EL-RUFA'I ƊAN TA'ADDA NE.

WATA SABUWA: 'Elrufa'i kai ne ka yi wa Mutanen Jihar Kaduna Laifi,ba Shaikh Zakzaky ba' -Mabiya Alzakzaky.

"A tsawon shekaru 40 cur na da'awarsa, Shaikh Ibraheem Zakzaky bai ta6a afkawa wani ba, kai ko cin bashin wani ya ki biya bai ta6a yi ba! Wani bai ta6a kai shi kara wajen yan sanda akan ya cuce shi ko ya take hakkinsa ba. Magoya bayansa ba su taba kwashe kayan wani ko su zubar masa a yayin taron su ba, bare su je su dira kan wani ko su kashe shi. Ba a taba yi ba!

Kai kuwa Elrufa'i, sakataren gwamnatinka, ya fada karara cewa bayan da sojoji suka dira a kan Shaikh Ibraheem Zakzaky, inda suka kai kansu gidansa cikin dare, suka rika bude wuta, suka kwana biyu suna harbin almajiransa har sai da suka kashe daruruwan al'ummar Nijeriya, kai ne ka ba da umurni tare da wakilta wasu daga gwamnatinka, suka je suka taya sojoji haqin rami tare da bizne bayin Allah, al'ummar Nijeriya, mafi yawa 'yan jihar Kaduna, kuma Musulmi, su kimanin 347 a ramin bai-daya.

Na farko bai 6uyawa duniya cewa da umurninka sojoji suka je suka kai hari gidan Shaikh Zakzaky ba, domin a ranar da yamma bayan sun kewaye Husainiyya, ka je ka same su kun tattauna, ka basu damar hakan sannan ka wuce. Bidiyo din zuwan naka na nan.

Na biyu kuma: Sakatarenka ne ya furta a gaban kwamitin da kai ka kafata ta JCI cewa kai ka ba da umurnin a bizne gawarwakin mutane 347 alhali kowannensu an san gidansu, an san iyayensa, an san yan uwa da danginsa.

Shirmen banza ne kace wai ka shigar da Shaikh Ibraheem Zakzaky da matarsa Malama Zeenah kara a kotu, wai kana tuhumarsu da laifin kashe soja a yayin da sojojin suka kai masa hari cikin dare a cikin gidansa, suka kashe almajiransa fiye da dubu, suka kashe yayansa a kan Idonsa, suka kona gidansa, suka harbe shi suka fito da shi jina-jina, suka dauko hoto ma suka yadawa Duniya.

Kai al'ummar jihar Kaduna ke bi bashin jinanen da aka shekar musu bisa umarni da lamuninka! Kai al'ummar Jihar Kaduna ke bi hakkin gawarwakin Yayansu da ka taimaka ka sa hannu, ka ba da gudummawa sojoji suka bizne su a ramin bai daya a kauyen Mando, da sauran gurare.

Kai ka wa al'ummar jihar Kaduna laifi, kai ka kamaci hukuntawa a duniya da lahira Nasiru. Shaikh Zakzaky bai taba kashe kowa ba, bai taba zaluntar kowa ba, bai kuma taba tunzura kowa ya je ya zalunci kowa ba. Kuma duniya shaida ne a kan cewa yana da almajiran da suka sallama rayuwarsu a gare shi, amma yau shekara 4 kuna tsare da shi, duk sanda suka fito kan titi suna kira a sake shi kuma sakawa karnukanku suna bude musu wuta, amma basu taba ramawa ba, ba su taba kashe wani ba ko su barnata dukiyar wani.

Nasiru, babu shakka kai al'ummar jihar Kaduna ke bi bashin zaluncin da ka musu, kuma ko ba dade ko ba jima insha Allahul Azeem sai al'ummar jihar Kaduna sun dauki fansa a kanka da duk wanda ya jibince ka wajen zaluntarsu. Kafin ka je lahira ka hadu da fushin Allah Ta'ala akan izgili da kake da addininsa da bayinsa da kuma zaluntarsu da kake yi kana mai tinkaho da gadara."

Ya kuke Kallon wannan Al'amari?

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky