AL'MAJIRAN SHEIKH ZAKZAKY 38 GWAMNATIN BUHARI TA KASHE ACIKIN SHEKARAR DATA GABATA 2019

ALMAJIRAN SHAIKH ZAKZAKY 38 JAMI’AN TSARO SUKA KASHE A SHEKARAR 2019

Daga Saifullahi M. Kabir

A yayin da shekarar Miladiyya ta 2019 ke karewa a yau Talata, muna tunawa da irin ta’addancin gwamnatin Buhari a kan ‘yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Zakzaky (H), wanda ya sabbaba samun Shahidai akalla 38 a cikin wannan shekarar.

A ranar 9/7/2019 ne ‘yan sanda suka bude wuta a kan masu muzaharar kira a saki Shaikh Ibraheem Zakzaky, inda suka kashe mutane biyu a kofar majalisar tarayyar Nijeriya a garin Abuja. ‘Yan uwan da suka kashe a wannan ranar sune Shahid Jafar Mika’il Lafiya da Shahid Mahmud Umar Suleja.

Bayan kwana uku da wannan waki’ar a ranar 11/7/2019 kuma ‘yan sanda suka kuma budewa masu muzahar kira a saki Shaikh Zakzaky din a garin Kaduna, inda suka kashe ‘yan uwa Musulmi guda biyu; Shahid Ahmad Nasir da Shahid Abubakar Aliyu Badikko.

Kwanaki biyar bayan hakan, a ranar Talata 16/7/2019 ‘yan sanda suka kuma aukawa masu muzaharar kira a saki Malam Zakzaky a Kaduna, inda suka kashe dan uwa daya mai suna Shahid Nura Lawal Markaz.

A cikin wannan shekarar mai karewa ta 2019, ba za mu taba mantawa da waki’ar da ta auku a Sakatariyan Gwamnatin Tarayya (Federal Sectariat) da ke Abuja  a ranar 22/7/2019 ba. Domin kuwa a wannan ranar gamayyan jami’an tsaron soji da ‘yan sanda, mopol da ‘yan sandan farin kaya (DSS), sun yi mummunan ta’addanci a kan ‘yan uwa Musulmi, inda suka kasha mutane kusan 16. Kuma suka sace gawargwakin, har yau din nan gawan mutane shida kawai aka iya samu akai musu janaza.

A wannan ranar ta 22/7/2019 jami’an tsaro sun kona motoci, tare da barnata dukiya, cikin barnar da suka yi har da kashe mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, da wani mai hidimar kasa da ke aiki da gidan jaridar Channel Television. Sannan kuma sun kama ‘yan uwa kusan 60 ciki har da mata da yara da masu rauni, har yau da shekarar nan ke karewa, kimanin watanni biyar kenan ba a sake ‘yan uwan ba.

A yayin karewar shekarar 2019, muna tunawa da ta’addancin ‘yan sandan Nijeriya akan

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky