RAHOTON BBC HAUSA DANGANE DA MALAM ZAKZAKY A GIDAN YARIN KADUNA

Hatsaniya a gidan yarin Kaduna inda ake tsare da El-Zakzaky Mintuna 12 da suka wuce —BBC Hausa. Sheikh El-zakzaky na tsare a hannun gwamnati tun 2015 Wasu fursunoni da ke babban gidan yarin Kaduna sun tayar da yamutsi inda suka bukaci gwamnati ta sake su saboda fargabar kamuwa da coronavirus. Rahotanni dai sun ce an yi yamutsin ne bayan wasu fursunoni sun nemi a sake su suna masu ikirarin cewa wasu fursuna biyu sun mutu sakamakon coronavirus. Sai dai shugaban gidan yarin Sanusi Mu'azu Dan-Musa, ya shaida wa BBC cewa batun mutuwar fursunonin ba gaskiya ba ne. A babban gidan yarin na Kaduna ake tsare da shugaban kungiyar 'Yan Uwa Musulmi ta Islamic Movement in Nigeria Sheikh Ibrahim Zakzaky da mai dakinsa. Rahotannin sun ce 'yan sanda sun rika harbi a iska da kuma rufe hanyoyin shiga gidan yarin domin hana fursunonin tserewa. Hakan ya sa kungiyar ta 'Yan Uwa Musulmi, a sanarwar da kakakinta Ibrahim Musa ya aike wa manema labarai ta yi kira ga dukkan hukum...