WAN'NAN ZALUNCIN YA ISA HAKANAN

LALLAI FA A SAKI SHAIKH ZAKZAKY! ZALUNCIN YA ISA!!

A wata irin wannan wata na Disamba, 2015 gwamnatin Tarayyar kasar nan ta aiwatar da shirin da ta dade tana kullawa na yunkurin halaka Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky da ma murkushe Harkar gaba daya. Sai dai ba kamar yadda suka so ba, Allah ya tseratar da rayuwar Jagoranmu, kuma Harkar ta ci gaba da wanzuwa. Amma duk da haka sun yi barnar da a tarihin kasar nan ba a taba yi wa wata jama’a irin ta ba, don kuwa sojojin Nijeriya sun kashe mutane sama da dubu guda. A cikin su akwai mata masu ciki da yara kanana. Sun kone tare da rushe gidan Jagoranmu da Cibiyar Musulunci ta Husainiyya Baqiyyatullah.

Har ila yau tun bayan aukuwar wannan kisan kiyashin na Zariya, mun rika fitowa muna muzaharorin lumana don neman a bi mana hakkinmu, a yi adalci, a saki Jagoranmu da aka raunata da harbin bindiga, amma ba abin da aka rika tarbar mu da shi sai kisa, dauri da cin zarafi iri-iri. A irin haka gwamnatin Buhari ta kashe akalla mutane 200, baya ga raunata dubbai a garuruwa daban-daban da suka hada da Kano, Katsina, Kaduna, Gombe, Bauchi, Jos, Zariya, Funtuwa, Azare da Abuja.

Sannan a tsawon wadannan kwanaki 1476 da wannan ta’annuti da sojoji suka yi, Jagoranmu Shaikh Zakzaky da matarsa Malama Zeenah Ibrahim ke fama da matsanancin ciwo saboda burbushin harsasai da ke jikinsu, amma ba su samu maganin da ya dace da su ba. Wata kotu har ta ba da izinin a fita da su kasar waje a duba lafiyarsu, kuma an je din, amma gwamnatin Tarayya ta kulla makarkashiyar da ta sa ala dole suka dawo gida, ba su samu biyan bukatar da ta kai su can ba.

Kar kuma a manta an yi shekara guda ana tafka sharia’a a wata babbar kotu da ke Abuja na neman a kiyaye hakkin dan Adam da Shaikh Zakzaky ke da shi. Kuma a karshe kotu ta ba da umurnin a sake shi, har ma da biyan diyya. Amma saboda rena alfarmar kotu haka gwamnatin Tarayya ta ki bin umurnin kotun nan, ta ci gaba da tsare Jagoranmu. Karshe ma suka kirkiri wasu tuhume-tuhume na wauta a kansa, suka ci gaba da tsare shi a Kaduna har kawo yanzu.

Wannan zalunci da me ya yi kama? Gwamnatin nan a duk sa’ad da ta fuskanci matsin lamba a kan me ya sa ta ki sakin Jagoranmu, sai ta ba da amsar da ta sha bamban da na baya. Misali ba jimawa sosai da aukuwar kisan kiyashin Zariya, gwamnatin nan ta ce tana tsare da Jagoranmu ne don ba shi kariya. Da tafiya ta yi tafiya ta ce, tana tsare da shi ne saboda ba wanda yake so ya yi makwabtaka da shi. Ta zo ta ce tana tsare da shi ne saboda kare muradun kasa na tsaro. Dalili na baya-bayan nan shi ne wanda Ministan shari’a ya bayar cewa, gwamnatin Tarayya ba za ta sa baki a al’amarin da ke hannun gwamnatin jihar Kaduna ba.

Duk da haka, ba za mu yi kasa a gwiwa ba, za mu ci gaba da shaida wa jama’a da duniya baki daya cewa an zalunci Shakh Zakzaky tare da mu mabiyansa. Fatanmu shi ne ilahirin jama’a su fahimci wannan sako, su kuma gane cewa zaluntar mutum guda fa, tamkar zaluntar kowa da kowa ne. Shiru a kan zaluntar Shaikh Zakzaky da gwamnatin Buhari take yi ba zai haifar wa kasar nan da mai ido ba. Dolen kowane dan kasa ne ya tashi tsaye ya ba da gudummawarsa kan kawar da wannan zalunci. Da ma Allah ya ce ba ya son zalunci da azzalumai.

Don haka yau ma mun sake fitowa, muna kara yin kira da babbar muryar cewa a saki jagoranmu Shaikh Zakzaky, mai dakinsa da sauran ’yan’uwa da suke tsare tun Disamban 2015. Yin haka ne kawai zai tabbatar da cewa gwamnatin nan da gaske take yi, tana son gyara kura-kuran da ta aikata a baya na danne hakkin bil’adama da saba wa kundin tsarin mulkin kasar nan.

SA HANNU
SHAIKH ABDULHAMID BELLO ZARIA
27/12/2019https://www.youtube.com/channel/UCU4nlVVY37r2s461g9NBZcQ

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky