TAURARUWAR AREWACIN NIGERIA-Nana As'ma'u

Tauraruwan Arewacin Nigeria A Qarni Na Sha Tara: Nana Asma'u  Bint Fodio.

By Anas Lawal

A tarihin ƙasar nan anyi jarumai Maza da yawan gaske amma Mata Kadan ne tarihi ya tuna dasu, a ƙarni na Sha Tara, an samu jajirtacciyar mace, Malama, yar uwa, gimbiya, uwa, kuma marubuciya daga gidan mujaddadi shiekh Usman Dan Fodio (1754-1817) wato Nana Asama'u bnt Fodiyo.

Haihuwar Ta

An haifi Nana Asama'u ne shekarata 1793/4, shekaru 11 Kafin kafa Daular Sakwkkwato, a garin Ɗegel ga shehu mujaddadi, an haifeta ne a matsayin tagwaye amma Dan uwanta ya rasu tun Suna qanana. Shehu ya sanya mata Suna Asama'u ne Domin tuna Sahabiyyar nan Mai daraja Nana Asama'u bnt Abubakar Saddiq. Nana Asama'u ba fullatana ce yar Qabialar Toronkawa. Gidan Su kuwa gidan Malamai, Abdullahin Gwandu Baffanta  ne Muhammad Bello kuma Yayanta ne Dan Fodio kuma Mahaifinta.

Karatun Ta

Malama Asama'u tayi karatun addini Mai zurfi  awurin mahaifinta Dan Fodio, da sauran malaman gidansu. Ta kware wajen haddace alqurani,  tafsir, larabci, da fiqhun malikiyya, sannan ta kware wajen magana da rubutun ajami da yaren Hausa,  fillanci,  larabci da buzanci. Ta kuma San Lissafi,  kimiya da Ilimin siyasa da tarihi, masaniya a fannuka daban daban wato (polymath).

Nana ahlus sunna ce mai bin Ɗarikar Qadiriyya Kamar Mahaifinta.

Hidimar ta Wurin Yaɗa Ilimi.

Nana ta sadaukar da lokacin rayuwanta wurin yaɗa Ilimi musamman ga matan karkara, Kamar mahaifinta, tayi imanin cewa Ilimin da ba a yaɗawa bayida wani amfani.

 Tayi Rubuce-Rubuce da harshen Hausa, buzanci,  larabci da fillanci a waƙe da zube domin yayai sauƙi ga mata mazauna karkara da na birni. Ta sadaukar da rayuwanta Domin ganin cewa ta koyar da iya adadin Matan da zata iya koyarwa. Mafi yawancin ƙasidun da ta rubuta a da harshen Hausa, Fillanci da Buzanci ta rubutasu ne Domin matan karkara Su iya rerawa lokacin da suke aikace aikacen gida, domin yaye duhun jahilci,  ɗebe kewa da kuma gyara zamantakewa.

Nana ta ƙirƙira wani ƙungiya da ake kira " 'Yan Taru" Wanda suke karade kauyuka wurin ganin sun koyar da mutane,  sun wayar musu da kai, koyar da Ilimin addini da rubutun ajami.  Yan uwanta Fatima da Maryama Suma sun taimaka wurin tafiyar da Qungiyar.  A yanzu haka akwai Gidauniyar yan Taru a wasu biranen America.

Wallafe Wallafen Ta.

Nana ta Yi Rubuce Rubuce da yawa da Hausa, Larabci, Fillanci da Buzanci, A zube da waqe, Jean Boyde ta fassara fiye da littafanta guda sittin zuwa turanci, wanda na taba karanta dayawa daga ciki a Dakin Karatu na, Sashen Karatun Tarihi na Jami'ar Jihar Kaduna.

Tayi rubce-rubucen ta ne a bangaren nasiha, tarihi, tafsiri, wa'azi, fiqhu, yabo, ta'aziyya da dai sauransu. Tayi kokarin hana Mata bori, tsafi da bokanci, inda ta nusar da su muhimmancin ayoyin Qur'ani wurin neman waraka.

Shawar-Warin Ta Ga Sarkunan Daular Sakwkkwato.

Da yike Allah Ya mata yawancin kwana Nana ta ga zamanin mulkin mahaifinta Usman Fodio, ta kuma ga na Yayanta Muhammad Bello, da Dan uwanta Abubakar Atiku da Ali Babba, kuma tana nan akayi mafi yawancin yaqunan Jihadi, wannan duk ya sa ta samu basisar siyasa da mulki, har ta zama Mai bada shawara ga Sarkunan Sakkwato na baya baya.

Aurenta.

Ta auri waziri Gidado Dan Laima, kuma Allah Ya azurta Su da 'ya'ya.

Rasuwar Ta.

Nana ta rasu a 1865 tana da shekaru 70/71 a duniya, shekaru talatin bayan Rasuwar Yayanta Sarkin Musulmi Muhammad  Bello kuma shekaru 48  bayan Rasuwar Mahaifinta Dan Fodio. Wanda duk tayi waƙen ta'aziyyar Su.

An Yi Wallafe wallafe da yawa akan tarihinta kamar su The Caliph Sister, One Woman Jihad, Educating Women; The Legacy of Nana Asama'u bnt Fodio by Jean Boyld wanda tace "nazo in yi bincike akan Asama'u, sai naga tana koyar dani ta rubuce-rubucenta. Dayawa Suna ganinta a matsa yin Mace ta farko da tayi gwagwarmaya akan hakkin mata a arewacin Nigeria da yammacin Africa musamman ta fuskan Ilimin 'ya mace.

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky