SALLACEWAR SOYAYYA BAYAN AURE.da yanda za a magance ta.

*An bayyana Sallacewar dandanon Soyayya bayan Aure da rashin aza tubalinta tun farko saboda Allah.*

Daga *_Auwal Isa Musa._*

Malama Hadiza Wowo ta bayyana haka a lokacin da take gabatar da Lakca ga Ma'aurata,a wata Walimar Aure a ranar Alhamis din nan a Katsina.

Malamar ta ce,zamantakewar auren nan da ake yi tana da Ka'idoji da Sharudda da Allah ya gindaya kuma muke da abubuwan koyi a zamantakewar daga Fiyayyen Halitta Manzon tsira(S) wanda shi ne makura a wajen kowace irin kyakkyawar dabi'a,wadda har Allah ya lazimta mana koyi da shi a cikin dabi'un,amma abin takaici yau an wayi gari masu shirin yin Aure har ma da yawa daga wadanda suka yi auren, ba su da masaniyar wadannan ka'idoji ko kuma sun yi watsi da su suna aikata son zuciyarsu.

A wani bangare na jawabinta,Malamar,ta kuma Kalubalanci Masoyan da Soyayyarsu.                                                    ke disashewa nan-da-nan kafin aje ko'ina bayan Aure,inda ta kwatanta hakan da rashin aza tubalin Soyayyarsu akan Allah da Annabi tun da fari,alhali *"Shi aure ana yin shi ne domin Allah,ba don wani abu na daban ba"* -Inji ta.

Malama Wowo ta kuma gargadi Samari da 'yan mata masu biyewa kyal-kyali da gayu akasin tarbiyya da Addini a lokacin da za su za6i abokan zaman junansu tun da farko,inda ta misalta haka da cewa; akasari su ne zaman aurensu ke ta6arbarewa lokacin kadan da sun yi aure, karshe har auren ya kai ga lalacewa.

*"Saboda haka a aure Allah ake kallo ba kyale-kyale da gayu ba.A rika zama na Allah da Annabi(in an yi auren) ba a rika kuntatawa juna".*

Dangane da sanin dokokin aure kafin ayi shi kuwa,malamar ta raka lakcarta da yin bulala a fakaice da cewa,ya kamata Ma'aurata su rika sanin ilimin aure kafin su yi shi duba da yadda Allah ya tanadar da ukuba ga wanda ya tozarta shi ko wulakanta da shi ta kowace hanya,sananan sanin ilimin auren zai sa kwamacalar da ake yi a cikinsa wanda ya zama ruwan dare ga al'ummarmu a yanzu ya takaita.

*"Akwai hakkoki da yawa tsakanin miji da Mata wadanda suka dole a san su kafin a riga a yi auren kamar yadda Addini ya tanadar.Maimakon Hadisan kano(Litttafan karatun Hausa) da mata ke ke karantawa,ya kamata a maida kai wajen sani ilimin aure wanda shi ne abu mafi muhimmanci har a wajen Allah(T)".*

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky