WANI BAƘON AL'AMARI DA YA KUSA YA FARU A ƘASAR IRAN DUK DA HALIN DA DUNIYA TAKE CIKI


Wani bakon abu ya so ya faru a Iran cikin wannan mawucin halin.
-
A ranar 23 ga wannan watan na Maris ne hukumar dake kula da yada labaran kasar Iran (IRIB) ta fitar da wàni faifan bidiyo wanda a ciki aka hasko hoton wani jirgin yaki kirar F-18 Jet Fighter ya doso kasar Iran gadan gadan,inda irgin ya sato hanya ta tekun Gulf zai bullo ta gabashin kasar.
 Wannan lamarin ya faru ne a ranar 20 ga wannan watan na Maris.
Ganin haka ne yasa sashin sojan Iran dake kula da tsaron sararin samaniyar kasar suka kintsa domin kaddamar da aikinsu kan wannan bakon jirgin.
Amma bisa tsarin tsaro na jumhuriyar musulumci,sai da aka yi masa gargadi sau uku,sannan sai aka bayyana masa cewar ya fa shiga hatsari domin yana tsallakawa Iran zai ji shi a kasa,sai jirgin yayi wuf ya juya ya tsere.
-
Haka zalika har an seta jirgin za'a harba masa wasu makamai masu linzami, amma sai ya taki sa'a ya dauki gargadin da aka yi masa ya tsere abinsa.
Har yanzu Iran bata fito ta nuna kasar da ta turo jirgin ba,duk da cewar sun dauki hoton jirgin,kuma an bi sawunsa har zuwa masaukinsa, amma ba'a fitar da sunan kasar da ta turo jirgin ba,kila ko sai nan gaba.
Amma ana zargin cewar,tun lokacin da Jagora Imam Khamnei yayi 'FATAWA' kan cewar duk jami'in da ya rasa ransa wajen yakar Corona-Virus yayi shahada. Ganin cewar hankalin sojojin Iran da jami'an tsaron kasar ya koma kan yakar Corona-Virus gadan gadan,shi yasa makiya suka yi yunkurin yin latsi su gani ko akwai wata kofar da ba'a rufe ba domin su yi amfani da ita wajen cutar da Iran din.
-
Wannan ne yasa Hafsan Hafsoshin Iran, Janar Muhammad Husain Boqare ya fito fili ya yi wa makiya kashedin cewar,Corona-Virus fa bata shafi sashin tsaron Iran ba,illa iyaka su ma suna bada tasu gudun muwar ne kawai wajen yakar cutar
Corona din.
Don haka ya kamata makiya su kwan da sanin cewar,ana kallon takunsu tarr.

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky