SHEKARU GOMA DA MUTUWAR'YAR ADUA

Shekaru 10 Da Mutuwar Yar Adua:
SHAIKH ZAKZAKY NA NAN RAYE!

— Saifullahi M. Kabir

A ranar 5/5/2010 aka bayyana mutuwar tsohon shugaban kasa, Umaru Musa Yar Adua, bayan ya shafe watanni kusan shida yana jinyar ciwon zuciya.

A watan Satumbar 2009 Umaru Musa Yar Adua ya ba da umurni aka yi wani shiri na yunkurin saka Bomb a gidan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).

A ranar Alhamis, 10/9/2009 Shaikh Ibraheem Zakzaky bayan kammala Tafsirin Alkur'ani a FIC, Zariya, ya tona wannan shirin na gwamnatin Yar Adua na yunkurin sanya Bomb a gidansa ta hanyar jefowa daga kan jirgin sama. Inda ya yi kira ga Yar Adua da cewa idan yana burin ya kashe shi ne, to ya kasheshi shi kadai, ba bukatar ya sanya bomb a gidansa alhali akwai mahaifiyarsa yar shekaru fiye da 80.

Shaikh Zakzaky ya cewa Yar Adua a lokacin: "Yanzu za ka burge Amurka da Isra'ila idan ka kashe Al-Zakzaky? Sun Dora ka a kan cewa yanzu za ka yi kisan kai, kila (ka yi kisan) don ka samu fuska a wajensu. To, Sunnah za ta maimaita kanta. Ni na yi burin a ce wanda zai kashe ni ya zama wani mutum wanda ba shi da rabin Lahira ne, amma ni ka bani mamaki saboda ina jin tausayinka kamar yadda nake jin tausayin yayanka Shehu Musa Yar Adua da aka kashe."

Shaikh ya ce: "To amma in haka ka so, shi kenan Falillahil Hamd! Amma dai rokona shi ne ka kashe ni ni kadai, ba bukatar ka yi 'Massacre'. Ba bukatar yin kisa-kiyashi. Ba bukatar kashe mahaifiya da yayana, suka maka mene? Da kuma makwafta ma, duk su kai muku mene?"

Wannan jawabin da Shaikh Zakzaky ya yi a lokacin bai sa sun janye daga nufinsu na yunkurin kashe Shaikh Zakzaky da yi wa almajiransa kisan kiyashi ba. Don haka a ranar Juma'ar karshen Ramadan din 1430, daidai da 18/9/2009 sai ga cincirindon motocin yan sanda nan, a karkashin Kwamishinansu na lokacin, Tambari Yabo, inda suka bude wuta a kan masu Muzaharar Quds a Zariya, suka raunata gomomi tare da kashe mutum biyu; Shahid Musa Muhammad Jaji da Shahid Abdurrahman Soje.

CP Tambari Muhammad Yabo, ya zo da motocin yan sanda manya da kanana fiye da 10, inda ya girke su a Kofar Doka Zariya, daidai lokacin da goshin Muzaharar nuna goyon bayan Palasdinu ya karaso wajen, suka rika bude wuta a kan yan uwa.

Bayan wannan harin, sun cigaba da kokarin neman dama don kashe Shaikh Zakzaky, amma bisa hikimar Allah suna fara tsanantawa sai Allah Ya kama Yar Adua, aka fita da shi daga Kasar don jinya. Duk da ana cewa ya jima da mutuwa, amma suka kasa fadan ya mutu din, sai dai kawai ace yana murmurewa. Har zuwa rana mai kamar yau 5 Mayu, suka ambata mutuwar Ummaru, inda aka dawo da shi Kasar nan ranar 6/5/2010 a Akwatun Gawa.

Da yake yunkurin Kashe Shaikh Zakzaky kwangila ne daga Amurka da Isra'ila, bayan mutuwar Yar Adua sai Ebele Jonathan da Namadi Sambo suka dora! Har zuwa sadda suka kashe yayan Shaikh din uku da almajiransa 30 a ranar Quds 2014. Bayan shekara guda da wannan kuma Buhari ya zo ya dora, inda ya kashe yayan Shaikh din guda 3 da almajiransa fiye da 1,000, sannan suka yi kokarin kashe shi, Allah bai nufa ba. Yau shekaru 5 suna tsare da shi da matarsa cikin raunin harsasai.

Daga abubuwan da za a iya tuna Yar Adua da su, akwai cewa shine ya karbi kwangilar fara yin Ta'addanci da sunan Boko Haram. Kuma shi ya fara aiwatarwa.

Muna rokon Allah Ya nuna mana karshen azzalumin yanzu, wato Dan Daura, Ya raya Shaikh Zakzaky da kariyarsa.

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky