SABON MAKIRCIN EL'RUFA'I GA SHEIKH ZAKZAKY

Shari’ar ‘Yan’uwa A Kaduna: Sabon Makircin El-Rufai Ga Shaikh Zakzaky

Daga Ammar M. Rajab

Idan ba ku manta ba gwamnatin Kaduna a karkashin gwamna Nasir El-Rufai ta gurfanar da ‘yan’uwa Musulmi almajiran Shaikh Zakzaky kusan 200 a kotun Kadunan tun bayan kisan kiyashin da sojojin Nijeriya suka yi a kan ‘yan’uwa a ranekun 12-14 ga watan Disamban 2015.

Da yammacin ranar Talatar 31 ga watan Yulin 2018, Alkali D.S. Wyom ya kori karar da gwamnatin Kaduna take yiwa ‘yan’uwa Musulmi almajiran Shaikh Zakzaky kusan 100 inda ta wanke su tare da sakin su.

Dama shari’ar ta ‘yan’uwa an raba ta gida biyu ne, inda tun bayan wannan sakin, aka ci gaba da shari’ar dayan bangaren. Wanda ya zuwa hada rahoton nan tuni aka kammala karbar duk wata shaida, inda Alkaliya yanke hukunci kawai ake jira daga gare ta. Sai dai wata majiya mai tushe ta tabbatar mana da cewa; hukuncin wanda Alkaliyar ta kasa yanke wa a zama biyu hakan ya faru ne sakamakon barazanar da gwamnan Kaduna yake yi mata.

Rahotannin sirri daga majiya mai tushe ta kara tabbatarwa da MUJALLAR GWAGWARMAYA cewa; gwamnan na Kaduna ya nemi Alkaliyar da ta yanke hukunci mai gauni akan ‘yan’uwan, kuma ka da ta saki ta sake su, sai dai ita kuma Alkaliyar ta nusasshe da gwamnan cewa tana bisa doka ne ba karkashin gwamnan Kaduna ba. Duk da wannan amsar, majiyar ta ci gaba da cewa; “Bayan ya kasa cimma wannan, ita ma Kwamishiniyar Shari’a ta Kaduna, Aisha Dikko da Cif Joji na Kaduna sun nemi Alkaliyar da ka da ta yadda ta yanke hukuncin da zai sa a saki ‘yan’uwa, inda Alkaliyar ta sake jaddada musu cewa; tana bisa doka ne ba karkashinsu ba.” in ji majiyarmu.

Har wala yau majiyar ta tabbatar mana da cewa; gwamnan na Kaduna ya yi nuni da cewa idan har kotu ta saki wadannan ‘yan’uwan a hukuncin da kotun za ta yanke, to shar’ar da ake yiwa Shaikh Zakzaky da matarsa bisa zargin aikata laifuka takwas ciki harda kisan kai (iri daya da wadannan ‘yan’uwan), to shari’ar ta mutu murus. Domin kuwa zargi ne iri guda da gwamnan yake yiwa Shaikh Zakzaky, kuma a baya, kotu ta saki ‘yan’uwa kusan 100 akan irin wannan zargin, sannan kuma tana son sakin wasu kusan 100 din.

A ranar 28 ga watan Maris din 2019, kotun daukaka kara a Kaduna ta yi watsi da kararraki biyu da gwamnatin jihar Kaduna a karkashin El-Rufai ta kawo gaban kotun tana mai bukatar kotun daukaka karar ta soke hukunci da manyan kotu biyu suka yi a Kaduna na saki tare da wanke ‘yan’uwa Musulmi mabiya Harkar Musulunci a Nijeriya ku san 100.
Daukaka karar farko da gwamnatin jihar Kaduna ta yi, tana kalubalantar hukuncin kotu wanda ta yi a cikin watan Nuwamban 2017 inda ta wanke ‘yan’uwa Musulmi guda 15 wadanda aka kama su a yayin da suke gudanar da muzaharar Allah wadai dai da kisan kiyashin Sojoji a Zariya da kuma neman a saki Shaikh Zakzaky kwanaki kadan bayan ta’addancin Sojojin. Inda gwamnatin Kaduna ta gurfanar da su a gaban kotu bisa zarginsu da yin taro ba bisa umurni ba, da kuma raunata ‘yan Sanda da sauran jami’an tsaro, zargin da Kotun ta yi watsi da shi tare da wanke dukkanin ‘yan’uwa 15 da ake yiwa wannan zargin bayan an kwashe ku san shekaru 2 ana shari’ar.

Sai batun hukuncin kotu da gwamnatin jihar Kaduna ta daukaka kara shi ne; saki tare da wanke ‘yan’uwa Musulmi ku san 100 da wata kotun jihar Kaduna ta yi wanda aka kama tun lokacin kisan kiyashin Sojoji a Zariya cikin watan Disamban 2015. Inda gwamnatin jihar Kaduna ta gabatar da su gaban kotun bisa zarginsu da laifuffuka daban-daban ciki harda kisan kai.

Bayan kwashe shekaru biyu da rabi ana fafata shari’a a kotun, a karshe kotun ta wanke ‘yan’uwa daga dukkanin wadannan zarge-zarge, tare da sakin su.

Idan mai karatu bai manta ba, irin wadannan zarge-zargen da gwamnatin jihar Kaduna ta yiwa ‘yan’uwa Musulmi kuma har kotuna suka wanke su da sakin su, irin shi take yiwa jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky. Ganin cewa; gwamnatin ba ta da wani hujjar gabatarwa da kotu, shiyasa suke ta jan shari’ar duk da cewa; har yanzu Shaikh Zakzaky da matarsa na fama da matsanancin rashin lafiya tun 2015. Domin har yanzu akwai harsasai a  jikinsu da ba a cire ba.

Wannan shi ne sabon kulli na makirci da Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ke kullawa a shari’ar da ake yiwa Shaikh Zakzaky wanda za a koma a ranar Alhamis 6 ga watan Fabarairun 2020.

Daman kamar yadda kuka sani, shari’ar kamar wasan kwaikwayo ne aka shiryata domin ci gaba da rike Shaikh Ibraheem Zakzaky da matarsa domin kuwa gwamnatin har yanzu ta kasa gabatar da wata hujja a gaban kotun, kuma har yanzu kotun ba ta yi wannan takamaimen zama dangane da shari’ar ba.

A yayin harin ta’addancin sojojin Nijeriya akan Shaikh Zakzaky da mabiyansa, sojojin sun kashe sama da 1000+, tare da jikkata da dama, da kuma raunata Shaikh Ibraheem Zakzaky da matarsa da kuma kashe masa ‘ya’ya hudu.

Tun bayan wannan aikin ta’addancin ne dai, gwamnatin Kaduna ta maka ‘yan’uwa kusan 200 a kotun Kaduna tana zarginsu da laifuka ciki kuwa harda kisan wani soja a yayin ta’addancin sojojin.

@MujallarG
@04022020

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky