AL-BISHIRINKU

 ALBISHIRINKU! 


Cibiyar Wallafa Ayyukan Jagora, Shaikh Zakzaky Na Gabatar Muku Da Sabon Littafi Mai Suna:


“DA’AWAR HARKAR MUSULUNCI”

(Karkashin Jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky)


Littafin wanda ke da shafuka 400, shine mafi girman littafi da aka wallafa da ke dauke da bayanan Tarihin Harkar Musulunci zuwa yanzu. Ya kunshi muhimmai kuma gamsassun bayanai dangane da Asalin Da’awar Harkar Musulunci da Musabbabi ko dalilinta, Hadafi da Manufarta, Tarihi da Nizaminta, Ayyuka da Harkokinta, Cibiyoyi da Mu’assasosinta, Fitintinu da Waqi’o’inta.


Littafin Da’awar Harkar Musulunci na dauke da babuka 17, fasulla 120 da kuma kalmomi dubu 85,000, ya kunshi hotunan Tarihi a wasu babukan da suke bukatar mai karatu ya ga hoton abin da ake magana a kai.


 Bayan gabatar da bayanai kan lalurar da ta sa aka rubuta littafin a daidai wannan lokacin wanda ya hada da yadda makiya Harkar Musulunci ke ta kokarin samar da rubuce-rubuce da littafai da ma fima-fimai a kan Harkar Musulunci ta fuskar da ba haka Harkar take ba, da yadda magoya bayan Harkar Musulunci ke kishin ruwan samun sahihin bayani a kan ma’ana da manufar Harkar, an kuma yi babi na musamman da ke bayani a kan wadanda suka yi aikin duba littafin a tsawon shekara guda kafin a kai ga matakin buga shi.


Daga cikin wadanda Cibiyar Wallafa ta ba aikin gyara littafin da ba da shawarwarin da suka dace akwai; Shaikh Yaqubu Yahya Katsina, Shaikh Adamu Tsoho Ahmad Jos, Shaikh Abdulhamid Bello Zariya, Shaikh Abdurrahaman Abubakar Yola, Shaikh Sunusi Abdulqadir Qoqi, Furofesa Dahiru Yahya (BUK), Furofesa Abdullahi Danladi (ABU), Furofesa Isah Meshalgaru (ABU), Dakta Maimuna Hussaini (BUK), Dakta Ibrahim Sulaiman Rinji (BSU), Malam Ibrahim Musa (Editan Almizan), Oga Danjuma Katsina (Hantsi), Malam Ibrahim Gamawa (Alqalami), Malam Haruna Uba Jahun (Tsokaci), Malam Muhammad Sulaiman Kaduna (Tambihi), Malam Aliyu Saleh (Almizan), Hajiya Jummai Ahmad Karofi, Malam Yusuf Abdullahi Kano, Malam Rabi’u Shu’aibu Ringim, Malam Nuraddeen Aliyu, Malam Bashir Yusuf Allamah, Muhammad Mukhtar Idrees, da wasunsu da dama. Da yawansu sun yi gyare-gyare da tsokaci sun mai do an shigar don inganta littafin. 


Da yake tsokaci a kan littafin, Farfesa Isah Hassan Meshalgaru, na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ya bayyana cewa: “A wannan zamani na farfagandar maqiya ta hanyar kafafen yada labarai na zamani, akwai buqatar fito da gaskiya daga ma’abotanta, don tallatawa da yadawa ga al’umma, don hakan ya zamo zabi ga masu nazari da bibiya.” Ya cigaba da cewa: “Samuwar wannan littafi na ‘Da’awar Shaikh Zakzaky’ a daidai wannan lokaci, tamkar bishe hasken qarya da farfagandar maqiya ne akan Harkar Musulunci, domin abubuwan da aka fada game da Harkar abubuwa ne da suke a zahiri da kowa ke iya shaidawa, ba labaran gaibu ne da ke boyuwa ga idanu ba. Tabbas wannan littafin ya cancanji jinjina da samun karbuwa!”.


Daya daga cikin Malaman Harkar Musulunci, Shaikh Yaqubu Yahya Katsina, wanda yana daga cikin wadanda littafin ya shafe shekara guda cur a hannunsu suna nazari da bitansa, a karshe ya rubuta cewa: “Ban san wadanne kalmomi zan yi amfani da su, wanda suka dace in bayyana muhimmancin wannan littafin da dacewar fitowarsa a wannan lokacin ba. Duk da cewa an makara qwarai, ya kamata a ce tuntuni aka samar da irin wadannan littattafan, ya dace ne rubuta tarihin Harka ya riqa tafiye kafada da kafada da ita Harkar, amma ba a samu yin hakan ba sai da Harkar Musulunci ke cika shekaru 40, kun ga ba zai yiwu a iya rubuta duk abubuwan da suka faru a shekaru 40 ba.”


Shaikh Yakubu ya cigaba da cewa: “Na’am, duk da makarar da aka yi, wannan littafin zai bada gudunmawa qwarai wajen haskawa duniya mece ce Harkar Musulunci, meye hadafinta, ya take gudanar da ayyukanta! Zai dace qwarai a fassara littafin zuwa manyan harsuna na duniya, don fadada yaduwar saqonsa”.


Ita kuwa Hajiya Jummai Ahmad Karofi, Fitacciyar Marubuciyar Littattafan Hikaya, masaniya kuma ma’abociyar fikirar Gwagwarmayar Musulunci, ta wa littafin tsokaci da cewa: “Wannan littafin ya qayatar da ni sosai, domin an yi bincike, zai iya amsa tambayoyi da yawa na neman sanin wani abu game da Harkar Musulunci bakin gwargwado, wani abun burgewa shi ne, bayani akan aqalla fanni hudu na Harkar Musulunci littafin ya qunsa, tarihi, hadafi, ayyuka, da kuma tsari, lallai littafin zai amfani al’umma, musamman mutanen qasashen waje, da manazarta, da kuma yara masu tasowa, har ma kowa da kowa, domin an yi bayanan cikin sauqaqan kalmomin da za a yi saurin fahimta”.


 Me ke cikin wannan littafin da masana suke masa irin wadannan tsokaci?


Littafi ne da ya fara da bayani a kan Kasar Nijeriya da yadda aka kafata a asali, har zuwa kan bayyanar Shaikh Ibraheem Zakzaky, ya ba da takaitaccen tarihinsa daga kakanninsa har zuwa fara gwargwarmayarsa a jami’a. Sannan ya shiga bayani a kan Ma’ana da manufar Harkar Musulunci.


 BABIN FARKO NA LITTAFIN ya yi Magana ne kan Ma’anar Harkar Musulunci, Sunan Ma’abota Harkar Musulunci, Wanene dan Harkar Musulunci?, Dalilin Fara Da’awar Harkar Musulunci, Manufa Da Hadafin Harkar Musulunci, Burin Harkar Musulunci, Hanyar Kawo Sauyi A Harkar Musulunci, Kafa Gwamnati A Fikirar Harkar Musulunci, ya karkare da bayani a kan Harkar Musulunci Da Matakan Tabbatar Da Addini.


 BABI NA BIYU A LITTAFIN KUWA yayi bayani ne a kan Hadafi (Principle) Da Salo (Policy) Na Harkar Musulunci, Tantance ‘Hadafi’ Da ‘Salo’ Na Harkar Musulunci, Harkar Musulunci Da Salonta, Tasirin Salo (Policy) Ga Da’awar Addini, ya kuma karkare da bayani a kan ‘Ci-Gaba’ A Fikirar Harkar Musulunci.


 BABI NA UKU A LITTAFIN ya Kunshi Tarihin Tsirowar Harkar Musulunci a Nijeriya ne. Inda ya yi gamsasshen bayani a kan Da’awar Sirri Ta Shekara Uku da Shaikh Zakzaky yayi kafin bayyana da’awa a fili, da kuma yadda aka bayyana da’awar, Jawabin Shaikh Zakzaky Na Shelar Funtuwa 1980 tare da bayani a kan Saqon Da Jawabin ‘Shelar Funtuwa’ Ya Qunsa.


 BABI NA HUDU A LITTAFIN ya yi bayani ne a kan Tsarin Harkar Musulunci, inda ya fara da fasalin da ke bayani a kan Bambancin Harkar Dda Qungiyoyin Addini, ya yi fasali a kan Harkar Musulunci Ba Qungiya Bace, inda ya yi gamsassun bayani a takaice a kan yadda ya zama a Harkar Musulunci Ba Kundin Tsarin Mulki, Ba Gungun Masu Mulki, Ba Tsarin Rijista, Ba Tsarin Zabe, Ba Wa’adin Gudanarwa, Ba Mustawar Takardu, Ba Kora Ko Ritaya, Ba Tanadadden Hukuncin Laifuka, Ba Hargitsi da Qyama, sannan aka rufe babin da fasalin da ke bayani a kan kalmar “Jagora” a Harkar Musulunci.


 BABI NA BIYAR A LITTAFIN ya yi bayani ne a kan Bangarorin Gudanarwa a Harkar Musulunci, inda ya yi fasulla akan; Tsarin Gudanarwa; Jagora, Wakilan ‘Yan uwa da kuma ‘Yan uwna. Har ila yau, ya yi bayani dangane da Da’ira a Harkar Musulunci, Da’iratul Amma, manya da kananan da’irori, halkoki da majalisai.


 BABI NA SHIDA A LITTAFIN cikin gamsasan bayanai ya yi magana a kan Lajanonin Harkar Musulunci da ayyukan ko wacce daga cikinsu. Ya fara da fasali a kan ma’anar Lajana a Harkar Musulunci, Dandali (Forum) a Harkar Musulunci, Banbanci Tsakanin Lajana Da Dandali, Fitattun Lajanoni A Harkar Musulunci, Kwamitoci A Harkar Musulunci. Sannan ya shiga yin tsokaci akan hakikanin ayyukan Lajanoni, musamman ma Lajanar Harisanci, Mu’assasar Abul-Fadal Abbas, Lajanar ‘Ittihadush-Shu’ara’, Mu’assasar Kula Da Iyalan Shahidai, Lajanar Kiwon Lafiya da bada Agaji, Lajanar kula da makarantun Harka, Lajanar Ilimi Da Tarbiyyah, Lajanar Yada Labarai, Lajanar kula da dab’i da buge-buge, Lajanar Fimafimai (A.M. Production), Mu’assasar Zahrah (SA), Lajanar Ashura, Tattaki Da Maulidi, Cibiyar Wallafa Da Yada Ayyukan Jagora (H) da sauran kwamitoci a Harkar Musulunci.


 BABI NA BAKWAI kuwa ya yi bayani ne a kan Dandamaloli (Fora) a Harkar Musulunci, inda ya kawo misalan fitattu daga Dandamalolin da ake da su a Harkar Musulunci akalla guda 15 tare da gamsasshen bayani a kan kowannensu. Daga wadannan Dandamalolin akwai Dandalin Qwararru da Ma’aikata (Resource Forum), Dandalin dalibai ‘yan makaranta (Academic Forum), Dandalin ‘yan uwa mata (Sisters Forum), Dandalin masu hannu da shuni (Ahlid-Duthour), Dandalin Matasa (Youth Forum), Dandalin ‘yan Jarida (Media Forum), Dandalin Marubuta/Mawallafa (Writers Forum), Dandalin masu mu’amala da yanar Gizo (Internet Forum), Dandalin masu Fasahar Zamani (Technology Forum), Dandalin Mahaddata Alqur’ani (Huffaz Forum), Dandalin jikokin Annabi (S) (Shurafa’u Forum), Dandalin Fulani (Kautal-Ko’e Julbe), Dandalin Barebari (Kanuri Forum), Dandalin Samar da Hadin Kai (Wahda Forum), Dandalin Injiniyoyi (Engeerneers Forum), Dandalin Direbobi masu sana’ar tuqi (Drivers Forum), da dai sauransu.


 BABI NA TAKWAS kuwa ya yi bayani ne a kan Aikace-aikacen Harkar Musulunci, inda ya yi fasulla da gamsassun bayanai a kan Ta’alimi, Ribadi, Lailatut Tarbiyya, Ijtima, Daura Ilmiyya, Mu’utamar, Wa’azozin Juma’a, ya karkare da bayani a kan yadda Harka ke tura dalibai don karo ilimi.


 BABI NA TARA A LITTAFIN ya yi bayani ne a kan Tarurruka (Programs) a Harkar Musulunci, inda ya bayani gamsasshe akan tarurukan murna da biki guda 11 da Harkar Musulunci ke gudanarwa a shekara. Sannan ya kawo tarurrukan jaje da juyayi guda takwas da Harkar ke yi akalla a duk shekara. Ya kuma yi bayani a kan tarurruka guda biyar na karawa juna sani da fadakar da al’umma (Tablig) da Harka ke yi a kowace shekara. Ya kuma jimlace ya kawo jadawalin Tarurrukan guda 36 da Harkar Musulunci ke gudanarwa a kowace shekara.


 BABI NA GOMA A LITTAFIN ya fadada bayani ne a kan muhimman tarurruka guda 12 a shekara da Harkar Musulunci, inda ya kawo tarihinsu tare da bayani a kan yadda kowanne ke gudana. Tarurrukan sun hada da; Jerin zaman makokin Ashura na Al-Muharram, Yaumul-Arba’in na Shahadar Imam Hussain (AS), Maulidodin Annabi (S) na Zaune, Makon Hadin kan Musulmi, Maulidin Annabi (S) na 17 ga Rabi’ul Auwal, Makon Maulidin Sayyida Zahra (SA), Makon Imam Khumaini, (Imam’s Week), Yaumus-Shuhada (Ranar Tunawa da Shahidai), Nisfu-Sha’aban (Maulidin Imam Mahdi (AF), Shahadar Amirul Muminin Imam Aliy (AS), Maulidin Imam Ridah (AS) da kuma bikin Idin-Ghadir (Eedul Ghadeer).


 BABI NA 11 A LITTTAFIN ya kunshi bayanai ne a kan manyan Muzaharori da Harkar Musulunci ke gabatarwa a shekara, tarihinsu da yadda suke gudana. Muzaharorin sun hada da Muzaharar Ashura ta 10 ga watan Al-Muharram, Muzaharar Maulidin Annabi (S) (ta 12 ga R/Auwal), Muzahar Maulidin Annabi (S) (ta 17 ga R/Auwal), Muzaharar Maulidin Sayyida Zahra (SA) (20 ga J/Thani), sai Muzaharar Qudus ta Juma’ar qarshen Ramadan. Sannan babin ya karkare da dogon bayani a kan Tattakin Arba’in na shahadar Imam Hussain (AS) da yadda yake gudana daga zangonni bakwai.


 BABI NA 12 A LITTAFIN ya kawo wasu abubuwa na musamman na halayyar ‘yan Harkar Musulunci ne, inda yai magana a kansu, da suka hada da Lizimtar shiru da natsuwa, amana da gaskiya a tsakanin juna, bin umurni da tsari, juriya da dakewa, samar da mai gudanarwa, ‘yancin kai da karbar tunani.


 BABI NA 13 kuwa ya yi bayani ne a kan wasu nasarori da Harkar Musulunci ta cimma a tsawon shekarun faruwarta. Daga ciki akwai farfado da tunanin addini a zukatan al’umma, Istibsari (Farkawa) daga Sunnah zuwa Mazhabar Ahlulbait (AS). Tasirin Harkar Musulunci a Duniya, Nasarar Dogaro da kai, Hada kan al’umma, kyakkyawar zamantakewa, raya zukatan al’umma, tsayuwa da ibada da kuma hidimtawa al’umma.


 BABI NA 14 kuwa ya yi bayani ne a kan makiya Harkar Musulunci, inda ya kawo gungun masu gaba da Harkar Musulunci, kowannensu aka masa babi na musamman mai kunshe da bayani a kansa da salon gabarsa ga Harkar. Daga wadannan gungun akwai; Tinkahon Duniya (Amurka, Isra’ila, Ingila da Saudiyya), Masu Mulki (Gwamnatin Nijeriya), Wahabiyawa da kuma ‘Yan Shi’ar Gargajiya (Commercial Shi’a). Har ila yau a babin akwai fasula da ke bayani a kan irin jarabawowin da wasu ‘yan uwa kan fuskanta daga iyaye da danginsu.


 BABI NA 15 yayi bayani ne a kan wasu abubuwa da za a iya kallonsu a matsayin matsaloli da suke bijirowa a cikin Harkar Musulunci. Daga cikinsu akwai raunin wakilci, kuskuren fahimta da karancin fahimtar mas’uliyya, kuskuren daukar mataki, gurguwar fahimtar hadafi da karancin fikira.


 BABI NA 16 kuwa shine babi na kusa da mafi girman fadi da bayanai, domin kuwa ya kawo gamsassun bayanai da tarihi da yadda wasu fitintinu suka rika faruwa ne a Harkar Musulunci. Daga Fitintinun da littafin ya fede akwai; Fitina Darkawiyya wacce ta fara a 1980 ta kare a 1986. Fitinar Zuhudu da ta fara a 1984 zuwa 1990, Fitinar Tawayiyya da ta kawo karshe a 1994, Fitinar Taqalidi da ta 1999 zuwa gaba. Bayan an hallale bayanai sanka-sanka a kan wadannan fitintinun sannan kuma aka kawo bayani a kan wasu kananan Fitintunun, kamar Santsin Mai Sandar Karfe na 1982, da Batun ‘Yan Jumudi na 1993 da sauransu. 


 BABIN KARFE A LITTAFIN wato babi na 17, shine mafi girman babi a cikin littafin, domin kuwa ya tsaya ya yi bayani sanka-sanka da kowannensa zai iya zama littafi mai zaman kansa a kan manya-manyan waki’o’i guda bakwai (7) da suka auku ga Harkar Islamiyya, wanda suka hada da; Waki’ar Kafancan 1987, Waki’ar Katsina 1991, Waki’ar Abacha 1996, Waki’ar Sokoto 2005&2007, Waki’ar Quds 2014 da kuma Waki’ar Zariya ta 2015, tare da wasu daga kananun waki’o’in da suka rika biyo bayan ta Zariya din da shekara guda akalla.


 A KARSHE:


Littafin DA’AWAR HARKAR MUSULUNCI, ko da yake ba yana wakiltar Harkar Musulunci bane, sai dai Littafi ne da ya kamata ace kowane almajirin Shaikh Zakzaky ya mallake shi, don sanin inda aka faro da inda ake a yanzu, tare da taskacewa ‘ya’ya da zuriyarsa tarihin Harkar a cikin gidansa. Ya kamata ace an yi ribibi wajen sayan adadi masu yawa na littafin don kyautarwa ga wasu da ake sa ran zai amfane su. Ko ba komai, bugun farko da aka wa littafin a yanzu haka kwara dubu daya ne kacal! Kowane daya farashinsa naira dubu daya (N1,000) ne kacal. Ku yi maza ku yi tanadi don mallakarsa da zaran ya fito, nan da yan kwanaki. 


 Tuni aka fara aikin fassararsa zuwa yaren Turanci a matakin farko, ba da jimawa ba insha Allah aikin zai kammalu. Kuma muna fatan nan da wani lokaci, littafin ya fassaru zuwa Larabci, Farsi da sauran yaruka daban daban don isar da sakon da ke cikinsa ga duniya baki daya.


— Saifullahi M. Kabir

Cibiyar Wallafa Da Yada Ayyukan Shaikh Zakzaky (H)

26/1/1442 (14/9/2020

cibiyarwallafa@gmail.com

www.cibiyarwallafa.orgCINIYAR WALLAFA TAZO MAKU DA WANI SABON LITTAFI


Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky