Hirar jaridar dailytrust tare da Sheikh zakzaky a Shekarar 2009

 WATA HIRA DÀ SHEIKH IBRAHIM ZAKZAKY (H) YAYI DA JARIDAR DAILY TRUST A 

10/10/2009. 


TRUST: Kwamishinan ’yan sanda na jihar Kaduna, Tambari Yabo, an jiyo shi yana cewa 

duk da cewa an hana duk wata zanga-zanga ta addini, a taron su na Kwamitin tsaro 

an ce musu su kyale mabiyanka su yi zanga-zangarsu, kana ganin gwamnatin ba za ta iya 

dakatar da ku bane cikin sauki, dama kuma wasu na ganin cewa gwamnati ba za ta iya iko 

da kai da mabiyanka ba, kana jin wannan shi ne 

dalilin da ya sa Kwamitin tsaron ya zartar da shawarar 

kyale ku ku yi zanga- zangarku duk da cewa an hana? 


SHAIKH ZAKZAKY: To, ni dai ban da masaniyar wani hani da aka yi, ban taba jin an 

hana wata muzaharar addini ba. Ban kuma taba sanin an kyale ba. Abin da muka sani shi ne 

mun shafe shekaru 26 muna irin wannan jerinn gwano. 


Muzahara ce ta nuna goyon baya ga Palasdinawa, kuma ana yin sa a kasashe da dama 

na duniya. In ka kira shi na addini, kana kuma iya kiran sa na jin kai irin na bil’adama. 


A wasu wuraren ma irin su London, Malaman 

Yahduwa ma kan shiga cikin sahu, da Fada-Fadan kiristoci, mutane masu bin wasu addinai 

da dama duk suna shiga ciki. A Venezuela ma, Shugaban kasar, Hugo Chavez, da kansa 

kan shiga sahu tare da jama’a da dama, wadanda yawancinsu ba musulmi bane, haka ma 

a Palasdinun kanta. Saboda haka ban ga ta inda wani zai kira wannan taro na addini ne kadai 

ba. Taro ne na wasu mutane da suka fadaku cewa ba wata hujja da zai sa wata kasa ko 

wasu mutane su mamaye kasar wasu, su kafa tasu kasar. 


Ciki kuwa har da wasu Yahudawa wadanda su ma Isra’ilawa ne, amma ba su ganin 

akwai adalci a cikin mamayar Palasdinu. Amma mu a nan banda masaniyar cewa an hana 

mu yin muzahara, ba ni kuma da masaniyar an kyale mu. 


TRUST: Ko kana da na sanin irin yadda ake kashe mabiyanka, musamman daga zamanin 

Abacha kawo yanzu? 


SHAIKH ZAKZAKY: Mu dama mun san cewa wannan 

hanya da muke bi haka ta gada. Ita ce hanyar wadanda suka gabata, su ma irin wannan 

ta faru gare su. Lokacin da Manzo (SAWA) ya fara kira a Makka kafin ya yi hijira zuwa Madina 

an samu wasu shahidai wadanda suka samu shahada ba don komai ba sai don sun ce 

Ubangijinsu shi ne Allah. Haka nan kuma duk wata gwagwarmaya ta musulmi, irin wadannan 

abubuwa kan faru. Abin da kawai za mu ce shi ne kamar 

gwamnatocin Nijeriya ba su kai mustawar da za su fahimci lokacin da ya kamata su kai duka ba. 


Kullum suna kai duka ne a lokacin da bai dace ba. Ai 

sai in ka ga wani abu da kake tsoron zai kau da kai ko ya fi karfinka, to shi ne za ka ce bari ka 

bude wuta. Amma wannan ai wata zanga-zangar lumana ce kawai suka kai wa hari. Da alama 

suna yin haka ne bisa jahilci ko kuma saboda wata kiyayya da suke da ita a zuciyarsu. 

To, maimakon ka bar kiyayyar da ke zuciyarka 

ta rufe hankalinka, kamata ya yi ka sa hankali da fahimta. 

In har wannan abin hadari ne, to yaya za ka yi da shi? Mu makaminmu shi ne amfani 

da hankali, muna magana ne tare da rubuce-rubuce. 


Muna amfani ne da ilimi, don haka ba za ka iya 

fada da wannan da bindiga ba. 


TRUST: To, ko Malam zai ba mu damar mu ji daga 

gare shi, manufofin wannan Harka? 


SHAIKH ZAKZAKY: Wannan Harka da mutane 

take magana, kodayake wasu suna cewa da gwamnati muke yi. Mu ba magana da gwamnati 

muke yi ba, da mutane muke yi. Muna so ne jama’a 

su fahimci hakkin da ke kansu a matsayinsu 

na Musulmi. Idan ka ce kai musulmi ne, to bai yi daidai da kamar ka ce kai Bahaushe ne ko Ibo 

ko Bayarbe ba, wanda ka zama a sanadin haihuwa. 


Shi Musulunci ana sanin sa ne a matakai uku: 


Imani a zuciya, 

furuci da baki 

da kuma aiki a gabobi. 


Wadannan ne ke maishe ka Musulmi. To, muna 

tunatar da mutane ne ayyukan da suka hau kansu a matsayinsu na musulmi, wanda 

babba a cikin wadannan shi ne cewa tunda mu musulmi ne, to dole ne ya zamanto Musulunci 

ne ke tafi da rayuwarmu. Ba mu da wani uzuri da 

za mu gabatar gaba ga Allah a ranar tashin kiyama mu ce wasu mutane ne suka zo suka yi 

mana mulkin-mallaka suka dankara mana wani abu sabanin Musulunci. Wannan ba zai karbu 

a matsayin uzuri ba saboda za a tambaye mu me muka yi don mu ga cewa lalle mun bi dokokin 

Musulunci a rayuwarmu? Wannan shi ne aikin Harkar Musulunci. Bari in maimaita wannan, 

mutane muke fuskanta, amma ba gwamnati ba, amma ita gwamnatin kullum 

cikin tsoro take tana ganin ita ake nufi. 


Haka abin ya gudana a zamanin Manzannin Allah 

Ta’ala, da suka zo da kira ga mutane, sai Hukumomi suka dira a kansu. 


TRUST: Yaya za a yi 

ka samu mutane saboda yana da wuya ka tara 

mutane, in ba kana da mulki ba? Kana ganin 

za ka ci gaba da yin wa’azi kawai? 


SHAIKH ZAKZAKY: To, kamar yadda kake iya gani, ba 

na jin ko da wani yana cikin gwamnati, ko da ma 

shi ne Shugaban kasa, in ya kira mutane za su fito 

a kashin kansu haka. Mun ga yadda Abacha ya so ya tara mutane miliyan biyu a Abuja, amma 

mutanen da ya iya tarawa ba su shige dubu 

ashirin ba. Kuma muna iya ganin irin gangamin goyon bayan da aka yi wa Abacha 

a garuruwa daban- daban. A wani lokaci a Kaduna an yi irin wannan gagarumin gangamin 

aka nufin gidan Gwamnati, amma na mutane 

25 kacal, suka je don nuna goyon baya ga Abacha, a lokacin kuma yana kan mulki. To, mu 

kiranmu yana zuwa ga zukatan mutane ne, kamar 

yadda za ka gani daga dimbin jama’ar da ke zuwa tarurrukanmu. 


Gwamnati da kanta ta ce Ashurar da muka yi bara 

kusan mutane miliyan biyu suka halarta. Wannan a ta bakin gwamnati kenan, amma ba 

mu san adadinsu ba. Kuma a lokacin bukin Maulidi suka ce mutane miliyan goma ne suka taru.

 

Ba na tsammanin wani daga cikinsu yana jin zai 

iya tara mutane kusa da wancan adadi. 


TRUST: Yaya za ka iya kankare rade-radinmu da ake yi cewa kana da dangantaka 

da kungiyoyin kasashen waje da wasu gwamnatocin kasashen wajen? 


SHAIKH ZAKZAKY: Wace irin dangantaka kake magana? 


TRUST: Kowace irin dangantaka nake nufi. 


SHAIKH ZAKZAKY: Lalle wannan Harka Islamiyya 

ta kasa-da- kasa ce, ta ratsa kan iyakokin kasashe. 

Wannan Harka tana da karfi a kasashen Hausa 

na Arewacin Nijeriya, Kamaru, Chadi da jamhuriyar 

Nijar, amma ta yi kama da sauran Harkoki da suke da manufa iri daya. Don haka muna 

kallon Harka Islamiyya a matsayin wani tunani game- duniya da ke ta tashi a sassan 

duniyar gaba daya. Zai iya zamowa tana da karfi a 

wasu wurare saboda tarihin wuri, misali tana da 

karfi a nan saboda a tarihi tsarin Musulunci ya taba iko kafin zuwan Turawan 

mulkin- mallaka. Don haka abin da mutane suke kauna shi ne dawowar abin da suka rasa. Shi 

ya sa ka ga kiran nan na samun amsuwa sosai a nan. 


Ba zai zama da sauki ba a wasu wuraren. Don haka 

ita Harka Islamiyya akwai ta a ko’ina ba lalle a nan Nijeriya ba. 


TRUST: A nan Nijeriya ana nuna cewa ba ka yarda 

da gwamnati ba, wannnan gaskiya ne? 


SHAIKH ZAKZAKY: Da ma su wadanda suke da iko 

kullum suna neman wani dalili ne da zai sa su auka 

mana. Ga misali, wane abu ne muka taba yi wanda ya nuna cewa mu masu karya doka ne? 

Ba za su iya nuna wani abu guda da muka yi ba. Duk 

abin da muke yi muna yin sa ne cikin kwanciyar hankali da lumana, amma yana firgita su 

ne saboda mutane suna amsa mana, wannan shi ne kawai. 


TRUST: Kana da wani abu da kake so ka ce, amma 

ban tambaya ba a wannan hirar? 


SHAIKH ZAKZAKY: Zan so in yi kira ga mutanen 

kasar nan, musulmin cikinsu musamman, cewa Musulunci shi ne makomar wannan kasa nan 

gaba. Na farko dai musulmi sune majoriti. Ban san me ya sa wasu ke da shakku kan wannan 

batu na cewa musulmi ne majoriti ba, alhali kuwa wannan wani abu ne da babu shakku a 

kansa tunda dai ba wani dalili da zai sa Turawan 

Mulkin-mallaka su fifita musulmi a kan sauran a 

lokacin da suka yi kidayarsu. A dukkan kidayarsu musulmi ke da kashi 66 cikin dari na 

yawan mutanen kasar nan. Don haka babu wani 

kokwanto cewa musulmi ne majoriti a kasar nan. To, kuma suna da addini wanda ke da 

ka’idoji da ke tafi da dukkan bangarorin rayuwa, ciki kuwa har da siyasa. Akwai iyaka ga 

iya lokacin da za a ci gaba da mulkar ku da abin da ya saba wa dokokin Allah. 


Insha Allahu watan wata rana wadannan dokokin 

su za su yi mulki. Wannan kuma ba zai auku haka nan kawai ba, sai ta hanyar yin kira da 

wayar da kan jama’a, kuma hakan yana samun 

karbuwa.


Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky