HABA DAKTAN MAƘARYATA KO ƊAN FIRAMARE ASIYASA YASAN WACE ƘASACE TAKEDA ALAƘA TA ƘUD'DA ƘUD DA AMERIKA.

Yanzu ka ce da Sani Rijiyar Lemo ya nuna a ina Iran ta ke a taswirar duniya to sai dai ka kwace limancinsa indai ba ka hada masa da sunan kasar a kan taswirar ba. Amma duk wata siyasar kasar sai ya shiga rediyo yana bayaninta. Ka ji tsoron Allah dakta. Duk abin da fa kake fada mala’iku suna nan suna rubutawa.

Kada ka ga wai don kasar yan Shi’a ce sai ka yi ta karya kana zaton ba komai. Irinku ne fa suka gaya mana wai yan Shi’a sun ce Jibrilu manta sako ya yi ya bawa Annabi Muhammad ba Aliyu bn Abi Talib ba, muka duba muka ga karya ne. Kuka ce mana yan Shi’a suna da nasu Quranin, muka shiga nema a kasuwa aka dinga yi mana dariya!

Ko dan firamare a siyasar duniya ya san cewa Saudi Arabia ita take da alaka ta kusa da Amerika. Kuma tun da aka yi juyin-juya-hali a Iran aka kifar da gwamnatin Shah ba a kara samun daidaito tsakanin Amerika da Iran ba. Amma wai an ce kai ka yi karatun nuna cewa bakin Amerika da Iran daya! Kai sai ka ce Amerika ba tare da Saudi Arabia suka hada kai wajen yaki a Yemen da Syria ba.

Sau nawa Trump yana cewa Israel da Saudi Arabia su ne kasahen da suke da interest a kansu a gabas ta tsakiya? Me ya hada Hezbollah da Iran take taimakawa da kuma Israel da Amerika ke taimakawa? Haba Sani Rijiyar Lemo! Meye a kwakwalwarka? Ko saboda rigimar Shi’a da Salafiyya sai duk ka rikirkice ka dinga fadar abin da kai kanka ka san wallahi karya ne.

Yanzu siyasar duniya ba abin kunya a ciki. Zamanin rufa-rufa da sunan addini ya wuce. Lokacin da ake turo “grants” don kare Saudi Arabia ya kare. Yanzu duniya a tafin hannun kowa take. Idan kun rainawa na baya hankali to na yanzu za su yi muku wuya domin da Google a hannunsu. Shekarun karairayi sun kare. Ka hakura da Saudi Arabia din nan domin za ta ci gaba da baka kunya har sai dan ragowar mutuncinka da bana gani ya karasa zubewa a idon duniya ta bangaren siyasa.

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky