KOTUN ICC TAFARA BINCIKEN KISAN KIYASHIN DA SOJOJI SUKAYI A ZARIA

Daga Ammar M. Rajab

Kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya (ICC) ta bayyana cewa ta fadada bincikenta dangane da laifukan yaki da take hakkin bil’adama a Nijeriya wanda rundunar sojojin Nijeriya suka aikata akan mabiya Harkar Musulunci a Nijeriya.

Har wala yau kotun ICC din ta ce binciken na ta zai kuma shafi kisan da sojojin Nijeriya suka yiwa mabiya kungiyar masu rajin kafa kasar Biyafara wato IPOB.

ICC din sun bayyana hakan ne a rahoton taron su na shekarar 2019 dangane da ayyukansu wanda ofishin bincike na kotun duniyar wanda Fatou Bensouda ke jagoranta.

Rahoton wanda aka sanya masa kwanan watan 5 ga watan Disamban 2019, ya nuna cewa tun a ranar 18 ga watan Nuwamban 2010 aka kaddamar da fara binciken abubuwan da suka faru a Nijeriya. Har wala yau rahoton ya nuna cewa; ofishin bincike na ICC din, a ranar 12 ga watan Nuwamban 2015 ya gano; “Laifuka takwas na yaki da take hakkin bil’adama a karkashin makala ta 7 da 8 na ‘Roman Statutes.”

Haka zalika duk a rahoton, ya nuna cewa Nijeriya na daya daga cikin kasashen da suka kai mataki na uku a binciken da ofishin binciken laifuka na ICC din ke yi. Inda rahoton ya kara da cewa; a halin yanzu Nijeriya ta aikata manyan laifuka guda goma a maimaikon takwas da ake zarginta na yaki da take hakkin bil’adama. Wanda rahoton ya ce daga cikin laifuka goma din, kungiyar Boko Haram ta aikata guda bakwai, a yayin da jami’an tsaron Nijeriya suka aikata guda uku.

Ofishin binciken manyan laifuka na ICC ya bayyana cewa daga cikin abubuwan da ofishin ke bincika sun hada da kisan kiyashin ‘yan shi’a da jami’an tsaron Nijeriya suka yi, da kuma kashe ‘yan kungiyar IPOB da sauran rikice-rikicen kabilanci dake faruwa a jihohin Binuwe, Filato, da kuma sauran jihohin dake arewa ta tsakiya, da wani bangare dake arewa maso gabashin Nijeriya.  

Idan ba ku manta ba, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta haramta ayyukan Harkar Musulunci a Nijeriya, da kuma ayyukan IPOB, sai dai tuni Harkar Musulunci ta kalubalanci wannan kuduri na gwamnati a kotun daukaka kara.

Har wala yau a kwamitin binciken da gwamnatin Kaduna ta kafa domin binciken kisan kiyashin ‘yan shi’a a Zariya na shekarar 2015, kwamitin ya tabbatar da cewa sojoji sun yiwa ‘yan shi’a 347 kisan kiyashi a Zariya dake jihar Kaduna. Kuma rahoton kwamitin ya nemi da a hukunta duk sojan da yake da hannu wajen aikata hakan.

Sannan rahotanni sun tabbatar da cewa a cikin watan Satumban 2017, a atisayen Rawar Kada na II da sojojin Nijeriya suka kaddamar kan mabiya IPOB domin kawo karshen rajin kafa kasar Biyafara, sun kashe membobinsu da dama.

ICC a rahoton na su sun ce dangane da rikicin kabilanci dake faruwa a arewa ta tsakiya da arewa ta gabas, sun karbi bayanai 15. Sannan ta ce tana nan tana ci gaba da binciken zargin da ake yiwa Nijeriya na “kokarin biznewa da rushe duk wata hujja” dangane da kisan kiyashin mabiya Harkar Musulunci da sojoji suka yi.

Rahoton ya ce; “A lokacin tattara bayananmu, ofishin binciken ya yi kokarin tattara bayanai da gudanar da bincike dangane da zargin da ake yiwa jami’an tsaron Nijeriya kan kisan kiyashin mabiya Harkar Musulunci a Nijeriya a Disamban 2015 a Zariya dake jhar Kaduna.”
Rahoton ya kara da cewa; “sauran zarge-zargen da muke bincike sun hada da ayyukan jami’an tsaron Nijeriya kan membobin IPOB da rikice-rikicen kabilanci da yake aukuwa a arewa ta tsakiya da arewa maso gabas.” 

Shin kana da wani labari da kake son mu buga maka a shafinmu? Idan eh maza ka turo mana shi ta hanyoyi kamar haka:
voiceofsheikh@gmail.com

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky