MALA'IKA JIBRILU SAIDA YA SHAWARA NB DA ANNABI LOKACIN DA ZAI FARA YIMASA WAHAYI. Ba maƙure shi yayi ba

"Mala'ika Jibrilu sai da ya nemi Izinin manzon Allah ranar da ya fara kawo mashi sako,ba makure shi yayi ba" -Shaikh Yakubu Yahaya Katsina.

Daga Auwal Isa Musa.

A cikin Jawabin da Malamin Addinin Musuluncin nan a 6angaren 'yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Yaqoub Alzakzaky na Katsina, Shaikh Yakubu Yahaya ya gabatar a ranar Lahadin nan na tunawa da ranar Yaumul-mub'ath wato ranar da aka fara aiko manzon Allah(S) da Sako zuwa ga Talikai,Malamin yace; Mala'ika Jibrilu(A.s) bai ta6a razana manzon Allah(S) balle makureshi ko kuma wahalar da shi ba tun da yake zuwa kawo masa sako,bilhasali ma yana neman izininsa ne a duk lokacin da yazo garesa.

Malamin ya kara da cewa; a lokacin da Manzon Allah ya kai shekara Arba'in. sai Allah ya turo mala'ika Jibrilu da sakon Annabta da Ayar nan ta 'Ikra'a,amma da yazo ya sami Manzon Allah a kogon Hira sai da ya nemi izin shiga wajensa,ba matse shi yayi ba:

 "Wata ruwayar a falke (Jibrilu) ya sameshi (Manzon Allah) a cikin natsuwa.Yai masa Sallama, 'Assalamu alaika ya rasulallah'. Ya amsa masa yace; 'Wa'alaikassalamu wa rahmatullah'. Yace; in shigo? Sannan yace shigo. Kaga ba maganar makurewa."

Ya ci gaba da cewa; "Wannan ya faru ne a ranar Litanin 27 ga Rajab kamar yadda yake a ruwayar Ibn Abbas, duk Imamiyya sun yi Ittifaki akan haka,kuma shi ya fi karfi a cikin Sunnah.

Ya kara da cewa: "Wansafake ranar Talata sai Jibrilu ya sake dawowa da Suratul Fatiha da Suratul Ikhlas.Sannan sai Jibrilu yasa kafa ya shuri Kasa,sai ruwa ya 6u66ugo,sai yai Alwala Manzon Allah ya gani;sai shi ma ya yi,sannan sai aka farlanta ma shi Salloli guda Biyar.Wannan Hadisi(na Isra'i da Mi'iraji) cewa an farlanta mashi Salla biyar, ya dawo Musa yace ma shi koma,ya dawo yace koma, har suka dawo sallah biyar; ba su da Inganci. Ba Sahihai ba ne. Sahihin Hadisi shi ne wannan wanda Iyalan gidan Annabi suka ce haka akai."

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky