AL'ƘALAMI KAFI REZA KAIFI. TARE DA M.I GAMAWA-Janar ƙasim suleimani: Amurika ta hadiyi tabarya.

*ALKALMI KA FI REZA KAIFI*

TARE DA M. I. GAMAWA

*Janar Qaseem Soleimani: Amurka ta hadiyi ta barya!*

Wata mas'ala da marubuci ke fama da ita a kullum, musamman rubutu a kan abin da ke gudana a yau da kullum shi ne rashin tabbas kan abin da zai rubuta. Fakam da yawa mai rubutu na iya kimtsawa tsaf don rubutu a kan wani abu, amma sai sawun giwa ya taka kafar rakumi.

Na shirya don maida wa wani kumurcin Farfesa da ke amsa sunan Malamin tarihi a Nijar martani kan jahilcin da ya nuna game da tarihin Shehu  Dan Fodiyo, Hasken zamani, amma sai sawun giwa ya take na rakumi.

Mun taka birki don magana a kan Qaseem Soleimani, wanda Amurka ta kashe a satin da ya gabata. Soleimani ya tafi kasar Irak a matsayin dan sakon kasarsa Iran bisa gayyatar da ita kanta kasar Irak ta yi masa.

Ashe tafiyar ita ce ta karshe. Abin da ya samu wannan gwarzo shi ne abin da yake nema tuntuntuni. Abin nema ita ce SHAHADA.

Yanzu Allah ya yi wa Janar Sulaimani gyadar dogo da abin da ya fi so fiye da komai. Muna taya shi murnar wannan daukaka. Tabbas ya cancanci wannan darajar da babu irin ta. Shahada za bin Allah ne. Akwai wadanda suke ba da rayukansu don duniya da abin da ke cikin ta. Wadannan sune sojoji masu ba da rayukansu don kare abin da suka dauka a matsayin mafita don saukaka rayuwa.

Sai dai tabbas Sulaimani ba ya daga cikin sojojin da ke shan jinin raunana. Shi mai kare su ne da karfinsa da guminsa har da duk abin da ya mallaka na lokacinsa. Ga shi yanzu ya ba da rayuwarsa don kare raunana. Ganin aikinsa na ceto raunan shi ne ya sa mafi sharrin halittu suka far masa.

Kamar yadda Jagoran fandararrun duniya, Trump na Amurka ya ce, “mun dade muna farautar Sulaimani.” Wannan magana daga Sarkin kazaman duniya ke nan, wanda ke bugun kirjin kashe wani. Amma abin lura a nan shi ne. Shahadar Soleimani ta sa kasar Amurka a tsaka mai wuya. Tabbas Amurkawa sun yi da na sanin za bar Bakauye mai ruwan aladu da tunanin da ya gaza na dabba a matsayin Shugabansu. Yanzu wannan kazami ya mai da rayuwarsu a cikin hadarin da ba a san iyakarsa ba.

Hadari kuma uwar hadurra. Yanzu duk inda Ba'amurke yake a duniya yana cikin fargabar da ta wuce kima. Fargaba uwar rudewa.

Abin da Trump ya ce, shi ne wai Soleimani ya yi sanadiyyar mutuwar dubban Amurkawa. Wannan magana ta fito ba tare da an yi la'akari da abin da duniya za ta fahimta daga cikin ta ba. Fassarar maganar ita ce 'yan ISIS Amurkawa ne. In ma ba ’yan Amurka ba ne, Amurkawa ne a tunani da akida. Yanzu ya kamata duniya ta sani cewa, duk wani dan ta'adda Ba'amurke ne. Tilas Amurka ta yaki duk mai yakar ’yan ta'adda.

Soleimani ya ba da rayuwarsa domin nema wa raunana mafita. Wannan shi ne dalili na farko. Na biyu shi ne kokarin da Amurka ke yi na dawo da ISIS Irak, shi ma dalili ne mai karfi da ya sabbaba kawar da Soleimani daga doron kasa.

Na uku, kamar yadda rahotanni suka fadi shi ne neman sasantawa tsakanin Saudiyya da Irak, wanda Sulaimani ya je Irak a kai. Na hudu tsoron da Amurka ke ji na shawarar da Soleimani ka iya bayarwa ga raddin da Irak ya kamata ta kai don ramuwar gayyan kashe Kwamandan sojojin Sa-kai na Irak.

Wata wauta daga Trump ita ce wai sai da ya kashe Soleimani sa'annan ya nemi dalilan da ya fada wa duniya. Dalilan da ba su kamaci fitowa daga bakin wanda ke cikin maye ba, kodayake Trump na cikin mayen mulki.

An ce hatta karyar Amurka ta farko, Birtaniya, ba ta da labari,sai da aikin gama ya gama. Watakila wadanda Trump ya fada wa sune Isra'la da kanwarta Saudiyya. Shi ma wannan akwai wasu nasarori a ciki. Na farko Amurka ba ta, ta ba nasara a wani yaki ba. Ganin haka sai ta fara gayyato wasu kasashe domin taimaka mata. Haka na faruwa ne bayan ta kitsa karyar cewa wanda za a taya ta yaka hadari ne ga duniya baki daya.

