Posts

Showing posts from February, 2022

Sheikh Adamu Tsoho Jos Ya Cika Shekaru 60; Tarihin Sheikh Adamu Tsoho A Taƙaice !

Image
  Sheikh Adamu Tsoho Jos Ya Cika Shekaru 60 Tarihin Sheikh Adamu Tsoho A Taƙaice ! Sheikh Adum Tsoho Jos (Malamin Addinin Musulunci Yau 21-Feb-2021 yayi daidai da ranar zagayowar Haihuwar Sheikh Adamu Tsoho Jos, kuma an haifi Shaikh Adamu a garin Jos ta jihar Plateau, ranar Alhamis 27 ga Ramadan 1382H daidai da 21/2/1962. Yau kimanin shekaru 59 kenan.  Mahaifinsa sunansa Malam Muhammad Sani, amma an fi kiransa da Tsoho, kakansa kuma Malam Ahmad Kiffa, wanda yana daya daga cikin mutane 14 da aka kwaso su daga Bauchi a wancan lokacin aka kawo su Jos da nufin su raya garin na Jos. Kamar yadda mahaifin Shaikh din ya tabbatar min a wani hira da na taba yi da shi a kan tarihin kafa garin Jos a kwanakin baya. Mahaifiyar Shaikh Adamu Tsoho kuwa sunanta Hajiya Amina, ba a fi shekaru 11 ba da Allah Ya mata rasuwa. A yayin da su goma ne a wajen mahaifinsu, sai dai mahaifin nasu ya tabbatar min da cewa Shaikh Adamu Tsoho na daban ne a cikin 'ya'yan nasa ta fuskacin tsayuwa da addini da kum