Posts

Showing posts with the label TARIHI

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Image
Saura Kwanaki 15 Shaikh Zakzaky Ya Cika Shekaru 70 -Saifullahi M. Kabir TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H) Ranar Talata 15 ga Sha’aban, 1372 aka haifi Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), a unguwar Kwarbai da ke birnin Zariya ta jihar Kaduna. Mahaifinsa shine Malam Yaqoub dan Malam Ali dan Sharif Tajuddeen, shi kuma dan wani babban limami da ake kiransa da Liman Husaini. Kakan Shaikh Zakzaky na uku ya kasance daga cikin mutanen Shaikh Usman Danfodiye, wadanda ya tura su garuruwa a matsayin wakilansa, sai ya zama shi Malam Muhammad Tajuddeen Shaikh Danfodiye ya turo shi Lardin Zazzau ne a matsayin mai ba Amir din Zazzau, Malam Musa shawara da taimakonsa wajen tafiyar da harkokin al’umma akan tsarin Musulunci. A wata hira da aka yi da Shaikh Zakzaky dangane da tarihin rayuwarsa a shekarun baya, ya bayyana cewa: “Mahaifina Malamin Alkur’ani ne, haka ma kakana shima Malamin Alkur’ani ne, haka ma uban kaka na. Sai dai shi uban ...

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky

Image
Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky Haihuwarsa An Haifi Sayyid Hammad Ibraheem Zakzaky Ne A Rana mai Kamar ta yau 01 ga Sha'aban 1417 Hirari dai-dai da 10 Ga December 1996 Miladiyya. A Cikin Birnin Kadunan Tarayyar Nijeria. Sunansa Da Laqabin Sa. Sunan sa Sayyid Hammad Ibraheem Anai Masa Laqabi Da Saajid.  Nasabarsa Ta Wajan Uba Nasabarsa  Ta Wajan Mahaifin Sa: Sayyid Hammad, Shine Dan Allamah Ibrahim Zakzaky, na 7, Shi Kuma Dan Malam Yaqoub Shi Kuma Dan Malam Aliy Dan Malam Muhammad Tajuddin Dan Liman Husaini. Shi Liman Husaini Wani Bawan Allah Ne Kuma Babban Malami Da Yake Limanci A Wani Masallaci A Lokacin. Malam Muhammad Tajuddin Yazo Birnin Zariya Ne Daga Sokoto A Cikin Tawagar Amir Na Zariya. Wato Lokacin Da Shaikh Usman Dan Fodiyo (Ra) Ya Na Da Malam Musa A Matsayin Amir Na Lardin Zazzau Sai Ya Hada Shi Da Malam Muhammad Tajuddin A Matsayin Mai Bashi Shawara, Da Kuma Mai Taimaka Masa Wajan Tafi Da Harkokin Jama'a Akan Tsarin Musulunci. Assalin Iyayen Su...