To, yanzu me za ta ce wa duniya don neman taimakon yi wa Iran taron dangi?Amsa ita ce babu. Na biyu shi ne, duk da cewa har yanzu su ke juya kafofin yada labarai, amma wasu kasashe irin Iran suna da hanyoyin fada wa duniya nasu labarin. Kai su ma kafofin yada labarun Trump sun hakaito shi yana cewa shi ne ya ba da umurnin aikata wannan ta'addancin. A karo na farko Allah ya toshe basirar Amurka, ko dai don sun samu sakarai a matsayin Shugaba ko kuma kamun Allah don yawaitar ta'addancinsu.

Pentagon na gama wannan ta'addanci, sai suka ce Trump ya ba su umarni. Shi kuma Dolon doliyo nan take ya bugi kirji ya amsa. Kai ka ce abin kirki ya yi.

Mutane suna rama wa wanda ya amfane su bayan babu shi. Jana'izar Janar Soleimani ta tabbatar da haka. Domin tun ran da aka fara mutuwa a duniya ba a ta ba samun taron dan Adam a wata jana'iza kamar ta Soleimani ba. Ashe sakamakon jarumai daban yake. Babu wanda ke murna da rashin Soleimani sai azzalumi, sai kuma wanda azzalumai suka mai da a matsayin karensu.

Ashe da mutum zai daure ya kyautar da rayuwarsa don wasu su rayu, tabbas wadanda ya bai wa ransa don su, za su saka masa da addu'o’i da hidima a lokacin da ba shi raye. Zai samu sulda da iko a kan jama'a fiye da lokacin da yake raye.

Wane buki ko hidima Soleimani zai yi, wanda zai tara wadannan mutanen da babu wani mutum da ya ta ba tara irin su a duniya bayan babu shi.

Lokacin wannan rubutu nake sauraro daga talabijin na Aljazeera cewa, akalla mutane hamsin ne turmutsutsun mutane ya kashe. Babu wanda zai ce wa wadannan mutane aikin ganin ido suka yi wa Soleimani. Sun san babu shi.

Shahadar Soleimani tabbas ta aika sakonni masu cike da darasi. Kadan daga ciki sune: Duk abin da mutum yake yi masoya da makiya suna kallon sa. Na biyu shi ne mai yin abu don Allah yana dawwama a zukatan mutane, kuma za su nuna masa soyayya a duk lokacin da damar nuna soyayyar ta samu.

Sa'annan masu neman daraja su yi aikin da ya bari don sun shaida aikinsa shi ne abin da ke kawo daukaka bayan an bar duniya. Kadan daga abin da mutum irin Solaimani ya girba ke nan a nan duniya. Lahira kuma da ma don ita ya yi duk abin da ya yi. Ya yi don Allah Madaukaki. Ya bi turbar wanda Allah ya aiko domin nuna wa mutane da aljanu sirrin samun lahira. Shi ne Manzon tsira, wanda babu kamar sa.

Su kuma Amurkawa dole su biya farashi mai tsada ta hanyar samun martani mai gauni daga Iran. Kowa a duniya ya shaida cewa Amarka ita ta takali Iran. Fatanmu shi ne Imam Mahdi ya dafa wa Iran a lokacin ramuwar gayya.

Abin lura na farko ta  bangaren Amurka shi ne, rashin tabbacin ta inda ramuwar gayyar za ta  bullo musu. Na biyu shi ne rashin tabbas ga karfin da ita Amurka ke tutiya da shi. Watakila duniya ta fahimci cewa karfinta ya fi yawa a kafofin yada labarai fiye da yadda za a ga karfinta a aikace in an gwabza.

Da yiwuwar a fahimci karfin Amurka ba komai ba ne idan an shirya mata. Sa'annan ga taimakon Allah ga wanda aka zalunta.

Wannan aiki na rashin imani ya bayyana jami'an Gwamnatin Amurka a matsayin makaryata masu kame-kame. Yanzu sune kan gaba wajen karya dokokin kasa da kasa. Duk wanda ya ga hira da manema labarai da Sakataren harkokin wajen Amurka ya yi da manema labarai ran Talatar da ta wuce, zai gane cewa Shugaba Trump ya yi aiki mai wahalar karewa. Mike, bai dade yana magana da su ba. Kashi tis'in na tambayoyin sun gagari amsawa, sai kame-kame. Da ya fahinci magana za ta kare, ya kama tari, sai ya ce musu “na gode muku sosai.” Ya yi tafiyarsa.

Wani rukushi ga Amurka in Iran ta rama shi ne faduwar girmanta. Haka kuma za a dauke ta katuwar banza kuma fankam-fayau.

Allah ya kar bi Soleimani a matsayin shahidi. Tururuwar jama'a a guraren jana'izarsa ya nuna tasirin da akidunsa da manufofinsa suke da shi a gun mutanen Iran da ma duniya baki daya. Tabbas Amurka ta yi aikin baban giwa. Ta shahadantar da jarumi Soleimani, amma dole ta fahimci cewa ya bar miliyoyin Sulaimanawa a duk fadin duniya. Domin abin da ya tafi ya bari akida ce. Akida kuwa a zuciya take. Zuciya kuma a cikin kirji take, babu mai ganin abin da take dauke da shi. Ko mai karatu ya fahimci abin da ya sa ALKALAMI ya ce Amurka ta hadiyi ta barya? Wanda ya hadiyi ta barya kuwa, kun san tsaye zai kwana!

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky