🌐 *Kauna Da Yanke Kauna* 🌐

Kafin bayyanar Musulunci, dan’Adam dai ya rayu cikin yanayi na jahiliyya mai tsanani cikin karnoni da dama, kafin daga baya hasken Musulunci da shiriyar da Manzon Allah (s.a.w.a) ya zo da ita ta bayyana ta kuma haskaka duniya.

A wancan lokacin dai dan’Adam yana rayuwa ne cikin yanayi na dar-dar da yanke kauna, sai dai kuma lokacin da ya ji kalmar ‘yanci daga bakin Mai Albishir, Manzon Allah (s.a.w.a) yana kiransa zuwa ga shiga jirgin ‘yan’Adamtaka, nan take ya bude zuciyarsa, ya kuma karbi wannan kira na kauna da fatan alheri.

Haka dai lamarin yake, a duk lokacin da aka samu duhun jahiliyya ya mamaye duniya, al’umma suka yanke kauna da fata, sai a samu wani sako na Ubangiji da zai zo ya yaye wannan duhu daga kan al’umma ya kuma dawo musu da kauna da kuma fatan da suke da shi.

*وَ إِنْ مِنْ أُمَّةٍ إلاّ خَلاَ فِيها نَذِيرٌ*

*“Kuma babu wata al’umma face wani mai gargadi ya shude a cikinta”.* (Surat Fatir: 24).

Haka dai hasken Alqur’ani ya ratsa duniya, ya kawar da duhun jahiliyya, ya mayar wa dan’Adam da ‘yanci da karamarsa da azzalumai suka hana shi.

Ta hakan ne kuma tausayawar Ubangiji ta samu dan’Adam da kuma shiryar da shi a duk zamunna.

A fili yake dai cewa samuwar Mahdi mai gyara yana nuni ne da kulawa ta Ubangiji mai wanzuwa kana kuma tausayawar Ubangiji wacce aka kira dan’Adam zuwa ga dakonta, kamar yadda aka bukace shi da ya zauna cikin shirin dakon Annabawa masu kawo gyara.

Hakika duk mutumin da yayi biris da wannan alkawari na Ubangiji na gadar da kasa da sahilan bayi, kuma bai yi imani da bayyanar Al-Mahdi mai kawo gyara ba, babu shakka zai samu kansa cikin yanayi na yanke kauna da rashin fata.

Kamar yadda kuma kira zuwa ga gaskiya da Alkur’ani mai girma ya yi wa dan’Adam kana kuma Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi bayani kanta, ita ce kira zuwa ga aiki, jihadi da kuma kawo gyara, a daidai lokacin da ‘yan’Adam suke jiran dakon Mai gyaran da aka yi musu alkawarin bayyanarsa, don su share fagen mallakar duniya ga salihan bayi da halifancin Wanda aka jima ana jiran bayyanarsa (a.s).

Tarihi ya tabbatar da cewa al’ummomin da suka zo gabannin aiko Annabawa masu kawo gyara, sun kasance cikin jiran dakon samuwar wani Annabi da zai kawo musu gyara cikin al’amurransu da rayuwa cikin yalwa da tsaro, don su taru a karkashin tutar wannan aikakken Annabi. To sai dai kuma bayan kawo karshen annabci da annabcin Manzon Allah (s.a.w.a), Allah Madaukakin Sarki Ya kaddara cewa wannan gyara da al’umma suke so zai kasance ne a hannun wani Imami daga zuriyar Manzon Allah (s.a.w.a), wanda zai gina wannan aiki nasa na kawo gyara karkashin Littafin Allah da sunnar ManzonSa (s.a.w.a).

Don haka kula da kuma ba da muhimmanci ga wannan lamari na Imam #al_Mahdi (a.s) wajibi ne, kamar yadda aiki da kuma kokari don share fagen bayyanarsa da kuma riko da tafarkinsa shi ma wajibi ne. Haka nan ma addu’a da kuma neman taimakon Ubangiji wajen gaggauta bayyanarsa (a.s) shi ma dai yana da nasa gudummawar da kuma muhimmanci.

Irin wannan kauna dai na daga cikin abubuwan da suke dada karfafa al’ummar musulmi a duk inda suke wajen cewa nan gaba za su sake rayuwa karkashin iko na addininsu kana kuma cikin adalci da daidaituwa ba tare da tsangwama da kawar musu da ‘yancinsu ba.

🎂Amincin Allah ya tabbata a gare ka Ya Aba Saleh al-Mahdi ranar da aka haifeka, ranar da ka shiga buya da kuma ranar da za ka bayyana alhali jama’a suna cikin dakon jiranka don ka tabbatar da adalci a bayan kasa bayan an cika ta da zalunci da babakere.

*(Dukkan Godiya Ta Tabbata Ga Allah Ubangijin Talikai)*

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky