JAWABIN AYATULLAH EL'SISTANI AKAN HARIN DABBANCI AMURICA DA TAKAIMA DAKARUN IRAN A IRAQ
Ayatullah Sistani: Harin Dabbanci Ya Yi Sanadiyyar Shahadar Jan Gwarzon Da Ya Sami Nasara A Fada Da Daésh
~Daga Ishaq Mohd Kibiya
A wani bayani da ya fitar a yau jumaá, babban malamin addinin musulunci na kasar Iraki, Ayatullah Sistani ya mayar da martani akan shahadar Kasim Sulamani kwamandan rundunar Kudus, a sanadiyyar wani harin dabbanci akan kwamandojin da su ka sami nasara a fada da Daésh.
Kafafen watsa labarun kasar Iraki, sun ambato babban malamin addini na kasar yana yin kira ga wadanda lamarin ya shafa da su yi aiki kafada da kafada da gwamnatin Iraki.
An karanta bayanin na Ayatullah Sistani ne a yayin hudubar jumaá da aka karanta a birnin Karbala.
Bayanin na ayatullahi Sistani ya ci gaba da cea: “ A cikin saoín da su ka gabata manyan abubuwa sun faru a cikin kasar Iraki wacce ta ke fama da rikice-rikice, take kuma cikin wani yanayi mai hatsari; wadannan laifukan sun hada da kai wa sojojin Iraki hari a garin Kaím, wanda ya yi sanadin shahada da jikkata gwamman mayakanmu, haka nan kuma abinda ya faru a Bagadaza na takaici sai kuma a karshe harin dabbanci na daren jiya a kusa filin saukar jiragen sama na kasa da kasa a Bagadaza da hakan ya yi sanadin shahadar jaurman da su ka sami galaba akan Da’esh. Wannan harin yana nuni ne a fili da yadda Amurka ta keta hurumin kasar Iraki da kuma dokokin kasa da kasa.”
Wani bangare na jawabi ya kuma ce; “Wadannan abubuwan da su ke faruwa suna nuni da cewa kasar Iraki tana fuskantar yanayi mai wuya a nan gaba.”

Comments
Post a Comment