TARON MATASA KARO NA 27 A GARIN BAUCHI- Nasihohin Sheikh yaqub yahya katsian.

Taron Matasa Karo Na 27 A Garin Bauchi: Rahoto Na Biyu:

Nasihohin Sheikh Yakubu Yahaya Ga Matasa

Daga Bilya Hamza Dass

“Ba sai anzo wajan taro (Mu'utamar) kafin a dinga tashi ana sallar dare ba, wannan wani abu ne muhimmi, hasalima yana daga cikin manyan alamomi da ake gane mumuni” inji shi. A wani bangare na jawabin nashi babban bako me jawabi a wajan Sheik Yakubu Yahaya yaja hankalin matasa wajan kula da Ibada musamman a shekarun su na matasan taka. Yace “Abinda su Mallam suke so shine su samar da wasu mutane wadan da Allah zai damka musu amanar al'umma, wadanda zasuce Allah yayi kuma yayin” kuma wannan alkawari na shi.

Yakawo misalai yanda Allah yake zabar wasu dai-daikun bayin shi ya damka musu amanar al'umma, yayin da yaga tsaran su greshi da kuma amanar su. Misali Imam Kumai ni (R) da Shehu 'Dan Fodiyo wadanda wadanan sun faru shekaru kadan baya. Yace to wannn shine hankoron su Mallam (H) yace ya bayyana ba sau daya ba, cewa babbn gudumawa da wani zai bayar ga wannn harka shine yazama na kwarai, bi ma'ana ya garu da kyautatawa irin yanda Allah keso. Kuma yayi kokarin samun yarda daga Allah ta'ala wannan shine hadafin farko kuma mafi girma na wannan kira (Da'awa).

Su Mallam sun samar da dukkan tsari da yanda mutum zai bi yazama ya amfanu al'umma. Dayake magana kan ina matsalar take, yakawo fadin Allah ta'ala dayake cewa; bazai taba wassada kafirai akan musulmai ba. Kuma Alkawarin Allah gaskiya ne baze canza ba, to amma me yafaru yanzu kafiran duniya ke kada mutane kaman tumaki? Menene matsalar? Akwai matsala? Eh lalle akwai matsaloli ma ba matsala ba. Inji shi. Yace babban matsalar al'ummar musulmi sun kauce tsarin addinin Allah ta'ala, shiyasa suke ta shan wahala, kuma babu wata mafita me sauki ko me wahala daya wuce adawo akoma ga wannan addini.

Daya zurfafa cikin Nasihohi ga Matasa, Shehin Malamin yace, abubuwa dayawa sun dauke hankalin matasa ga yin ayyukan alheri yabada misali da “Handset” wayar hannu yayi amfani da kalmar “Charting” inda yace sai matashi ya shiga nan yashiga nan, har tsawon dare sai zuwa karfe 2-3 sai ya kashe ya kwanta babu sallar dare. Wanda yace a baya idan dan uwa yazo wajan dan'uwa sai kaji yana cewa, temakeni da addu'a yanzu bana tashi sai karfe 3 na dare, wanda a baya karfe 1 zuwa 3 nake tashi! Yanada misali.

A gefe guda yasake kwankwasan matasan da maida hankali ga biyayya da kuma neman ilimi a lokaci guda na kiwanne bangare. Ba'a bautawa Allah dole sai da ilimi, shine hanyar da zaka san Allah. Yayi magana sosai kan abinda ya shafi hanyoyin dogaro dakai da yanda 'yan uwa zasu hadu a wani adadi su temaki kansu, wanda yace da irin wannan salo ne watarana zamu wayi gari tattalin arziki yadawo hannun mu. A rubutu na gaba zan kawo hanyoyin da ya kawo da irin salon daza abi domin samu kafuwa daka.

—Bilya Dass
voiceofsheikh@gmail.com

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky