MUHIMMAN RANEKU 400 A TARIHIN HARKAR MUSULINCI A NIGERIA

 Daga littafin:

MUHIMMAN RANEKU 400 A TARIHIN HARKAR MUSULUNCI A NIJERIYA


–Saifullahi M Kabir


Na: Cibiyar Wallafa Da Yada Ayyukan Shaikh Zakzaky (H)


RANAR:15 May, 1984 (14 Shaaban, 1404H):


A Ranar Talata, 15 ga watan Mayun 1984 ne wa'adin zaman Shaikh Zakzaky a kurkukun Inugu na kamun gwamnatin Shehu Shagari ya cika. Bayan Malam din ya shafe shekaru uku cur da wata daya a tsare. 


An kama Shaikh Zakzaky ne a garin Sokoto a ranar 15 ga watan Mayun 1991, inda wata kutu ta yanke masa daurin shekaru hudu (kamar yadda bayanin kamun ya gabata). 


Lokacin da Shaikh Zakzaky ya fito daga wannan kurkukun, isowarsa Zariya ke da wuya ya riske masu tariyarsa wadanda a lokacin 'yan uwa ne kasa da mutum 30. Kuma ya yi musu jawabin karfafawa, akan cewa kar su ga cewa bamu da yawa a yanzu, nasara ba shine yawan mutane ko kafa daula ba. 


Malam ya yi bayani cewa, nasara a wajen Allah (T) shine mutum ya koma gareShi yana mai biyayya a gare shi, in ya samu uzuri a wajen Allah ya samu nasara kenan. Har a lokacin Malam ya kawo misalai da wasu Annabawa da Allah ya aiko ba su kai ga kafa daula ba aka kashe su, wasunsu ma ko mabiya basu samu da suka amsa daawarsu ba.


*


RANAR: 6 July, 1984 (8 Shawwal, 1404H):


A wannan ranar Juma'a din ne aka yi Muzaharar Quds ta farko a Nijeriya don amsa kiran Imam Khumaini (QS) akan muhimmancin fitowa don nuna goyon bayan raunanan alummar Palasdinu da Yahudawan Sahayoniya ke wa kisan kare dangi bayan sun mamaye yankinsu.


An fara taron Qudus na farko ne da shirya lakcoci tun a ranar Alhamis, ranar Juma'a aka gabatar da Muzaharar wacce aka faro ta daga cikin Zariya City aka rufe ta a Sabon-garin Zariya. Sannan kuma ranar Asabar aka gabatar da gangami (rally) a Jamiar Ahmadu Bello (ABU).


Yan gomomin yan uwa ne suka halarci Muzaharar a wannan shekarar, ba su kai mutum ko 100 ba.


*


RANAR: 8 July, 1984 (10 Shawwal, 1404H):


Ranar Lahadi 8/7/1984 daidai da 10 ga Shawwal, 1404H ne aka daura auren Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky da matarsa Malama Zeenah Ibrahim a garin Zariya.

 

An daura auren ne bayan fitowar Shaikh Zakzaky daga kurkukun Inugu da watanni biyu, kuma bayansa da watanni kamar biyar aka kuma kama Shaikh Zakzaky inda aka tsare shi a kurkukun Kiri-kiri da ke Lagos.


*


RANAR: August, 1984 (Zulhijja, 1404H):


A wannan watan Shaikh Zakzaky ya tafi Hajji tare da matarsa Malama Zeenah Ibrahim, wata daya da 'yan kwanaki bayan aurensu da aka daura a watan July 1984.


*


RANAR: December 1984 (Rabiul Auwal, 1405H):


A farko-farkon watan December 1984, wacce ta dace da Rabiul Auwal 1405 Hijiri ne kuma Shugaban kasa na Soja, Muhammadu Buhari bayan ya hambare Shagari, ya kuma kama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).


A ranar da za a yi kamun 'yan sanda sun zo gidan Malam da yamma suka yi sallama da shi, bayan ya fita suka nemi za su tafi da shi. Malam a lokacin bai fi wata hudu da aure ba, don haka ya nemi su bar shi ya koma gida ya sanar da iyalinsa hakan, amma suka ki. Aka dauki lokaci suna jayayya har Malama Zeenah ta jiyo su, ta fito. Nan ta fahimci halin da ake ciki.


A rannan sun tafi da Shaikh Zakzaky, a yayin da Malama Zeenah ta bi su, suka kai su ofishin hukumar tsaron Nigerian Security Organization (NSO) a Kaduna, bayan sun kwana, washe gari suka sa Malama Zeenah ta koma gida, shi kuma Malam suka tafi da shi Lagos.

 

Bayan an je Lagos, an tsare Malam a Interrogation Center da ke Lagos din na tsawon wata uku, tun daga Disambar nan har zuwa watan Maris 1985, sannan suka mai da Shaikh Zakzaky kurkukun Kiri-kiri inda ya shafe watanni biyar a nan, a farkon watan Satumbar 1985 bayan an hambare Buhari daga mulki sannan Malam ya fito.


***


RANAR: 1985 (Haihuwar Sayyida Muhammad) ? 


A wannan ranar ce Malama Zeenah Ibrahim ta haifawa Shaikh Ibraheem Zakzaky yaronsa na farko wanda aka sakawa suna Muhammad. 

 

An haifi Muhammad ne a daidai lokacin da mahaifinsa, Shaikh Zakzaky ke tsare a kurkukun Kiri-kiri a mulkin shugaban kasa Buhari. Don haka ma sai bayan kwanaki 28 da haihuwar sannan Malam Zakzaky ya samu labarin. Sai dai dama ya riga ya yi wasiyya da in an haifi namiji a sanya masa Muhammad, idan kuwa macece a sanya mata Nusaibah.


*


RANAR: 1 September 1985 (16 Zulhijja, 1405H)


A wannan rana ne Shaikh Ibraheem Zakzaky ya iso gida, bayan ya fito daga kurkukun Kiri-kiri wanda Janaral Buhari ya daure shi.


Sakin Malam ya biyo bayan hambare gwamnatin Buhari da Ibrahim Badamasi Babangida ya yi a ranar Talata 27 ga Augustan 1985, bayan kwanaki 4 da wannan juyin mulkin aka saki duk wadanda Buhari ya tsare.


*


RANAR: February, 1986 (Jimadal Thani, 1406H):


A wannan shekarar Shaikh Ibraheem Zakzaky ya kara zuwa Jamhuriyar Musulunci ta Iran, inda ya halarci bikin cikar juyin Musulunci shekaru bakwai (7). A wannan karonma, Malam ya samu ziyartar Imam Khomain a gidansa a Jamaran, Tehran.


Daga Iran, Shaikh ya wuce London, inda ya yi jawabi a kan ‘Iran a jiya da yau, ya ba da labarin irin canje-canjen da aka samu daga shekarar farko na bayan juyi da ya samu zuwa zuwa yanzu bayan shekaru kamar bakwai da juyin. Bayan dawowarsa gida Nijeriya ma ya gabatar da lakca a kan wannan mauduin. 


***


RANAR: August, 1986 (Zulhijja, 1406H):


A wannan shekarar ma, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya kuma zuwa Hajji. Ya je London don halartar wani taron 'yan uwa Musulmi da suka gayyace shi, daga can ya wuce Saudiyyah don aikin Hajjin.


— Littafin MUHIMMAN RANEKU..., Littafi ne da zai tattaro takaitaccen bayani a kan duk wata rana da wani abu ya auku a cikinta, wanda ya shafi Harka Islamiyya da Jagoran Harkar a tsawon shekaru fiye da 40 da fara da'awa. Kowane Maudu'i a cikinsa abin a fadada shi zuwa ga littafi mai zaman kansa ne, muna fatan ya zama an rage hanya da samar da shi ga manazarta da marubuta a nan gaba.

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky