usman Dan Fodiyo (Ra) Ya Na Da Malam Musa A Matsayin Amir Na Lardin Zazzau Sai Ya Hada Shi Da Malam Muhammad Tajuddin A Matsayin Mai Bashi Shawara, Da Kuma Mai Taimaka Masa Wajan Tafi Da Harkokin Jama'a Akan Tsarin Musulunci.

Assalin Iyayen Su, Sun Fito Ne Daga Magarib, Maroko Kenan A Wancan Lokakacin. Musamman Ma Daga Wani Birni Da Ake Ce Masa Shingidi, Wanda Yanzun Yana Cikin Muritaniya Ne. Amma Alokacin Babu Muritaniya, Shingidi Ake Ce Masa. Kuma Sun Tashi Daga Sassa Zuwa Sassa Har Suka Zauna A Mali Ta Da. Kuma Daga Can Suka Zo Nan. (Nigeria). Ana Cewa Suna Daga Cikin 'sulala' (Zuriya) Din Imam Hasan Al-mujitaba (As), Wadanda Suka Zauna A Qasar Magarib. Daga Nan Suka Gangaro Sukai Mali,  Suka Fado Nan Qasar Nigeria.

Nasabar Sa Ta Wajan Uwa

Sayyid Hammad Dan Malama Zeenah Ita Kuma Sunan Maihaifinta Ibrahim Sunan Mahaifin Shi Muhammad Auwal.
Sunan Mahaifiyar Ta Maryam Sunan Mahaifin Mamanta Abdullahi. Mahaifiyar Ta Maryan Ita Jikanyar Imam Akayede Ce Wani Babban Malami Dake Illorin Jihar Kwaran Taraiyyar Nijeriya.

Karatun Shaheed Hammad

Sayyid Hammad Ya Fara Karatun Sa Ne Agun Mahaifiyar Sa Dunda Shi Ya Taso Ne Mahaifin Sa Na Tsare A Kurkukun Abacha, Yayi Karatu Irin Yanda Aka Saba Kuma Karatu Mai Zurfi A Bangare Qur'ani Da Sauran Karatukan Gida Da Ake Cewa Karatun Ittafi A Cikin Bir Nin Zariya.

A Bangaren Karatun Boko Kuwa.

Sayyid Hammad An Ci Gaba Da Koyar Da Shi A Gida Daga Shekarar Da Aka Haife Shi Watau 1996 Zuwa 1998. 

Bayan Wannan Rainon Sai Aka Sanya  Shaheed Makaranta A Matakin Raino, Watau 'day Care' Ko Kuma 'kindergarten' Daga Shekara Ta 1998 Zuwa 2000 A Makarantar 'buks International School' Da Ke A Kwangila Daura Da Makarantar Koyon Tukin Jirgin Sama Da Ke  A Zaria, Watau 'aviation'.

Daga Gama Wannan Mataki Sai Aka Sanya  Shi A Matakin Da Ke  Gaba Da Wannan Watau Mataki Na 'nursery School' A Shekara Ta 2001 Zuwa 2003 Duk A Makarantar Ta 'books International School'.

Bayan Shaheed Ya Kammala Wannan Mataki Sai Aka Sa Shi A Mataki Na  Gaba Watau Mataki Na  'primary School' A Makarantar 'zaria Children School'. Shaheed Ya Yi Wannan Mataki A Wannan Makaranta Daga Shekara Ta 2004 Zuwa 2009.

Bayan Kammala Karatun Sa A Mataki Na 'primary' Sai Ya Tafi Mataki Na Gaba Watau Mataki Na Karamar 'secondary' Daga Shekara Ta 2010 Zuwa 2012 Inda Ya Kammala Aji Na Daya Zuwa Na Uku A Sashen 'secondary School' Da Ke  A Makarantar 'zaria Children School'.

Bayan Kammalawa Da Karamar 'secondary' Sai Ya Jona Da Sashen Babbar 'secondary' Da Ke  A Wannan Makaranar Daga Shekara Ta 2013 Zuwa 2015.

Sayyid Hammad Yayi Shahada Ne A Cikin Gidan Mahaifinsa Shaikh Ibrahim Zakzaky (H) Dake Unguwar Gyallesu Saka Makon Harin Kisan Kiyashin Da Sojojin Nijeria Suka Kaiwa Shaikh Ibrahim Zakzaky (H) Da Sunan Wai Almajiransa Sun Tarewa Shugaban Sojoji Hanyar Wucewa A Husainiyya Baqiyyatullah Dake Da Nisan Kimanin Kilo Mita 2 Zuwa Gidan Shehin Malamin Dake Unguwar Gyallesu, Sayyid Hammad Sojojin Nijeria Sun Yi Masa Yankan Rago Da Harsashi A Wuyansa A Lokacin Da Yake Bawa Mahaifinsa Shaikh Zakzaky Kariya Daga Harin Zaluncin Sojojin.

Amincin Allah Ya Tabbata A Gareka Ya Shaheed Hammad Ranar Haihuwarka Da Ranar Shahadarka Da Ranar Da Za'a Tasheka Tareda Madaukin Fansar Da Ba'a Nasara A Kansa(AF).

— Tahir Ibrahim Gwarzo.

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)