MUN SAKE KADA GWAMNATIN KADUNA A KOTU

Takardar Sanarwar Manema Labarai:

MUN SAKE KA DA GWAMNATIN JIHAR KADUNA  A KOTU

Harkar Musulunci a Nijeriya a ranar Juma’a, 21/2/2020 ta kara samun nasara a hukuncin da babbar kotun jihar Kaduna ta yanke a kan karar da aka shigar na sauran ‘yan’uwa Musulmi da ake tsare da su tun cikin watan Disambar shekarar 2015 biyo bayan mummunan harin da Sojojin tarayyar Nijeriya suka kaddamar a Zariya. Kotun ta wanke tare da sallamar dukkanin wadanda ake zargi su kusan dari, abin da ke tsame Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya da ma mabiyansa daga aikata duk wani laifi na lamarin da ya kai ga kisan kiyashin Zariya.

Wannan yanke hukunci ya kawo karshen shari’ar da aka kwashe shekaru hudu cur ana kwafsawa, inda gwamnatin Jihar Kaduna ta yi karar kimanin ‘yan uwa Musulmi na Harkar Musulunci kusan dari biyu bayan harin da Sojojin Nijeriya suka yi a cikin watan Disambar 2015, wanda ya sabbaba kashe rayukan fararen hula sama da dubu daya wadanda ba su aikata laifin komai ba, tare kuma da yi wa gawawwakinsu kabari na bai daya a asirce. To daga cikin wadanda suka tsira da ransu a yayin mummunan harin ne kuma gwamnatin Jihar Kaduna ke zargin su bisa karya, Kotun ta wanke tare da sallamar kimanin mutane dari daga cikin su tun a ranar 31 ga watan Yuli, 2018. Dukkanin sun fuskanci tuhumomi marasa tushe da suka hada da yin  kisan kai ba da gangan ba wanda hukuncinsa kisa ne.

Kazalika a wannan rana ta yau, gwamnatin jihar Kaduna ta kara shan kaye a gaban kotu bayan shari’ar da ta gudana cikin adalci. Wannan hukunci babbar nasara ce ta gaskiya da adalci a kan zalunci da danniya. Haka nan kuma wannan hukunci babbar nasara ce ta hakuri da juriya a kan bakin zalunci da gallazawa.

Tare da wannan nasara a yau, tuhume-tuhumen boge da aka shigar a kan Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky da mai dakinsa Malama Zeenah Ibraheem na tunzurawa da taimaka wa wadannan da aka sallama kan aikata kisan kai sun fadi kasa ba nauyi. Wannan cikakkiyar galaba da nasara da muka samu a Kotu ta kara tabbatar da cewa Harkar Musulunci a Nijeriya da kuma Jagoranta sune aka zalunta dangane da bakin zalunci da kuma makirci na gwamnati. Don haka muna kira ga gwamnatin Jihar Kaduna da ta yi wa kanta kiyamul laili ta janye tuhume-tuhumen karya da ta shigar a kan Shaikh Zakzaky da mai dakinsa Malama Zeenah, ta kuma sake su ba tare da wani bata lokaci ba.

Muna kara jaddada godiyarmu ga Allah Madaukakin Sarki dangane da wannan gaggarumar nasara da muka samu a gaban Kotu. Haka zalika za mu so mu yi amfani da wannan dama wajen bayyana dimbin godiyarmu ga dukkanin mutane ma’abota hankali da adalci, ‘yan rajin kare hakkin dan Adam da kuma Kungiyoyi kare hakkin Bil’Adama, ‘yan Jarida da ma dukkanin mutanen da suka goya mana baya wajen wannan fafutuka tamu ta ganin an yi adalci ga wadanda kisan kiyashin Zariya ya rutsa da su. Mun gode, Allah Ta’ala ya yi maku albarka.

SA HANNU:
IBRAHIM MUSA
SHUGABAN DANDALIN YADA LABARAI NA HARKAR MUSULUNCI A NIJERIYA
SKYPE: Ibrahim.musa42
21/02/2020
Fassarar Zaharaddeen Sani Malumfashi.

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky