ZANTUKAN HIKMA DAGA BAKIN SHEIKH ZAKZAKY (H)

[12/29, 6:03 AM] Ysf Hamisu Sani: "Mu makamanmu na hankali ne, muna magana muna rubutu, su kuwa suna sa hauma-hauma da zage-zage da harbi da kamu da dauri. Sai mu ce idan da da gaske in in kuna iyawa mu komo fage daya, na hankali da ilimi, ku fada mu fada, ku rubuta mu rubuta, a kaima al'umma talla ta zabi daya. Sun san a nan ba za su yi nasara ba, don haka sai suke saka bindiga. To bindiga tana da iyaka, sun kuma yi 'mistake' wajen sa bindigar, saboda da basu sa ba ma tun asali, da sai su rika ba da tsoro da bindigar, suce zan harbe ka! To sun harban, me Kuma ya rage? Yanzu za su bamu tsoro da me kuma? Akwai abin da kuke da shi bayan bindiga? In akwai ta ku harba. Iyakanta kenan ma (bindigar), da ita ce aka nemi a bamu tsoro kuma bamu ji tsoron ba, kuma bamu jin tsoron."

— Shaikh Ibraheem Zakzaky a bikin shekaru 25 da Harka Islamiyya.
[12/29, 6:04 AM] Ysf Hamisu Sani: ME KE SHUGABANCI BA WA KE SHUGABANCI BA

"To, ka ga akwai abubuwa guda biyu; akwai wane ne Shugaba? Akwai kuma me ke Shugabanci?

"Kun san a nan muna ta fama da mutane su gane ME? Su kuwa basu gane ME, sun fi gane WA? Kullum ai ta darga da su, ba WA za ka ce ba ME? ME ke mulki? Ba WA ke mulki ba. Domin idan ME bai canza ba, to WA ba a bakin komai yake ba.

"Idan me na nan, to da Buhari, da Shagari, da Olushegun, da Jonathan da Dan-Adua, duk daya ne, idan dai ME din daya ne. Amma kaga WA daban-daban ne, ko da wannan Buhari, Shagari, ko da kaji ri-ri amma daban-daban ne. In dai ME bai canza ba, to WA bai ce komai ba.

"To, yanzu mutane kamar suna cikin wani hali na neman Waye zai yi Shugabanci kuma Meye zai yi Shugabanci, ko? To, Matsalar kasar nan ba WA ke mulki bane, ME ke mulki din ne matsalar."

— Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).
[12/29, 6:04 AM] Ysf Hamisu Sani: "Ita Fikira ita ke tafiyar da rayuwar mutum, zantukan mutum da ayyukan gangar jikinsa, sakamako ne na irin tunaninsa, zuciya ke sauwalawa mutum abu, sannan ya aikata. Wato ke nan idan aka samu fikira gurbatacciya, to za a samu gurbataccen aiki, don haka in ana so kyakkyawan aiki, to dole a gina kyakkyawar fikira, don itace asasin kyakkyawan aiki."

— Shaikh Zakzaky (H) A garin Talatar Mafara.
[12/29, 6:05 AM] Ysf Hamisu Sani: 'OPERATION HIJACK'

"... Sai suka soma wani sabon shiri, wanda shine ita Hukumar ta ga cewa yanzu abin da ya kamata shine ta raba Harkar gida biyu. In aka zama gida biyu, sai kowanne ya rika fada da kowanne, wannan yai fada da wannan, wannan ma yai fada da wannan. Sannan kuma sai su rika taimakon kowanne a wajen fada da daya. Suka ce in an yi 50-50 yayi daidai, in ma an yi 40-60 yayi, in kuma ma an yi 70-30 shima ya yayi. Makasudi dai a sa wasu su zama basu a cikin Harka din, su zama 'yan wata bangare daban ba wai su fita ba kamar yadda 'yan Zuhudu suka tafi abinsu. A'a, ya zama sun yi 'Group' ne, an zama biyu, Harkar ta dare biyu ne.

"To, wannan operation high jack, ya sabbaba fitan wasu, amma ba da jimawa ba, sai ita Hukuma ta fahimci cewa ta yi hasara. Saboda abin da tai niyyar yi bai yiwu ba. Wato abin bai zama ratio din 70/30 ba ma, bai zama 90/10 ba, kai wadansu 'yan kwarori ne kamar furfura a kan yaro sukai waje. Duk da hadin kai da goyon bayan Hukuma a lokacin, amma ba su ga tasirin wannan rabawan ba. To, kuma hakan ya bakanta musu rai, ina jin wannan yunkuri kenan na karshe na Kurdawa (cikin Harka), ba wai sun bar mu kenan ba, ba sun kyale mu bane, har yanzu za su yi ta kokarin su ga ta ina za su shigo."

— Shaikh Ibraheem Zakzaky a ranar bikin cika shekaru 25 da bayyana Harka Islamiyya.
[12/29, 6:06 AM] Ysf Hamisu Sani: MUNATANE NE HANKORONMU BA HUKUMA BA

"Ni ina ganin cewa su mutane sun dauka hankoron mu Hukuma ne, muna ce musu a'a, sam, mu Hukuma bata dame mu ba, ita gwamnatin Nijeriya kamar ginin toka ne. In aka tara toka aka yi gini da shi, in ana so a rusa ginin ya ka gani Malam? Ana taba zai rumurmushe. To gwamnatin Nijeriya kamar ginin toka ce, bar ganinta hawa-hawa, kafar hagu za ka saka ka dan tunkuda za ka ga rigigi ta rushe. Amma mutane ne basu shirya ba.

"Saboda haka mu mutane ne damuwar mu ba hukuma ba, hukuma fankan-fayau. Zukatan al'umma bai shiryu ba tukunna, saboda haka 'target' dinmu mutane ne ba hukuma ba. In al'umma suka shiryu to shikenan komai ya yi daidai."

— Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky