AMFANI DA SUNAN MIJI BAYAN AURE

AMFANI DA SUNAN MIJI BAYAN AURE

Sauya sunan Mahaifi zuwa na Miji, na daga cikin babban kuskuren da Mata ke yi bayan sun yi aure.

Shin kun san wannan dabi'a ta sauya sunan Mahaifi zuwa na Miji, haramun ne a addinance? Misali: Kafin auren mace za ka ga sunanta 'Aisha Lawal Isa' amma bayan ta auri 'Ibrahim Yusuf' sai ka ga ta koma 'Aisha Ibrahim Yusuf' ko kuma 'Aisha Ibrahim' kawai.

Wannan haramun ne, kuma Musulunci bai yarda mace ta dauki sunan mijinta ta yi amfani da shi ba, a takaice ma dai, wannan dabi'ar ta samo asali ne daga Kafirai, makiya Allah da ManzonSa.

A kan wannan, akwai gargadi mai tsanani daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam.

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce, "Duk wanda ya danganta sunansa da na wani da ba mahaifinsa ba, Allah zai yi fushi da shi, haka ma Mala'iku da ma dukkan mutane." (Ibn Maajah 2599).

Abu Dharr (Allah Ya yarda da shi) ya ce, ya ji Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce, "Duk mutumin da yana sane ya danganta sunansa da na wani, ba mahaifinsa ba, ya yi aiki irin na Kafirai. Duk wanda ya yi ikirarin shi daga wasu mutane yake wanda kuma ba haka ba ne, to ya nemar wa kansa wurin zama a wuta." (Bukhari [Hadisi na 3508] da Muslim [Hadisi na 61]).

An kuma rawaito daga Sa'ad Ibn Abi Waqqass da Abu Bakrah cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce, "Duk wanda ya yi ikirari bayan Musulunta cewa, shi dan wane ne, wanda ba mahaifinsa ba, kuma yana sane, Aljanna ta haramta a gare shi. (Bukhari [Hadisi na 4072] da Muslim [Hadisi na 63]).

Idan muka dubi wadannan Hadisai da kyau, za mu ga cewa, lallai akwai tsoratarwa mai karfi a kan wannan al'amari na sauya suna. Baya ga wannan tsoratarwa ma, a hankalce idan mace ta sauya sunan mahaifinta da na mijinta, idan mijin ya mutu fa? Ko kuma idan ya sake ta fa? Shin za ta cigaba da sauya sunanta ne duk lokacin da ta auri wani?

'Ya 'yan'uwana Musulmi, da a ce sauya sunan iyaye yana da muhalli a Musulunci da matan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ne ya fi cancantar su sauya, saboda suna auren mutumin da Babu kamarsa kaf a halittun Allah.
Amma tare da wannan, Nana Aisha (Uwar Muminai) tana amfani da sunan mahaifinta ne (Aysha bint Abubakr).
Ba ma Nana Aysha ba, hatta matan da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya aura, wadanda iyayensu Kafirai ne, makiya Annabi, hakan bai sa ya sauya musu sunan iyayensu da nasa ba. Ga dai Safiyya bint Huyayy (Huyayy Bamajushe ne kuma babban makiyin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam), amma hakan bai sa ta sauya sunanta ba.

Ya 'yan'uwana Mata, duk wadda ta san ta sauya sunan mahaifinta da na mijinta bisa jahilci, ko kuma don dadin soyayyar miji, ko don raina asalinta da neman daukaka da sunan dangin mijinta, ta sani ta saba wa Allah Madaukakin Sarki, kuma ya kamata ta yi gaggawar sauyawa zuwa na mahaifinta, kuma lallai ta nemi gafarar Allah.

Mu sani, dukkan ayyukan da muka yi a duniyar nan, abubuwan kididdigewa ne, kuma da su za a yi mana hisabi. Kar mu yarda mu yi biyayya ga abin halitta wajen sabawa Mahalicci (Allah).

Ina rokon Allah Ta’ala Ya ganar da mu gaskiya, Ya ba mu ikon bin ta, Ya kuma ganar da mu karya, Ya ba mu ikon kauce mata.

© Muhammad Lawal Barista
Alhamis, Sha'aban 9, 1441 A. H.
Thursday, April 2, 2020 C. E.

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky