Posts

Showing posts from October, 2021

Haihuwar Mai Albishi, Annabi Muhammad (S)

 Haihuwar Mai Albishir, Annabi Muhammadu (s) Daga Marigayi Muhd Awwal Bauchi Manzon Allah Muhammad bn Abdullah (s.a.w.a)  (A bisa ingantattun ruwayoyi), an haifi Manzon Allah (s) ne a ranar 17 ga watan Rabiul Awwal, ko da yake wasu ruwayoyin sun ce ran 12 ga wanann wata ne, a garin Makka, a shekarar da ake kira da Shekarar Giwaye. Dalilin da ya sa ake kiran wannan shekara da haka kuwa shi ne wani gwamnan Sarkin Abbasiniya ne mai suna Abrahata ya shigo Makka da runduna mai yawa bisa kan giwaye (bayan ya kame garin Yaman) da nufin rusa Dakin Ka'aba da sauya alkiblar mutane zuwa San'a (domin a wancan lokacin mutane sukan kawo ziyarar bauta a Ka'aba) inda da ma tuni ya gina wani guri don wannan ziyara. Amma daga baya lokacin da Abrahata ya iso Makka da wannan runduna ta sa, sai Allah Ya aiko da wasu irin tsuntsaye dauke da tsakuwoyi a bakunansu, inda suka rinka jefo wadannan tsakuwoyi a kan wadannan runduna, nan take suka kashe sojojin da giwayen. Ta haka ne Allah Ya yi magani