Kotu Ta Yi Wa Wani Matashi Hukunci Sakamakon Batanci Ga Shaikh Zakzaky.

Wata Kotu ta daure wani Matashin akan ya yi 6atanci da Hoton Shaikh Alzakzaky.

A ranar talatar na da ta gabata (4/2/2020) ne, wata Kotun Majistare da ke Potiskum jihar Yobe ta yanke wa wani matashi mai suna Mohamad Garba hukuncin daurin watanni shida a gidan kaso ko kuma tarar Naira dubu 10,000 a bisa samunsa da laifin 6ata sunan Malamin Addinin Musulunci shugaban 'yan uwa Musulmi a Najeriya, Shaikh Alzakzaky,ta hanyar amfani da Hoton Malamin a cikin wani bidiyon 6atanci da ya yi wa wasu Mata ya sakie shi a kafafen sadarwa.

Bidiyon mai tsawon mintuna biyu da dakika 40 da Matashin ya saki kafafen sadarwa na zamani a ranar 26 ga Janairun 2020,ya nuna yadda yake 6atanci ga wasu matan da ba su da Hijabi a jikinsu yana kuma tallatasu da cewa "ana gwanjonsu",a inda daga karshen bidiyon ya dauka da Hoton Malam Alzakzaky, sakamakn haka Almajiran Malamin suka yi kararsa da sunan ya yi 6atanci da zub da Mutunci wa Malamin nasu.

Almajiran Malamin sun binciko matashin sukakuma damkashi a hannun 'yan sanda,su kuma ba su yi wata-wata ba suka mika shi Kotun Majistare da ke Karamar Hukumar Potistum a ranar 26 ga Janairun 2020.

Bayan shafe kwanaki biyu ana gabatar da shaidu a shari'ar, an tabbatarwa matshin da laifinsa kuma shi ma ya amsa laifin da ake tuhumarsa,in da ya bayyana haka a matsayin kuskure da yake neman afuwarsa.

Duba da yadda ya amsa laifinsa ba tare da ya ba shari'a wahala ba da kuma magiyar da yayi da cewa ya tuba,mai shari'ar Alkali Alagarmo ya yankewa masa hukuncin wata Shida a gidan kaso ko kuma tarar Naira dubu goma.

Ko irin wannan hukuncin zai kawo karshen 6atanci ga mutane masu kima a kafafen sadarwa duba da yadda lamarin ya zama ruwan dare a Najeriya?

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky