DAKARUN IRGC SUNYI KARIN BAYANI KAN RABO JIRGIN FASINJAN UKRAINE

Dakarun IRGC Sun Yi Karin Bayani Kan Harbo Jirgin Fasinjar Ukraine A Iran

Kwamandan rundunar kare sararin samaniyyar ƙasar Iran na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC), Birgediya Janar Amir Ali Hajizadeh yayi karin haske dangane da harbo jirgin  saman fasinjar ƙasar Ukraine da aka yi a birnin Tehran, babban birnin ƙasar ta Iran yana mai cewa haka ya biyo bayan kuskuren da aka samu ne, kamar yadda kuma ya ce babu wani ganganci cikin haka kuma babu wani ƙoƙarin ɓoye-ɓoye cikin jinkirin da aka samu wajen sanar da hakan kamar yadda wasu suke ƙoƙarin nunawa yana mai cewa wajibi ne a gudanar da ayyukan bincike kafin a sanar da haƙiƙanin abin da ya faru.
Birgediya Janar Hajizadeh ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da manema labarai don ƙarin haske dangane da haƙiƙanin abin da ya farun inda ya ce: Ya samu labarin abin da ya faru na harbo jirgin saman kamfanin jiragen sama na Ukraine din a lokacin yana yammacin ƙasar Iran bayan harin da dakarunsa suka kai sansanonin sojin Amurka da ke ƙasar Iraki. Inda ya kara da cewa: Lokacin da na samu labarin faruwar wannan lamarin na yi fatan ina ma da a ce na mutu kafin jin wannan labari mai sosa rai. Don haka sai ya ce: Ya ɗauki nauyin abin da ya farun kuma a shirye yake ya amince da duk wani mataki da za a dauka a kansa.
Daga nan sai ya fara bayanin haƙiƙanin abin da ya farun inda ya ce: Kamar yadda kuka sani sama da mako gudan da ya gabata ana cikin zaman ɗarɗar mai tsananin gaske a yankin nan, a ko da yaushe akwai yiyuwar ɓarkewar yaƙi. Don kuwa su kansu Amurkawan haka mu ma dakarun mu suna cikin shirin ko ta kwana ɗari bisa ɗari.
Janar Hajizadeh ya ci gaba da cewa: Amurkawa sun yi barazanar kai hari kan wajaje 52 a cikin ƙasar Iran. A saboda haka ne dukkanin cibiyoyin kare sararin samaniyyar ƙasar Iran suka zamanto cikin shirin ko ta kwana ɗari bisa ɗari. Ko shakka a irin wannan yanayin, makaman kare sararin samaniyya na birnin Tehran ma za su kasance cikin irin wannan shirin. Abin da bincike ya tabbatar shi ne cewa a daren da abin ya faru kai hatta ma tun daga wajajen almuru, an sanya dukkanin makaman kariyar sararin samaniyya cikin shirin ko ta kwana, kamar yadda an ƙara wasu na’urori da makaman kariyar ma a Tehran.
Janar Hajizadeh ya ci gaba da cewa: Na’urar kariyar sararin samaniyya ta farko da aka kafa a yammacin Tehran, wacce ita ce ta harba makami mai linzamin da ya harbo jirgin saman Ukraine ɗin tana cikin irin wannan yanayi 3-3 wanda shi ne yanayi na ƙoli na zaman cikin shirin ko ta kwana.
A ci gaba da bayanin haƙiƙanin abin da ya farun, Birgediya Janar Hajizadeh ya bayyana cewar wasu bayanai suna nuni da cewa an harbo makami mai linzami samfurin Cruise zuwa Iran don haka aka sanar da dukkanin cibiyoyin kariyar sararin samaniyyar da kuma makaman da aka kakkafa wannan lamarin ciki kuwa har da ita kanta wannan na’urar kariya da ta harba makami mai linzami da ya sami jirgin fasinjar. Daga nan sai ya ci gaba da cewa: Bisa la’akari da irin yanayin da ake ciki na zaman ɗarɗar an buƙaci da a dakatar da tashin dukkanin jiragen sama, to amma jami’an da abin ya shafa ba su yi hakan ba, don haka ita kuma wannan na’urar a ƙoƙarin faɗa da wannan jirgin wanda ta zaci wannan makami mai linzami samfurin Cruise ɗin ne kuma ga shi ya kusato kusa sosai, don haka ta harba makami mai linzami.
Ya ci gaba da cewa: An kafa wannan na’urar kariyar a wannan yankin ne da misalin ƙarfe 12 na dare, sannan lokcin da wannan jirgin sama ya taso, bisa la’akari da irin yanayi na ɗarɗar da ake ciki da kuma labarin da aka ba wa na’urar na cewa an harbo ‘Cruise missile’ don haka ganin wannan jirgin daga nesa ta ɗauke shi a matsayin wannan makami mai linzamin da aka harbo ɗin ne. A irin wannan yanayin abin da ya wajaba shi ne neman ƙarin bayani da tabbaci daga sama, nan ne kuskuren ya faru. A zahiri dai na’urar sadarwar ce ta fuskanci matsalar don haka ba su sami damar neman wannan bayanin ba. mai yiyuwa saboda na’urar da ke tattare bayanai da aka yi amfani da ita ne ko kuma saboda hanyoyin sadarwa sun cike. Don haka abin da ya rage kawai shi ne daƙiƙoƙi (seconds) 10 ko dai a ɗau mataki ko kuma komai na iya faruwa. Hakan ne ta sanya ɗaukar wannan mataki na kuskure na harbo jirgin.

Birgediya Janar Hajizadeh ya ci gaba da cewa: A na su ɓangaren jami’an hukumar jiragen sama ta ƙasa, kafin sanarwar ɓangaren sojin, sun sanar da cewa babu wani batun harbo jirgin da aka yi sannan kuma ana ci gaba da bin diddigin lamarin. Da farko dai su ɗin nan sun yi aiki ne bisa masaniyar da suke da ita, lalle ba su da masaniya kan haƙiƙanin abin da ya faru.
Ya ci gaba da cewa: A lokacin da na sami labarin faruwar hakan a safiyar ranar Laraba, ba tare da ɓata lokaci ba na sanar da jami’ai cewa lalle ga abin da aka gaya min amma dai ina shakku kan lamarin. Don haka nan take sai na kama hanyar Tehran, kuma a kan hanyar ma na sake gaya wa jami’an cewa lalle mun harbo jirgin sama amma daga dukkan alamu jirginmu ne muka harbo. Koda na iso Tehran sai na samu babbar cibiyar kula da dukkanin dakarun ƙasa ta kafa wani kwamiti na masu bincike da ta ƙumshi dukkanin waɗanda lamarin ya shafa. Don haka a lokacin ba mu da haƙƙin yin wani bayani.
Yayin da yake bayanin cewa jinkirin da aka samu wajen sanar da jama’a abin da ya faru ba wai da nufin ɓoye wani abu ba ne, Janar Hajizadeh ya ce: Dalilin jinkirin sanar da mutane abin da ya farun ba wai wani yana son ɓoye wani abu ba ne. Face dai hakan shi ne tsarin aikin cewa wajibi ne babbar cibiyar dakarun ƙasa ta gudanar da bincike, wanda da safiyar ranar Juma’a ne aka gaba tattara dukkanin bayanan da ake buƙata sannan kuma a lokacin ne haƙiƙanin abin da ya farun ya tabbata. Janar ɗin ko shakka babu cibiyar ta gudanar da aikinta cikin ƙaramin lokacin da za ta iya wato ƙasa da sa’oi 48.
Yayin da yake nuna damuwarsa kan abin da ya farun, Janar Hajizadeh ya ce: Mu ma dai kamar iyalan waɗanda suka rasa rayukansun muna cikin baƙin ciki da juyayi. Dukkanin abin da ya faru ya biyo bayan shaiɗanancin Amurka a wannan yankin ne, wanda hakan ne ya sanya mu zama cikin shirin ko ta kwana na yaƙi a wancan daren. Ni ma da na kasance a yammacin ƙasar nan ina jin cewa lalle yaƙi za a yi don kuwa jiragen yaƙin Amurka suna ta shawagi a sararin samaniyar yankin nan.
Yayin da yake amsa tambaya dangane da cewa me ya sa ba a hana tashin duk wani jirgin saman fasinja a Iran na ɗan wannan lokacin ba, Janar Hajizadeh ya ce: Ni dai ba ina so ne in tuhumci wani ba. Ni dai a ra’ayina a irin wannan yanayi na yaƙi wannan shi ne matakin da jami’an da abin ya shafa ya kamata su ɗauka (wato su hana tashin duk wani jirgin saman fasinja), amma dai hakan ba ta faru ba. Idan har an sami matsala ko kuskure, to ba ta ɓangaren gwamnati ko hukumar jiragen sama da filayen jiragen sama ba ne, ta ɓangaren sojoji ne. Aiki ne da ya kamata wasu su aikata shi.

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky