TA'AZIYYAYAR 'YAN'UWA ALMAJIRAN SHEIKH ZAKZAKY(H) GA SHEIKH DAHIRU USMAN BAUCHI NA RASUWAR MATAR SA

Almajiran Shaikh Zakzaky sun je ta'aziyyar Matar Shaikh Dahiru Bauchi.

Daga Auwal Isa Musa.

'Yan uwa Musulmi Almajiran Shaikh Ibraheem Alzakzaky na Jahar Bauchi,sun kai ta'aziyya ga Shehin Malamin Addinin Musuluncin nan na 6angaren Darikar Tijjaniyya a Najeriya, Shaikh Dahiru Usman Bauchi a yau Laraba,bisa rasuwar mai Dakinsa wadda ta rigamu gidan gaskiya a ranar Lahadin nan da ta gabata.

Tawagar Masu ta'aziyyar dai tana a kalkashin jagorancin wakilin Shaikh Zakzaky na garin Bauchi,Shaikh Ahmad Yashi.

A yayin da suke kar6ar ta'aziyyar a mamadin Shaikh Dahiru Usman Bauchi,yalan Mamaciyar,sun kar6i ta'aziyyara hannu bibbiyu sannan kuma sun nuna jin dadinsu da wannan ta'aziyya.

Tun farko,da yake Jawabi a yayin ta'aziyyar,wakilin 'yan uwan na Bauchi Shaikh Ahmad Yashi ya bayyana wannan rashi a matsayin wani rashi mai daci,ba wai ga shi Shehin Malami Shaikh Dahiru Bauchi ko Iyalan mamaciyar ba, a'a har ma ga sauran Al'ummar Musulmi baki daya,domin kuwa uwace aka rasa.

Daga bisani, 'yan uwa Musulmin sun yi Addu'ar samun rahamar Allah wa Mamaciyar, tare da fatan Allah ya ba wa Iyalai da dangin mamaciyar hakurin jure wannan babban rashi.

Comments

Popular posts from this blog

TARIHIN SHEIKH ABUL FATHI MAIDUGURI

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA