DDALILIN DA YASA MUKA CE AKORI SHARI'AR DA AKE MA MALAM ZAKZAKY(H)
Abin da ya sa muka nemi a
kori shari’ar da ake wa
Malam [H] – Barista Ishak
Adam
Barista Ishaka Adam na cikin Lauyoyin da
ke tsaya wa Shaikh Ibraheem Zakzaky a
karar da gwamnatin Jihar Kaduna ta shigar
da shi shekaru biyu da suka gabata. A
cikin wannan hirar da suka yi da Aliyu
Saleh, fitaccen Lauyan ya bayyana
dalilansu na shigar da bukatar kotu ta yi
watsi da shari’ar da ake yi wa Shaikh
Zakzaky da maidakinsa Malama Zeenah.
Sannan ya bayyana abin da suke fatan
samu a hukuncin da kotun za ta yanke
ranar Talata 29 ga Satumba mai zuwa.
ALMIZAN: Masu karatu za su so sanin
abin da ya sa Lauyoyin Shaikh Zakzaky
suka shigar da kara suna neman kotu ta yi
watsi da shari’ar da ake yi masa wacce
aka kwashe sama da shekaru biyu ana yi?
BARISTA ISHAKA ADAM: Sakamakon
gwamnatin Jihar Kaduna ta shigar da su
Malam Zakzaky kara tana tuhumar su da
aikata wasu laifuffuka guda takwas tun a
watan Yuni na 2018, wanda aka fara shiga
kotu a ranar 5 ga wata, har ya zuwa yanzu
fiye da shekaru biyu ke nan su Lauyoyin
gwamnatin, ko kuma gwamnatin Jihar
Kaduna ba ta iya kawo shaida ko guda
daya ba. Don haka muna iya cewa har
yanzu ba a fara ‘case’ din ba.
A bangare guda kuma sai muka ga an yi
wa ’yan’uwan da aka kama a waki’ar
Zariya, wadanda aka kama a Disamba,
2015 an yi masu irin wadannan tuhume-
tuhumen, kotu ta wanke su, ta ce ba su
aikata wadannan laifuffukan ba, kuma ta
ma sake su. An saki ’yan’uwa kusan 170,
court 6, 8, 11 (wacce yanzu ta zama court
9), duk sun saki ’yan’uwa, sun wanke su,
sun ce ba su aikata wadannan laifuffukan
ba.
Sannan kuma ga shi kuma sun kasa kawo
shaida. Har yanzu ba su kawo hujja ko
guda daya ba, duk da kuwa suna da su a
rubuce. Sai muka fahimci suna amfani da
abin da ake kira ‘delay tactics’ ne, suna jan
lokaci saboda su kansu sun san ba su da
‘case.’ Don an taba yin wata takwas ba a
ce komai a kan kes din ba, lokacin da aka
tura Alkalin ya tafi kotun sauraron
kararrakin zabe. Ya yi kusan wata shida,
ya dawo ya tafi hutun wata daya, da aka
tashi sanya kes din aka sanya wajen wata
daya.
Wani abin da nake so ka lura da shi ne, su
’yan’uwan da aka wanke ana tuhumar su
ne da cewa sun aikata laifi, su kuma su
Malam ana tuhumar su ne da laifin
ingizawa a aikata laifin. Lokacin da kotu ta
wanke wanda ake zargi da aikata laifi, ina
kuma ga wanda ake tuhuma da ingizawa?
Ka ga shi ma ke nan bai aikata ba. Ka ga
ana rike da shi ne ba tare da ya aikata
wani laifin ba. Wannan kuma ya sabawa
wasu sassa uku na dokokin kasa na tsare
mutum ba tare da ya aikata laifin komai
ba.
Sannan kuma daga cikin dalilin da ya sa
muka bukaci kotu ta yi watsi da wadannan
tuhume-tuhumen akwai cewa ba a dauki
jawabin wanda ake kara ba wanda ake kira
‘taking plea’. Idan ana tuhumar mutum da
laifi ana karanta masa tuhume-tuhumen,
sai a ji ra’ayinsa, zai amince, ko kuwa zai
nuna rashin amincewarsa (guilty or not
guilty). Don haka tunda ba a yi ba, a
shari’a mutum bai san laifin da ya sa ake
tsare da shi ba. Ke nan ana rike da shi ne
ba tare da an sanar da shi dalilin da ya sa
ake tsare da shi ba.
ALMIZAN: Amma Barista a baya an yi wani
abu mai kama da haka, kuma har su
Malam sun nuna ba su aikata laifin da ake
zargin sun aikata ba.
BARISTA ISHAKA ADAM: An yi ‘taking plea’
ne a lokacin da wadanda ake tuhuma da
aikata laifin mutum hudu ne, wato su
Malam da Malama da Malam Yakubu
Yahya da Dakta Sunusi Abdulkadir,
sakamakon an yi gyara a takardar
tuhumar aka cire sunan mutum biyu,
Malam Yakubu Yahya da Dakta Sunusi
Abdulkadir, sai ya zama ana tuhumar su
Malam ne da Malama. Wannan gyaran da
aka yi ya sa wancan ‘taking plea’ din da
aka yi ya riga ya rushe. Yanzu a doka ba a
yi ‘taking plea’ ba. Don haka shi ma
wannan a shari’a wata madogara ce da za
ta iya sa a nemi kotu ta yi watsi da kes
din.
Sannan kuma laifin da gwamnatin Jihar
Kaduna take tuhumar su Malam da
aikatawa, laifuffuka ne wadanda ‘Penal
Code’, wato kundin dokokin shari’ar
laifuffuka na Jihar Kaduna bai san da su
ba, domin an kafa su ne a shekarar 2017,
su kuma su Malam ana tsare da su ne tun
2015. Don haka ka ga ke nan laifuffukan
da ake tuhumar su Malam da aikatawa,
kotun shari’ar laifuffuka na Jihar Kaduna
bai san da su ba. Tsarin mulkin kasar nan
ya ce bai kamata a tuhumi mutum da laifin
da shari’a ba ta san shi ba.
Bisa wadannan hujjojin ne na cewa kotu ta
wanke ’yan’uwa da ake tuhumar su da
tuhume-tuhume iri daya da su Malam,
sannan kuma ga shi sai jan kafa suke, sun
kasa tsayawa a yi kes din saboda sun san
ba su da kes da kuma rashin daukar
jawabin wadanda ake tuhuma (taking
plea), bisa wadannan dalilan ne ya sa
muka nemi kotu ta yi watsa da waccan
karar.
Bisa wadannan hujjojin da na ambata da
wasunsu ma, shi ya sa aka shigar da
wannan korafi aka ce ana son kotu ta yi
watsi da wadannan tuhume-tuhumen da
ake yi masu ta sake su. An shigar da
wannan karar, an rubuta komai an bai wa
Lauyoyin gwamnati, su ma sun rubuta
tasu takardar rashin amincewa da wannan
bukatar da aka shigar, mu ma mun ba su
amsa na rashin amincewar tasu. An bai
wa kotu. Kowa yana da shi a tsakanin mu.
Don haka kotu ta sanya Juma’ar da ta
wuce a matsayin ranar sauraron dukkan
bangarorin, aka yi abin da ake kira
‘adoption,’ wato kowa ya tsaya gaban kotu
ya bayyana cewa ya shigar da kara, kuma
ya amshi takardar daga abokin shari’ar
tasa, kotu ta tabbatar kowa yana da
wannan takardar, kowa yana da takardun
kowa. Yanzu abin da ya rage kotu za ta
natsu ta duba duk takardun bangarorin
biyu, sai ta yanke hukunci, amma yanke
hukunci, bisa wannan bukatar tamu.
Ba za mu ce ga hukuncin da kotu za ta
yanke ba, amma dai a shari’ance za mu
iya cewa kotu tana da zabi guda biyu; na
farko ko dai ta ce ta gamsu da bukatarmu,
su Malam ba su aikata laifi ba. Don haka
ta yi watsi da duk tuhume-tuhumen da ake
yi masu, ta saki su Malam, ba su aikata
wani laifi ba, don haka ta sallame su. Ko
kuma ta ce a bar Lauyoyin gwamnati su
kawo shaidu a ci gaba da kes din, amma
kila sai ta zo da wasu sharruda, kamar ta
ce ta ba da wasu sharruda ta ce nan da
wani lokaci, ko wata uku suna so nan da
lokaci kaza tana so a gama wannan kes
din. Kes din shekara biyu da wata biyu ke
nan ana yin sa, amma har yanzu ba a ma
fara ba, saboda a doka in har kes ba a fara
kawo shaidu ba, ana iya cewa ba a ma
fara shi ba.
ALMIZAN: Amma Barista wasu za su iya
tambayar cewa a doka za a iya la’akari da
hukuncin da aka yanke wa wani a yi
hasashen hukuncin da za a yi wa wani
alhali ba a fara sauraron shari’arsa ba?
BARISTA ISHAKA ADAM: In da a ce
laifuffukan da ake zargin su Malam da
kuma ’yan’uwan da aka saki sun
bambanta, shi ne ba za a iya la’akari ko
dogaro da cewa an kori kes din ’yan’uwa
ba, amma tunda tuhume-tuhumen iri daya
ne, musamman ita babbar tuhumar
(capital offense) ta cewa an kashe wani da
ake kira Yakubu Dan Kaduna, kuma kotu ta
wanke wadanda ake zargi, don haka zai
zama bata lokaci ne, zai zama su Malam
ba su aikata wannan laifin ba. Kuma
wannan a shari’a ana yin sa, ya faru a kes
daban-daban, wadanda manyan kotuna
suka yi irin wannan hukuncin. Kuma a
tsarin doka ana amfani da hukuncin baya
wajen yanke wani hukunci a gaba. Lauyoyi
suna da hurumin su ce; “Wannan shari’ar
da ake yi mana irin ta ta faru a tsakanin
wane da wane a kotu kaza da kotu kaza,
kuma sun yanke hukunci iri kaza. Akwai
irin wannan hukuncin da wasu kotuna da
suke sa’o’in juna da wannan da kuma
wadanda suka girme ta da suka yi irin
wannan hukuncin.” Irin wannan ya ta faru
inda wata kotu wacce take daidai da
wannan kotun da take shari’ar su Malam
ta yanke hukunci irin wannan, kuma wacce
take sama da ita ma ta yanke irin wannan
hukuncin. Wannan yana daga cikin hujjojin
da muka gabatar a gaban kotu.
ALMIZAN: Jama’a za su so su san
matsayin kotun da ke shari’ar su Malam
da ta kuma wacce ta wanke ’yan’uwa
170?
BARISTA ISHAKA ADAM: Sa’o’in juna ne.
Dukkan su State High Court ne. Zai zama
hukuncinsu kamar wannan kotun ce, High
Court 3 ce ke shari’ar su Malam, su kuma
wadancan High Court 6,8, da 9, sune suka
wanke ’yan’uwa, suka ce ba su aikata
laifin komai ba. Dukkan su High Court ne
na Jihar Kaduna, kuma ko da High Court
ce a Kwara, Lagos, Jigawa ko Kano,
matukar a cikin kasar nan ne, duka abu
daya ne. In da a ce kamar Magistrate ce ta
yi hukunci, wacce tana kasa da High Court,
za su iya cewa wannan ai karamar kotu ce
(Lower Court) ce, ba ta da iko a kanmu,
amma kotunan sa’o’in juna ne, kafinsu
daya da kuma wacce take yayarsu ko
kuma uwa a gare su, wato Court of Appeal,
mun hada da hukuncin da ta yanke irin
wannan wanda ta sallami wanda ake
tuhuma din mun ba su.
ALMIZAN: Me kuke fata daga wannan
kudurin da kuka shigar?
BARISTA ISHAKA ADAM: Muna fatan za mu
yi nasara, domin mun fi su hujjoji. Muna da
hujjoji kashi 95, su kuma suna hujja kashi
biyar. Mun yi masu tambayoyi guda
takwas, daya suka iya amsawa, ita din ma
ba su amsa ta cikakkiya ba.
ALMIZAN: Wane hali Shaikh Zakzaky yake
ciki yanzu ganin cewa an kwashe fiye da
shekara biyu ana abu daya, ba gaba ba
baya, kuma ga shi suna fama da rashin
lafiya?
BARISTA ISHAKA ADAM: Su Sayyid dai
kowa ya san ba su ba da lafiya, kuma
Likitoci sun tabbatar da haka. Kowa ya
san abin da ke damun su da abin da aka yi
masu. Ko da ma a ce ba harsasai a jikinsu,
kashe masu ’ya’ya, ’yan’uwansu na jini da
kuma almajiransu fiye da 1,000 a
gabansu, sun isa sanya masu rashin lafiya,
balle su ma aka harbe su a hannu, kafa,
kafada da kansu, yanzu a kansu akwai
baraguzan harsashi sama da 40, wanda
hakan ya haifar masa da cutar shanyewar
barin jiki na wani lokaci a baya, dama
kuma idonsu daya ya mutu. Don haka
suna cikin wani yanayi na rashin lafiya.
Wannan ya sa muke da karfin gwiwa na
cewa kotu ta za ta kalli bukatarmu ta kori
wannan kes din don su samu su je samu
lafiya.
Kotu za ta iya la’akari da rashin lafiyar da
su Malam ke ciki domin su sallame su don
su je su nemi lafiya, kotun ta san halin da
suke ciki, ta gan su, sun bayyana a
gabanta, an yi maganganu sosai, kotu ta
ga yanayinsu. Akwai lokacin da aka zo da
su Malam kotu, lokacin tafiya Indinya din
nan, har ma jama’in tsaro da ma’aikatan
kotu kuka suke yi saboda sun ga yanayin
da su Malam ke ciki. Ni na ga wani dan
sanda da ma’aikatan kotu suna kwalla.
ALMIZAN: A karshe wane sako kake da shi
ga ’yan’uwa?
BARISTA ISHAKA ADAM: Sakona shi ne
’yan’uwa a ci gaba da addu’a dare da rana
ba kaukkautawa, kuma a ci gaba da yin
abubuwan da ake yi, kamar Abuja Struggle
din nan, kuma duk idan ’yan’uwa suke ya
zama suna masu bin tsari da nizami.
ALMIZAN: Mun gode kwarai.
BARISTA ISHAKA ADAM: Ni ma na gode
kwarai.
Voiceofsheikh@gmail.com
Comments
Post a Comment