LABARIN WANI KARE MAI KISHIN ANNABI MUHAMMAD (S)

 LABARIN WANI KARE MAI KISHIN ANNABI (S.A.W)


KARE MA YANA KISHIN FIYAYYEN HALITTU ANNABIN RAHAMA (S.A.W)


Babban Malamin nan, Shakundum a fagen ilimin Hadisi, Alhafiz Ibn Hajar Al-asqalani, wanda ya rasu a shekarata (852) bayan Hijra.


Babban Malamin ya rawaito a cikin littafinsa mai suna


الدرر الكامنة في أعيان المائة الثامنة


Littafi ne na (Tarajum) wato littafi ne da ya kunshi tarihin Manyan Malamai, da Manyan Sarakuna, da Shugabanni, da mawaqa masana harshen larabci, wadanda suka rayu tun daga shekara ta dari bakwai da daya (701) har zuwa karshen shekara ta dari takwas daidai (800) bayan hijra, duk Malamin da ya ambaci tarihinsa, sai kuma ya ambaci wani abu da aka rawaito daga gareshi na ruwayoyin Hadisi ko wani labari. Kamar dai yadda Ibn Hajar din yayi bayani da kansa a gabatarwar littafin.


Alhafiz Ibn Hajar da yazo tarihin wani Malami mai suna: "Aliyyu Bin Marzuq" sai ya ambaci labarin wani kare mai ban mamaki da ya faru a wajajen shekara ta dari bakwai bayan hijra, yau kusan shekaru dari bakwai da doriya da suka wuce kenan. wanda shi wannan Malami ya rawaito daga wani mai suna: Jamaluddin Ibrahim bin Muhammad, ga yadda labarin yake.


أن بعض أمراء المغل تنصر فحضر عنده جماعة من كبار النصارى والمغل فجعل واحد منهم ينتقص النبي صلى الله عليه وسلم وهناك كلب صيد مربوط، فلما أكثر من ذلك وثب عليه الكلب فخمشه فخلصوه منه وقال بعض من حضر: هذا كلامك في محمد، فقال كلا بل هذا الكلب عزيز النفس وآل أشير بيدي فظن أني أريد أن أضربه. ثم عاد إلى ما كان فيه فأطال فوثب الكلب مرة أخرى فقبض على زدمته فقلعها فمات من حينه. فأسلم بسبب ذلك نحو أربعين ألفا من المغل.


Ma'ana: Wani daga cikin sarakunan Mogul (Mugayen arna makiya musulunci da suka zubar da jinin musulmai ba adadi) ya karbi addinin nasara, wato ya zama kirista, sai wasu jama'a daga manyan Malaman kiristoci suka halarcin bikin zamansa kirista, anan wani daga cikin Malaman kiristocin ya fara jawabi yana zagi da sukar Annabi Muhammad (S.A.W) a jawabin nasa! A gefe guda kuma akwai wani karen farauta da yake daure, da kiristan nan ya cigaba da zagin Annabi (S.A.W) sai karen nan ya tsinke yayi tsalle ya dira a kansa ya turmushe shi, ya yakushe shi!!! da kyar aka kwace shi daga hannun karen. 


Sai wani daga cikin wadanda suka halarci taron yace: Ina ga fa wannan Karen yayi maka haka ne saboda sukar Annabi Muhammad (S.A.W) da kayi.


Sai kiristan nan yace: A'a, sam!!! Sai dai wannan karen mafadaci ne, yaga ina daga hannayena, sai yayi zaton zuwa zanyi na bugeshi, shine abinda yasa ya tsinke yayi tsalle ya hau kai na.


Kiristan nan bai daddara ba!!! Sai ya koma ya cigaba da jawabinsa yana suka da cin zarafi da batanci ga Annabi Muhammad (S.A.W), sai karen nan ya sake ballewa a karo na biyu, yayi tsalle ya kama makogoron wannan kirista mai zagin Annabi (S.A.W) ya farke shi, a nan take ya mutu ko shurawa bai yi ba!!!.


Ta sababin haka, saboda wannan mu'ujiza da Allah Ya nuna, kimanin mutum dubu arba'in ne suka musulunta.


 A duba littafin (Addurar al-Kaminah) juz'i na (4), shafi na (153) bugun Da'iratul Ma'arif.


Allahu Akbar!!! Annabi (S.A.W) ba abun wasa bane!!! Ahir din masu kokarin sukarsa ko zaginsa saboda wasu munanan Shehunnan su da suka dora su a bisa bata, suka wulla su a tafarkin Jahannama!!!


Ahir din duk Shugaban da ya kasa bai wa Annabi (S.A.W) kariya, ahir din al'ummar da zata bari tayi shiru ana cin zarafi da zagin Annabi (S.A.W).


Mun ji dai!!! kare ma yana kishin Annabi (S.A.W) kare ma ba zai iya hakuri a taba masa Annabi (S.A.W) ba.


Bamu ce wani ya dau doka a hannu ba, amma jan hankali ga hukuma, jan hankali ga Gwamnatoci, ku sani rashin gani a kasa, wato rashin hukunta masu zagi da sukar Annabi (S.A.W) shi zai sa al'umma daidaiku daukar mataki a hannunsu, domin fa ku sani babu mai imanin da zai tsaya ana zagar masa Annabi ana shiru, ba a daukar matakin da ya kamata ya iya hakuri ya danne. Dole idan baku dauki mataki ba, to Jama'a zasu dau mataki a hannun su, idan kuwa haka ya cigaba da faruwa, to zaman lafiya zai yi wahala tsakanin al'umma, rikicin da zai iya ballewa ba karami bane, masifar da haka din zai haifar ba yar kadan bace.


Ya Allah Ka yafe mana, Kada Ka kama mu da abinda wawaye batattun cikin mu suke aikatawa. Allah Ka lullube mu da RahamarKa da LudufinKa.


Allah Ka isar mana a kan duk masu hannu cikin wannan mummunan aiki. 


Mai rubutu:

Musa Muhammad Idris Dankwano

11-07-1441, 07-03-2020.

voiceofsheikh@gmail.com

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky