HADARIN JIRGIN SAMAN ƘASAR UKRAIN KWAMANDAN DAKARUN KARE SARARIN SAMANIYAR IRAN YAYI ƘARIN HASKE.

Tabbas harbo jirgin fasinjar Ukraine da ya faru a Tehran bisa kuskuren dakarun kasar wani abin bakin ciki ne da ke bukatar jami'ai su yi dubi cikinsa don guje wa sake faruwar hakan. Sai dai a daidai lokacin da mu ke taya iyalan wadanda lamarin ya ritsa da su juyayin wannan rashi su kuma wadanda suka rasa rayukansu Allah Ya jikansa, har ila yau kuma jami'an kasar Iran sun cancanci jinjinawa saboda yadda suka fito suka yi bayani da kuma daukar nauyin abin da ya faru wanda bisa kuskure ne hakan ta faru. Shi kansa wannan jaruntaka ce babba da kuma girmama al'ummominsu.

Zuwa an jima da yardar Allah zan kawo maka karin bayani kan hakikanin abin da ya faru din ta bakin kwamandan dakarun kare sararin samaniya na Iran din, Birgediya Janar Amir Ali Hajizadeh.

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky