NIFA ABINDA ZANCE SAIDAI AYI HAƘURI DANI- Bilya Hamza Dass

Angama Maganan Kotu Ko? To Ni Ga Abinda Zance, Sai Dai Ayi Hakuri Dani.

Abokin ku, Bilya Hamza Dass

Nagama ganin 'yan uwa sunyi ta kawo rahotannin abinda yafaru a kotu yau harda zuwa hutu da kuma dawowa da yanda aka kare har bada doka ta biyu da Alkali ya bayar na cewa lalle abaiwa likitotin su Mallam daman ganin su ko yaushe. Tare da maganan sake sanya watarana da akace kamar 23 da 24 na watan 4 domin cigaba da zaman! Toh!

Allah yafada a littafin shi me tsarki cewa; baze taba daura kafirai akan masu imani ba. Wani wajan yace; 'Hakki ne akan mu mu temaki masu imani' (Aya). To gashi munyi imani kuma har mun zamu “Victims” na imanin mu ga Allah ta'ala kuma gashi azzalumai nata kadamu da cutarwa menene ke faruwa?

Karka raba 1 zuwa 2, magana ta Allah bamu shirya tsakanin mu da Allah bane. Ranar wanka be kamata ayita boye ciki ba, domin shima yana bukatan a wanke shi. A baya muna hangen munanan ayyuka daga wajen mu muna bada misalai dasu muna gujewa tare da addu'o'in neman tsari, amma bamusan yaya aka wayi gari ba, misalan mu da abubuwn da muke kallo a nesa damu suka dawo cikin mu suka samu wajan zama! Menene ke faruwa? Mun kauce usulin tsarin kiran, kuma munata “pretending” nuna cewa lalle akai muke.

Watarana, muna hira da wani Uba kuma Malami a wannn harkar da nayi masa wannan tambaya sai yace, kila kodan muma mun zama Al'umma ne shiyasa dabi'un al'ummar suka maye jikkunan mu. To amma ni bana kallon haka a wani hujja da zaisa mu koyi munanan dabi'un daga makofta ko abokan zama. Saboda tarbiyan mu, malamam mu, tsarin mu da makaranrun harma da littafan mu daban ne da nasu to dan me zamu kwaikwaye su? Halain da muke ciki yanzu babu wani kaba'ir da ake bada labari daga wajen tafiyar nan wanda be samu gurbi ba a cikin tafiyan yanzu haka.

Cikii harda shaye-shaye ga maza, da kuma yawace-yawace ga mata tare da zuwa wajan Boka ga manyan mata da tauye hakkin Iyalai ga Iyaye Maza! Da kin karatu ga Matasa da raina Iyaye da Malamai! Subhanallah. Wallahi wannan ba tarbiyan su Mallam (H) bane. Bafa da wani nake ba da kaina nake! Me kake tsammani? Shin zamu yiwa Allah wayo ne? Mun aikata munanan ayyuka ranar Lahadi ranar Litinin kuma mufita neman dacewa? Allah ne fa ba mutum ba.

A baya anyi wasu mutane a harkar nan da idan sukaso Allah yayi abu wallahi suna roka yakeyi nan take. Akwai Misali dayawa game da haka. Meya jawo haka sun gayara kawukan su sun koma ga Allah sun zama nashi, shima sai ya zama nasu. Na'am Mallam Mumini ne Salihi kuma ya dauko aiki me nauyi daga Allah ta'ala dama akwai tabbacin jarabbatan tsayuwar zukatan su daga mahaliccin su, kuma su su Mallam sun san da akwai tabbataccen tsaayayyen lokacin ajalin wannan waki'a.

Na'am, 'yan uwa nason a fito a kwama wato ayi fito na fito tsakanin mu da azzalumai to tambaya su waye azzalumai kuma suwaye adalai? Su waye na Allah su waye na shedan? Mu ko Su? Kwanaki a nan kafar na sanya mana maganan su Mallam (H) inda wani buraza ke tambayar su Mallam cewa yaushe za'a kwama? su Mallam sukace sai ranar da muka zama Adilai masu tsoron Allah, yayin da azzalumai sunyi nisa a zalunci sai azo a kwama tsakanin mu dasu, kuma akwai tabbacin nasara a wajan mu, inji su Mallam (H).

Yaya Allah zai amsa addu'a ga bawan daya kasa sauke hakkin iyalan shi? Mace da take cutar da Mijin ta da kishiyar ta? Dan uwan da yake zalunta dan uwan shi? Abokin dayake kazafi ga Abokin shi? Matashin da baya kula da Sallar Farilla balle ta Nafila, babu takawa babu tsoron Allah a zukata! Musulami sun koma wani abu daban, suba kafirai ba kuma ba asalin musulmai ba!

Muzahorin mu zasu kasance basu da tasiri matukar bamu buya mun gyara tsakanin mu da Allah ba. Fuskokin mu a kan titi zasu zama abin burgewa ga wawaye ne kawai da kuma kyama ga Adilai tare da ban dariya ga azzalumai. Hanya daya zamubi shine muzama na kwarai da Allah keso, idan ba haka ba zamu zama munyi kamanceceniya ta wata fuska dasu Azzaluman. Allah ya kiyaye. Wajibi mudawo ga Allah mu tuba mu kaskantar dakai muna masu kuka gareshi sai ya amsa mana yana mai cikar iko kan halittu baki daya.

Shiyasa idan ance Jahiliyya basajij Muzahara wasu basa yarda ni wallahi na fara yarda to babu kamala a fuskata na fita titi halama wani dan kallon dake gefe yafini kusanci ga Allah. Ai dama ba yawa muke alfahari dashi ba, sai dai Allah. Idan mutum 10 suka samu yardan Allah suka fita sunfi 1000 irina mu fita. Ba ina haka fita bane, a'a ina kokarin kawo gyara da kuma tabbatar da fitan ne.

Bazan tsawaita ba, babu wani abu dana fada ina mejin dadin shi cikin rubutun nan, kuma babu abinda na kirkiro domin nayi ado ga rubutun. Wallahi da zuban hawaye na karasa rubutun, hasalima wasu abubuwan inada hujjoji da misalai akan su. Allah ka yafemana ka tausaya mana!

—Abokin ku, Bilya Hamza Dass

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky