SHIRU AKAN TA'ADDANCI JAMI'AN TSARO A SOKOTO YANUNA DA HADIN BAKINSU AKAYI.

Yin Shirun Hukumomi Ga Ta'addancin Jami'an Tsaro A Sakkwato Ya Nuna Mana Da Haɗin Bakinsu Aka Yi

–Sheikh Sidi Munir Sakkwato

Mun ji mamaki matuƙa akan yin shiru da gwamnatin jahar Sakkwato haɗi da masarauta suka yi akan wannan ɗanyen aiki na jami'an tsaro da ya faru, wanda a matsayinsu na shuwagabanni al'umma to ya kamata a ce sun yi magana ko ba komai muma ƴan jahar Sakkwato ne ba daga wani guri muka zo ba, mun ji kuma mun gani a watannin baya da wasu Sojojin sama suka kufce suka buɗewa mutanen unguwar Mabera dake cikin garin Sakkwato wuta saboda an taɓa budurwarsu har suka kashe wata mata, gwamna ya yi Allah waddai da abin da ya faru har ya ce za a hukumta su waɗannan Sojojin.

Amma mu a ɓangaren mu har ya zuwa Yau ɗinnan babu wani wanda ya buɗa baki ya yi magana akan wannan ta'addancin da jamin tsaro suka yi a kan mu, gwamna ko sarki ko wani Malami, haka kafafen yaɗa labarai. Wannan ne yake tabbatar mana da cewa wannan abin da ya faru da sanin gwamna ya faru domin sanin kowane gwamna shi ne Chef Security na jaharsa, ba wani abu da zai faru face da sanewarsa idan ma abu ya faru ba da saninsa ba to ya kan fito ya jajanta sannan ya yi Allah waddai da abin da aka yi tare da ɗaukar mataki.

A jiya jum'a ne 27/12/2019, da rana tsaka ƴan Sanda a bisa umurnin Kwamishinan jahar Sakkwato Ibrahim Sani Ka'oje, suka buɗe mana wuta da harsasai masu rai inda a nan take suka kashe mana ɗan uwa ɗaya mai suna Yahuza Umar dake zaune a garin Kalambaina ƙaramar hukumar Wamakko, suka raunata shaɗaya da raunuka mabambanta, Yara da Manya har da Mata, wasu an harbesu a Ciki wasu a Ƙafa wasu a Hannaye, akwai wani ɗan uwa da suka harba a hannu har sai da ɗan yatsan sa ya fita, duka fa wannan ta'addancin saboda mun fito ne domin gudanar da abin da yake ƴanci ne ga kowane ɗan ƙasa na ya fito ya bayyana ra'ayinsa na farinciki ko baƙinciki.

Yin shiru da abin da ya faru da mu a jiya ba fa zai haifarwa da jahar Sakkwato Ɗa mai Ido ba, domin muma ƴan haifen Sakkwato ne kuma adadin mu ya fi ƙarfin mutum goma ko ɗari ko dubu ɗaya da za a iya bindigewa a lokaci ɗaya, haka kuma dole cigaba da rayuwa za mu yi a cikin garin Sakkwaton.

Harwalayau kuma muna ƙara kira da kakkausar murya da gwamnatin Buhari da ta gaggauta sakin jagoranmu Allama Sayyid Zakzaky (H) da take cigaba da tsarewa fiye da shekaru huɗu ba tare da wani sharaɗi.

–Daga Bilal Nasir Umar Sakkwato.voiceofsheikh@gmail.com

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky