TAKAITACCEN TARIHIN JANAR QASIM SULAIMANI

An haifi Laftanar Janar Ƙasim Sulaimani ne a shekarar 1957 a ƙauyen Ƙanat-e Malek da ke lardin Kerman na ƙasar Iran. A lokacin samartakarsa ya bar garin na su in da ya koma garin Kerman da zama inda a nan ya yi karatu da kuma ci gaba da gudanar da wasu ayyuka na hannu musamman gine-gine don samun abin rayuwa, kamar yadda kuma a can ne ya dinga halartar lakcocin wani malami da yake zuwa yankin da suke mai suna Hojjat Kamyab, wanda kuma ya kasance ɗaya daga cikin mabiya marigayi Imam Khumaini (r.a).
Shahid Janar Ƙasim Sulaimani ya shiga cikin dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) ne a shekarar 1979 bayan nasarar juyin juya halin Musulunci a ƙasar Iran da kuma kafa dakarun da marigayi Imam Khumaini yayi. Bayan wani lokaci ya samu horo da kuma ƙwarewa cikin wannan aiki na soji.
A shekarar 1980 lokacin da Saddam Husain ya ƙaddamar da yaƙi kan Iran wanda ya ɗau shekaru takwas ana yi, Janar Sulaimani ya shiga cikin yaƙin inda ya jagoranci wasu dakarun sojoji daga lardin Kerman waɗanda shi da kansa ya tattaro su da kuma ba su horo na soji. Sakamakon irin gagarumar rawar da ya taka da kuma jaruntakar da ya nuna wajen jagorantar hare-haren da aka kai da kuma ƙwato wasu yankuna daban-daban da sojojin mamaya na Iraƙin suka mamaye hakan ya sa ya samu ƙarin girma da matsayi na soji daga ciki kuwa har da zama kwamandan bataliya ta 41 da ake kira da bataliyar Sarallah a daidai lokacin kuwa yana cikin shekarunsa na ashiri ne. ya fi gudanar da ayyukansa ne a yankuna da kuma fagagen yaƙi na kudancin ƙasar ta Iran.
Ya samu gagarumin rauni a hare-haren da dakarun Iran suka ƙaddamar da nufin ƙwato garin Bustan da ke lardin Khuzestan na Iran daga hannun sojojin mamayan Iraƙi da ake kira da ‘Operation Tariq al-Qods’ (hare-haren tafarkin zuwa Ƙudus) inda bayan gagarumin faɗa da yaƙi na tsawon mako guda, dakarun Iran sun sami nasarar ƙwato wannan gari.
Har ila yau kuma ya kasance yana jagorantar wasu hare-hare na sari ka noƙe har zuwa cikin ƙasar Iraƙin a lokacin kallafaffen yaƙin inda aka ce ta hakan ne ya samu ƙulla alaƙa da shugabannin Kurdawan ƙasar Iraƙin da kuma wasu ɓangare na ‘yan Shi’ar ƙasar musamman ƙungiyar nan ta Badr waɗanda dukkaninsu suke adawa da gwamnatin Saddam saboda zaluncin da yake yi.
Bayan kammala yaƙin, Janar Sulaimani ya zamanto kwamandan dakarun IRGC ɗin na lardin Kerman inda a nan ma ya taka gagarumar rawa musamman wajen faɗa da masu fataucin muggan ƙwayoyi da suke son shigowa da su cikin Iran bisa la’akari da kusancin da lardin yake da shi da ƙasar Afghanistan inda ake noma da kuma samar da muggan ƙwayoyin.
Bayan nan kuma a shekarar 1997 ko 1998 ne aka naɗa shi a matsayin kwamandan Rundunar Quds (Quds Forces da turanci ko kuma Sepah-e Qods da farisanci) da suke ƙarƙashin dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) wanda ɗaya daga cikin ayyukansu shi ne taimakawa dakarun gwagwarmaya na yankin Gabas ta tsakiya.
A a watan Janairun 2011 ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ƙara masa girma zuwa ga matsayin Manjo Janar sakamakon irin ƙwazon da ya nuna yayin gudanar da ayyukansa, wanda hakan ya sanya ya zama jami’an Iran da suke kurkusa da Jagora ɗin kana kuma daga cikin waɗanda Jagoran ya yarda da su sosai.
Har ila yau daga cikin ayyukan da Janar Ƙasim Sulaimani yayi wanda kuma kowa ya jinjina masa har da yadda ya jagoranci faɗa da ‘yan ƙungiyar ta’addancin nan ta Daesh (ISIS) da sauran ƙungiyoyin ta’addanci a ƙasashen Iraƙi da Siriya inda ya samu nasara da kuma kawo ƙarshensu a waɗannan ƙasashen biyu inda ya sanar da kawo ƙarshen daular su da suka kafa a wajen cikin wata wasiƙa da ya aike wa Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei a watan Nuwamban 2017. Hakan ne ma ya sanya daga baya Jagoran ya ba shi lambar girma ta soji mafi girma da daraja a ƙasar Iran wato lambar girma ta Zolfaƙar saboda gagarumar rawar da ya taka wajen faɗa da ta’addancin ƙungiyar Daesh a Siriya da Iraƙi.
Janar Ƙasim Sulaiman ya samu yabo hatta daga maƙiyansa saboda ƙwarewar da yake da ita a fagen yaƙi da kuma tsara dabarun yaƙin, ta yadda hatta mujallar Foreign Policy ta Amurka ta sanya shi a matsayin mutum na ɗaya cikin jerin mutanen da suke da ƙwarewa a fannin tsaro na duniya.
Irin wannan gagarumin aiki da yayi wajen tabbatar da tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma taka wa baƙar siyasar Amurka da Isra’ila a yankin Gabas ta tsakiya burki musamman irin yadda ya kawo ƙarshen ƙungiyar Daesh a Siriya da Iraƙi hakan ya sanya tsawon lokacin Amurka, Isra’ila, Saudiyya da wasu ƙasashen larabawa ‘yan koren Amurka da Isra’ila ƙoƙari ba kama hannun yaro wajen ganin sun kashe shi. Tsawon waɗannan shekaru ya sha fuskantar ƙoƙarin kashe shi da ƙungiyoyin leƙen asirin waɗannan ƙasashe suka yi sai dai kuma Allah Ya tseratar da shi.
To sai dai da yake kowace rai mai mutuwa ce, a ranar 3 ga watan Janairun wannan shekara ta 2020 ne, Allah Ya arzurta shi da yin shahada bayan harin da Amurka ta kai masa a kusa da filin jirgin sama Baghdaza tare da mataimakin shugaban ƙungiyar dakarun sa kai na ƙasar Iraƙi shahid Abu Mahdi al-Muhandis inda suka yi shahada tare da wasu da suke tare da su.
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, cikin saƙon ta’aziyyar shahadar Janar Ƙasim Sulaimanin wanda bayan shahadar tasa aka ƙara masa girma na soji zuwa ga matsayi na Laftanar Janar, Jagoran ya bayyana shi a matsayin: Babban kwamandan Musulunci abin alfahari kana kuma “kyakkyawan misali ne na waɗanda suka sami cikakkiyar tarbiyyar Musulunci da kuma koyarwar marigayi Imam Khumaini” kamar yadda kuma ya ce lalle za a ɗau fansar jininsa daga wajen waɗanda suka kashe shi kuma ɗaukar fansa mai tsanani.
Laftanar Janar Ƙasim Sulaimani yayi shahada ne ya bar mace guda da ‘ya’ya huɗu, maza biyu mata biyu.

Daga Awwal Bauchi.  Alwilayahnews.net

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky