Kotun Tarayya A Kaduna Ta Ba Da Odar Barin Likitocin Shaikh Zakzaky Su Rika Ganawa Da Shi A Gidan Yarin Kaduna.

SHARI'AR SHEIKH ALZAKZAKY: Kotun Tarayya da ke Kaduna a zamanta na yau Alhamis domin ci gaba da sauraren Karar da gwamnatin Jahar ta shigar akan wasu tuhumce-tuhumce da ta ke yi wa Jagoran 'yan uwa Musulmi Shaikh Ibraheem Alzakzaky da mai dakinsa Malama Zeenatu,Kotun ta ba da umurnin a rika barin Likitocin Shehin Malamin su rika duba lafiyar sa a cikin gidan Yari a duk lokacin da suka bukaci haka.

Shehin Malamin dai na ci gaba da tsarewa ne tun Watan Disambar 2015,biyo bayan kashe daruruwan Almajiransa, 'yayansa da wasu 'yan uwansa na jini a yayin da shi kansa da Matarsa ba su tsira daga halbin harsasan da Sojoji suka yi masu wanda har yau suke cikin rashin lafiya sakamakon illar da harsasan su kai masu a jiki.

Za dai a ci gaba da sauraren karar ne a ranar 24 da 25 na watan da muke ciki,bayan rashin halartar Malamin da Matarsa a zaman Kotun na yau sakamakon rashin lafiyar da ke su fama da ita, kamar yadda Lauyan Malamin Femi Falana ya bayyana.

Menene ra'ayinku akan wannan lamari?

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky