Iman Mahdi Al' muntazar

🌐 *Imam Mahdi Al-Muntazar (a.s)* 🌐

Rikici tsakanin alheri da sharri a doron kasa dai ya faro ne tun daga farko-farkon wannan duniya kuma wannan gasa da rikici zai ci gaba tsakanin tafarkuna bbiyn; wato tafarkin shiriya da tafarkin bata; tafarkin Annabawa da tafarkin ma'abota girman kai.

Hakika sakon Musulunci ya samu nasara ta hannun Manzon Allah (s.a.w.a) kuma haka wannan tafarki ya ci gaba har ya gina tafarkin tauhidi, ya ciyar da dan’Adam gaba bisa tushen ilmi da imani, ya haskaka shi  da wannan haske kana kuma ya shiryar da shi da wannan shiriya madaukakiya.

To sai dai kuma daga baya wannan tafarki ya fara yin rauni, lokacin da wasu akidu da wayewa na jahiliyya suka fara kunno kai, aka fara samun koma baya a wayewa ta Musulunci, aka hana dan’Adam rayuwa karkashin inuwar imani, gaskiya, adalci da zaman lafiya. A bangare guda kuma zalunci ya ci gaba da yaduwa a fadin duniya, al’adun jahiliyya suka fara samun gindin zama, har muminai suka fara yanke kauna, idan da ba don suna tunanin alkawarin Ubangiji ba na cewa Zai taimaki addininSa da kuma tabbatar da adalci da kawo karshen zalunci da fasadi ta hannu wani Mai kawo gyara, wanda zai tsayar da sunnar Annabawa da kuma gina rayuwa bisa asasin Alqur’ani da Sunna Manzon Allah (s.a.w.a) ba. Wannan mutumi kuwa shi ne ‘Mahdi (Mai Shiryarwar) wannan al’umma’ kamar yadda Manzon Allah (s.a.w.a) ya ambace shi cikin ruwayoyi daban-daban.

Babu shakka hakan kuwa alkawarin Ubangiji ne tabbatacce cikin Alqur’ani da sauran Saukakkun litattafa cewa wannan Mai kawo gyara da dawo da kaunar da muminai suke da ita na kawo karshen jahiliyya, zai cika duniya da adalci da daidaituwa bayan ta cika da zalunci da babakere.

Wannan Mai kawo gyara shi ne dai wanda ake magana kansa cikin wadannan ayoyin na Alkur'ani mai girma:

*1- وَلَقَدْ كَتَبْنَا في الزَّبورِ مِنْ بَعْدِ الذِّكْرِ أنَّ الأَرْضَ يَرِثُهَا عِبَادِيَ الصَّالِحُون*

*“Kuma lalle, hakika, Mun rubuta a cikin Littafi baicin Ambato, cewa bayiNa salihai su ne za su gaji kasa”.*
(Suratul-Anbiya: 105)

*2-  هُو الَّذِي أَرْسَلَ رَسُولَهُ بِالهَدي وَدِينِ الحَقِّ لِيُظْهِرَهُ عَلَى الدِّينِ كُلِّهِ ولَوْ كَرِهَ المُشْرِكُون*

*“Shi ne Wanda Ya aiko manzonSa da shiriya da addinin gaskiya, domin ya bayyana shi a kan addini dukkansa, kuma ko da mushirikai sun Ki”.*
(Suratut-Tauba: 33)

*3-  و نُريدُ أَن نَمُنَّ عَلَى الَّذِين استُضْعِفُوا فِي الأَرْضِ وَنَجْعَلَهُمْ أَئِمَّةً وَنَجْعَلَهُم الوَارِثِين*

*“Kuma Muna nufin Mu yi falala ga wadanda aka raunanar a cikin kasar, kuma Mu sanya su shugabanni, kuma Mu sanya su magada”.*
(Suratul Qasas: 5)

Kamar yadda wasu ruwayoyi daga Ma'aiki (s) suka yi ishara da shi kamar haka:

1️⃣ Jaddadawa cewa shi Bakuraishe ne: “Ahmad da Mawardi sun ruwaito cewa Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: “Ku yi bushara da al-Mahdi, shi Bakuraishe ne, daga cikin zuriyata, zai bayyana a sabanin zaton mutane, zai cika duniya da adalci da daidaito kamar yadda ta cika da zalunci da babakere”.

2️⃣ Cewa Mahdi (a.s) zai kasance ne daga ‘ya’yan Abdul Mutallib: Ibn Majah ya ruwaito daga Anas bn Malik cewa: “Na ji Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: “Mu ‘ya’yan Abdul Mutallib mu ne shuwagabannin ‘yan aljanna, ni da Hamza da Aliyu da Ja’afar da Hasan da Husaini da Mahdi”.

3️⃣ “Duniya ba za ta qare ba har sai wani mutum daga cikin mutanen gidana, wanda sunansa irin sunana ne, ya mallake ta”.

4️⃣ Ahmad bn Hambal da Abu Na’im sun fitar daga Abu Sa’id al-Khudri cewa: Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: “Duniya ba za ta qare ba har sai wani mutum daga zuriyata ya mallake ta, ya kuma cika duniyar da adalci kamar yadda aka cika ta da zalunci….”.

🙏Ya Allah Ka gaggauta bayyanarsa, Ka sanya mu daga cikin mabiyansa na hakika. Amin Ya Allah.

*Muna taya muminai murnar wannan rana mai albarka*

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky