Posts

Showing posts from May, 2020

SHEKARU GOMA DA MUTUWAR'YAR ADUA

Shekaru 10 Da Mutuwar Yar Adua: SHAIKH ZAKZAKY NA NAN RAYE! — Saifullahi M. Kabir A ranar 5/5/2010 aka bayyana mutuwar tsohon shugaban kasa, Umaru Musa Yar Adua, bayan ya shafe watanni kusan shida yana jinyar ciwon zuciya. A watan Satumbar 2009 Umaru Musa Yar Adua ya ba da umurni aka yi wani shiri na yunkurin saka Bomb a gidan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). A ranar Alhamis, 10/9/2009 Shaikh Ibraheem Zakzaky bayan kammala Tafsirin Alkur'ani a FIC, Zariya, ya tona wannan shirin na gwamnatin Yar Adua na yunkurin sanya Bomb a gidansa ta hanyar jefowa daga kan jirgin sama. Inda ya yi kira ga Yar Adua da cewa idan yana burin ya kashe shi ne, to ya kasheshi shi kadai, ba bukatar ya sanya bomb a gidansa alhali akwai mahaifiyarsa yar shekaru fiye da 80. Shaikh Zakzaky ya cewa Yar Adua a lokacin: "Yanzu za ka burge Amurka da Isra'ila idan ka kashe Al-Zakzaky? Sun Dora ka a kan cewa yanzu za ka yi kisan kai, kila (ka yi kisan) don ka samu fuska a wajensu. To, Sunnah za ta maimaita kant