WAYASANI MA KO RASHIN GYARUWAR MU KE DAKATAR DA FITOWAR SU MALAM

Waya Sani ma Ko Rashin Gyaruwar Mu Ke Dakatar Da Fitowam Su Mallam (H) Din?

Eh, to! maganan Gaskiya, kowanne cikin mu yasan abinda ke aikatawa a boye a hasken rana ko cikin duhu. Yau da ace a tara dukkanin matasan wannan harkar wadanda suke Dass, Bauchi, Kano, Katsina Abuja da Sokoto dama Zariya da Kaduna dama dukkan sauran yankunan kasar nan, bansan yawan mu ba amma nasan lissafin Miliyoyi za'ayi kuma tabbas munkai haka. Ba ina magana yara bane, a'a matasa da suka mallaki hankalin su.

Ace mana kowannen mu ya biya hakkin shuhada da ake binshi bashi na baya, wallahi da zamu biya, adadin kudin zai iya sayan babban mota da Jari dukkan iyayen Shahidan harkar nan duka! Kuma yabada dama a biya kudin makarantan 'ya'yan Shahidai su zama lauyoyi da Injiniyoyi da likitoti wallahi ba wasa nake ba. Amma meke faruwa? Bamu da kudin ne? A'a kawai bamu gama yarda gaskiya muke kai ba. Kuma bamu girmama maganan Jagoran harkar.

Nasan akwai iyaye a cikin mu, ko kaine akace maka wannan harkar gidan kane 'ya'yan Harkar 'ya'yan kane idan baka da zuciya me fadi wasu abubuwa zasu sanya kadugu kabar gidan da 'ya'yan, anan bawai inason nayi Misali da su Mallam (H) bane. Inason mugane wani abu ne anan me muhimmancin gaske. Yau ace harka tazama sansananin kulla abubuwa marassa dadi.

Ace wancan baya magana da wancan? Wancan tana jin haushin wancan, wani na kokarin cutar da wani, wancan yayi rubutu ya zagi wancan, wancan yayi waka ya zagi wancan, kowa na yin abinda yaga dama sa sunan addini kuma.

Dan Allah idan su Mallam suka dawo sukaga daga mutum miliyan 20 mun koma Miliyan 40 amma Halayan mu ya lalace da Kaso 50 cikin 100 zasuji dadi? Muji tsoron Allah kar munanan ayuukan mu suzama tabo a zuciyar wannan Salihin bawa.

Kowa ya zargi kanshi, kar ya zargi wanin shi. Mu gyara kan mu ko Allah zai tausaya yadawo mana da Mallam cikin mu.

—Abokin ku, Bilya Hamza Dass

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky