HARBO JIRGIN UKRANE BISA KUSKURE. Nashirya daukar duk wani hukunci da yadace dani- Birgedi janaral Ali Hajizadeh.

----
Nasir Isa Ali
Na shirya karbar duk wani hukunci daga hukumomi kan harbe jirgin kasar Ukiren (Ukraine) bisa kuskure.
---Birgediya Janar Ali Hajizadeh---
---
Babban kwamandar rundunar IRGC dake kula da tsaron sararin samaniyar kasar Iran,Birgediya Janaral Ali Hajizadeh ya bayyana cewar 'rundunarsa da aka kintsasu domin jiran ko-ta-kwana ne suka habo jirgin dakon farar hula na kasar Ukiren bisa kuskure a birnin Tehran.
Ya kara da cewar,babu rufa rufa a wannan lamarin,kamar yadda wasu ke fada,kawai an yi kokarin tabbatar da hakikanin abin da ya faru ne,kafin kuma a sanar wa duniya da mutane Iran sahihin labarin jirgin.
Yace lokacin da lamarin ya faru,shi yana can kudancin Iran yana kokarin kai hari kan Amurka,sai daga baya aka sanar da shi cewar,an harbo wani jirgi kusa da masaukin jiragen sama na Imam Khumaini dake Tehran. Yace ranar 8 ga wata ina kudancin Iran ne muna niyar kai wa Amurka hari,kuma mun kintsa rundunarmu a ko'ina cikin kasar da makamin kakkabo jirgin yaki,ko wani makamin da kila Amurka na iya harbo wa.
-
Don haka ni Ali Hajizadeh na dauki nauyin wannan kuskuren,kuma a shirye nake da in karbi duk wani hukunci kan hakan.
Yace an dora min nauyin kula da tsaron sararin samaniyar kasarmu,kuma na kintsa mutanenmu a ko'ina domin jiran ko ta kwana. Don haka wannan kuskure ne aka samu daga garemu.
Yace mai kula da tsaron samaniyar Birnin Tehran da kewaye ya samu siginal cewar,an harbo makami kan birnin Tehran din,don haka sai ya tashi makamin kakkabo makami (Cruise Missiles) domin kare birnin da mutanen ta. Amma sai aka samu kuskuren sadarwa aka harbo jirgin.
Ya kara da cewa,sam bai kamata a tuhumi ma'aikatan dake kula da tashi da saukan jirgin sama ba,domin basu san tanadinmu ba,kuma ba'a sanar dasu ba.
-
Yace na sanar da manyan kwamandojin mu kan ainihin abin da ya faru,kuma an kafa kwamitin bincike,kuma a shirye nake na karbai duk sakamakon inji Hajizadeh. Kuma da rundunar IRGC da rundunar sojan Iran,babu wanda yayi niyar yin rufa rufa da lamarin tun farko inji Hajizadeh.
-
Nasir Isa Ali.

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky