TUNATARWA TARE DA AMMAR M.RAJAB

ADDININ MUSULUNCI ADDINI NE NA KAMALA

Daga Ammar M. Rajab

Addnin Musulunci addini ne na kamalar mutum, kuma mafi girman tsarin kamala ita ce soyayya. Hakazalika soyayyarnan tana da tasiri mai girma wajen tabbatar da tsarin da Allah ya sanya a Musulunci domin ci gaban al'ummar Bani-Adama. Imam Muhammad Bakir ya siffanta Musulunci da cewa; ba komai bane fa ce soyayya da kaunar juna.

Alkur'ani mai girma, littafin Allah ya siffanta Allah ta'ala ga mutane da cewa; shi mai tausayi ne, mai so da kauna, kuma mai son bayinsa. Tabbas wannan Ubangijin ne ya kafa turakun gini na shari'ar Musulunci wacce ita ce shari'ar dukkanin Annabawa a bisa asasin kaunar juna da soyayya. Har wala yau Allah ta'ala ya saka ka'ida na saka soyayya ga mutane a kan jagororin addini da sauran shugabannin siyasar tafiyar da al'amarin al'umma.

Wannan yasa ya zama lazim jagorin addini da na siyasa su kira al'ummarsu zuwa ga kauna da soyayya a tsakaninsu da kuma kiransu zuwa ga sabo da juna, fahimtar juna da kuma yawaita kusantar juna domin samun soyayya a cikin al'umma domin samar da al'umma masoya. Wannan shi ne asasi da turbar gina al'umma ci gababbiya ba don bata da bambancin fahimta  ba. Sai domin tseratar da al'ummar da zata zo nan gaba daga gurbacewar tunani na kiyayya.

Barkanmu da yau.
https://youtu.be/gHZTPGyshZ0

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky