Labaran Kanzon-Kurege: Malamin Addini Ya Gargadi Masu Rubuta Labarun Karya A Kafafen Sadarwa.

An tsoratar akan rubuta labarun kanzon-kurege a kafafen sada zumunta na zamani.

Daga Auwal Isa Musa.

An tsoratar da kuma yin gargadi dangane da rubutawa tare da yada labaran karya da suka zama ruwan dare a kafafen sada zumunta na zamani(social media).

Malamin addini a 6angaren 'yan uwa musulmi a Katsina,Shaikh Yakubu Yahaya Katsina ne ya yi wannan jan hankalin a lokacin da yake gabatar da lakca a wani taron karawa juna sani na kwanki biyu akan 'hanyoyin da za a kaucewa yada labarun kanzon-kurege da yadda za a cin moriyar kafafen sada zumunta na zamani' wanda 'yan uwa musulmi almajiran shaikh Ibraheem Alzakzaky suka shirya a karshen makon nan da ya gabata a Katsina.

Malamin ya bayyana cewa,lallai a guji rubutawa da yada labarun karya wadanda ba su da makama balle tushe a cikin wadannan kafafe duba da yadda hakan ke tasiri ga al'umma cikin dan karamin lokaci,wanda su kan haifar da hargitsi da tada fitina da dasa kiyayya a tsakanin juna,inda yace "Kar ya zama karya muke yadawa,ya zama gaskiya muke yadawa" musamman mu musulmi da aka haramta mana yin karya, ko ba kome za a tambayemu abin da duk muka aikata a ranar gobe Alkiyama ciki hada abin da muka rubuta ko muka tura.

"Ina kira ga 'yan midiya da su hau kan turbar gaskiya.Idan kun fadi maganar gaskiya; Allah zai inganta aikinku,ko kuskure ku ka yi Allah zai 6oye kuskurenku"

Har wayau,shaikh Yakubu Yahaya ya kuma nasihanci masu t'ammui da kafafen yada labarai da kafafen sada zumunta na zamani da cewa; su san me suke rubutawa kuma su san don mi suke rubutun,Ka da su kasance masu yada labaran da za su rika kawo shubuhohi ko haifar da fitintinu a tsakanin al'umma, inda yace a rika amfani da kafafen da ikhlasi da kuma tsoron Allah.

"Muna da bukatar Ikhlasi(tsarkin zuciya) kuma da shi Allah ke aiki.Ikhlasi wani abu ne daga cikin asrar(sirrai) na Allah da yake saka shi a cikin zuciyar bawan da yake so,wanda ko shaidan ba ya iya ganinsa(ikhlasin),kuma Ikhlasi shi ke fadada aikin bawa.
"

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky