YUNƘURIN ZUBAR DA JINI. yakamata ɗan'uwa yayi kyakykyawan shiri.

 Me Zasuyi Nan Gaba? Allahu A'alamu:-


 SABODA HAKA MUTUM YAYI KYAKKYAWAN SHIRI DAGA NAN ZUWA ARBA'EENA—Shaikh Yakubu Yahaya Katsina.

"Sai su ce ai dan an tare hanya ne, shin hukuncin tare hanya shi ne ayi ma mutum abinda akayi wa Su Malam? Ko kuma suce ai dan ana zagin sahabbai ne to dama ita gwamnatin ta kare sahabbai ce? Kuma a kawo mana jawabi 1 ko inda jagoranmu Malam Ibraheem Zakzaky (H) ya zagi wani sahabi...

Saboda haka su 'yan'uwa kada suyi tunanin ba zasu kara ba, a'a shirye suke su kara, Allah kadai kuma Ya san miye tanadinsu, tunda sunje wata jaha sunyi taro kwanannan taron sirri irin wanda sukayi wancan lokacin wanda suna gama taron suka afka ma Malam a Zariya. To sun kara yin irin wannan taron kwanannan.

To kaga mi zasuyi nan gaba Allahu A'alamu, kaga ashe ba bari sukayi ba, ba kuma shirye suke su bari ba. Illa dai kamar yadda nace ta namu bangare din mu dauki 'Ayyi Ihtimal' (Any Possibility) in Allah Ya rayar da mu falillahil hamdu, yadda Allah ya so yayi damu... Mu kayansa ne, mu bayinsa ne mu kayansa ne kuma dama kowwa akwai kaddarar da aka rubuta masa...

Almuhimmu shi ne kaddarar ta sameka kuma kana nan bisa abinda kake baka canza ba wannan shi ne nasararka. Muna fatan 'Yan'uwa zamu dawo cikin hayyacinmu kuma wannan lokacine na tawali'u zuwa ga Allah Ta'ala domin mutanan nan bamu san mi suke shiryawa ba saboda haka ya kyautata alaqarsa da Allah, ya kyautata alakarsa da bayin Allah, yayi kyakkyawan fata kuma yayi kyakkyawan shiri Ya zuwa lokacin da zamu ga bayan Arba'eena domin daga yau zuwa Arba'eena komai na iya faruwa.

To kaga ya kamata mutum yayi shiri tsakaninsa da Allah Ta'ala yaga cewa ya inganta Sallah, hakkokin mutane, ko bashi, ko mutuncin mutane da yake tabawa ko amanoninsu. Kuma ya inganta gaskiyarsa da inganta tsakaninsa da Allah ta wajan zikirori, karatun Al'qur'aninsa da ya kauracewa ko yake yi dan kadan daa, ya dawo yanzu ya kara yawansa, tashinsa na Sallar dare ya karu. 

Duk irin wadanann abubuwan dai mutum ya muhimmantar dasu domin ya zama in wannan lokacin ya zama shi ne Mahada (Shahada) din to ya tafi da karin guzuri in kuma ba shi ne ba to shikenan yayi shimfida sai ya dora yayi tayi ya ci gaba Insha Allah. Muna fata Allah ya datar damu.

WASSALAMU ALAIKUM WA RAHAMATULLAHI WA BARAKATUHU"

voiceofsheikh@gmail.com

- A jawabinsa na (shimfida)  ranar farko da fara zaman makokin ashura a Katsina. Juma'a 2/12/1442=21/8/2020.

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky