MAZA SUN DAWA SAI NISA.

 *ALKALAMI KA FI REZA KAIFI*

M. I. GAMAWA 07035577745


 Dukkan alamu sojojin Najeriya sun hadiyi tabarya. Kamar yadda Bahaushe ke cewa, “wanda ya hadiyi tabarya tsaye zai kwan,” Sojojin Najeriya sun fahimci jini duk jini ne, amma banda na dan Sarki. Sun sha aikata danya su tsira babu mai tuhumar su. Kama daga yakin Basasa zuwa ta'addancin gidan Fela da ya jawo mutuwan mahaifiyarsa, matar da ta fara tuka mota a Najeriya, zuwa Zaki Biam da Udi da ke jihar Benuwe da Bayalsa a tartibance. Haka ya sa girman kansu ya karu, dagawa ta yawaita, rashin hankali ya wuce na mai shiga turu.

Da ma suna jiran Soja a farar hula domin ci gaba da aikata mugun aikin da suka saba na kashe ’yan kasa da azabta su. Ilai kuwa sai ga Buhari, wanda babu tausayi, babu ragowa balle imani a zuciyarsa. Ganin na gida ya samu sai suka fahimci, Tula ba ta rabu da Kalaye ba, suka bude kofar muguntan da suka rufe a sakamakon dawowar dimokradiyya. Shi kuma Buhari ya jinjina musu bisa wannan danyen aiki nasu. Bai damu da abin da duniya za ta fada a kansu ba. Bai damu da wulakantawa da kashe ’yan kasa da wadannan dabbobi a cikin mutane ke yi ba. Shi dai a nuna wa talakawa yana mulki.

Mulkin da ba shi da bambanci da fir'aunanci. Irin wannan rashin lissafi da rashin basira ne suka sabbaba kisan kare dangin da maganarsa ta ki ci, ta ki cinyewa. Duk wani sharri da tuggu an yi don kashe wannan abin kunya, amma abin ya ci tura. Kama daga tallace-tallacen karya a gidajen talabijin da Jaridu zuwa aiki da jakunan Yahudawa masu masallatan da aka gina don ruruta gaba tsakanin musulmi. In ba ka san su ba su ne Wahabiyawa da Salafawa, masu shaguna da sunan masallatai. Yanzu kusan kowane titi da ke wani birni a Arewacin kasar nan banda Benuwai da Kwara akwai masallatan wadannan zauna-gari-banzan. Ba su da aiki sai aikin banza, aikin da Shaidan ke maraba da shi, don tsananin muninsa. Aikin fasa gida don kasuwa ta yi kyau - kasuwar da ba tasu ba, kasuwar Yahudu da Nasara asara.

Masha Allah, duk da wannan mugun aikin gayya da ya fi kama da daukar jinka, Shi’a tana nan sai kara ruruwa take yi kamar wutar daji. Tana cin kowane unguwa da gida. Tana bi kauyaka da birane, lungunsu da sakonsu. Madalla da Shi’a a Najeriya.

Mai neman fushin Allah bai rabuwa da take hakkin masu hakki. Kamar yadda Shi’a ta shigo haka masu cutarwa da kashe ’yan Shi’a suka bayyana. Cutarwa da kashewa ya zama aiki bakin rai bakin fama. An manta Arewacin da ake karya da shi a Najeriya, kamar yadda karfin mulki ya mantar da su gane ’yan’adamtaka. Kafin a ankara sai ran dan Shi’a ya zama kamar ran cinnaka, ba a tsoron kowa don an kashe. Wannan bai isa ba, kuma bai tsaya nan ba, sai makisan zamanin Buhari suka bai wa wadanda ba musulmai ba kwangilar bata Shi’a da nuna su a matsayin ’yan ta'adda. Wadannan bayin duniya asararrun lahila, ba su damu da cin mutuncin da za a yiwa Musulunci wajen bata Shi’a da wanda ke jagorantar ta a kasar nan ba.

Kalmar shahada da kabbara sune abin wasa da isgili a fim din. Haka rawani da alkyabba sune rigar jarumin fim din. Duk wannan bai zama abin damuwa ga wadannan kazamai masu amsa sunan musulmi ba, muddin fim din zai nuna wa duniya cewa Shi’awa ’yan ta'adda ne. Su dai burinsu su saka kaki su samu kudi su sha giya su tsunduma cikin tekun alfasha.

Suka bai wa wani kafiri kwangilar rubuta luttafi don bata Musulunci da sunan bata Shi’a, babu abin da ya dame su.

Abin tambaya ga Buhari, Burutai da yaransu shi ne: Me suke tsoro ne har suka manta da girman addininsu, suka mika shi ga makiyansa don bata shi? Shin wannan ba lasisi suka bai wa wadanda ba musulmi ba na bata addinin Musulunci da Musulmi? Kiyayyarsu da Musulunci har ta kai haka? Ko sun fita a Musulunci ba sa kunyar ’yan’uwansu musulmi? Wadannan tambayoyi ne ga wadanda suka biya ladan wannan aikin ke nan.

Amma wadanda suka yi aikin fim din. Na yi magana da mutane biyu da sunayensu ya fi bayyana a fim din. Wato Kingsley Oji da Pete Edochie. Na yi magana mai tsawo da dukkan su ba sau daya ba, ba sau biyu ba. Abin da na fahimta shi ne, wanda ya karbi kwangilar shi ne Kingsley Oji. Domin da kamfaninsa aka yi wannan danyen aiki. Bincike daga hukumar rijistan kamfanoni (CAC) ya nuna cewa Kingsley da Matarsa ke da kamfanin da ya dauki nauyin aikin fim din. Sai dai ba a shirye yake ya fadi wanda ya sa shi wannan kazamin aiki ba. Amma duk wanda ya ji jawabin Pete Edochie zai fahimci cewa da hannun sojoji a ciki.

Lokacin da na kira Edochie na kuma ba shi bayani dalla-dalla kan waki'ar Zariya, sai da ya yi hawaye cikin tausayi. Ya kuma ce tabbas na kare shi da abin da bai sani ba kafin ya bayyana a cikin wannan fim. Ya sanar da ni cewa an kira shi ne ya yi aikinsa, kuma ya yi. Da na tambayeshi ko ya san littafin da ake fassarawa a majigance? Sai ya ce tabbas bai sani ba. Ya ce dadaddiyar sanayya ce ta sa yake wa Kingsley aiki, ba tare da binciken kwakwaf kafin ya fara aikin. Wannan dai kadan ne daga tattaunawa ta da Pete Edochie haifaffen Zariya. Ya kuma yi mini alkawarin neman littafin daga Kingsley domin ya karanta. Sai dai wani abin mamaki shi ne Kingsley ya nuna mini shi bai ma son littafin batanci mai suna ‘Fatal Arrogance’ ba.

Lokacin da Kingsley ya koka cewa, ana masa barazana, na ce masa barazana ba daga gare mu ba ne. Ya je ya bincika, kuma kar ya fasa daukan mataki. Ya yi mana tayin ko wasu daga cikin mu za su je Inugu kallon fim din kafi a sake shi a kasuwa?Amsa dai ita ce ba za mu je ba. Wannan ba amsata ba ce, amsa ce daga manyanmu. Shi ma babban Lauyan Najeriya da ke tare da mu haka ya ce, har da karin sakon da ba zan fada ba yanzu.

Dukkan su sun fada mini cewa, abin da muka gani ba ya cikin fim din. Abin da ya faru shi ne, kamar a ce Dan Ibro ne, ya fito a fim na Darikar Tijjaninya, sai a ce ya fito kamar Shaikh Dahiru Bauchi (ra), sai aka gan shi yana shan taba a cikin suturar da ya fito a fim din bayan an fara ko kafin a fara dauka. Abin da ya faru ke nan. Wannan misali ya yi daidai da abin da Yakubu Muhammad ya fada wa BBC. Ko haka ne? Na shiga ban dauka ba, ba ta fid da 6arawo! Wani abu muhimmi shi ne na taskace kusan duk maganganun da na yi da Kingsley da Pete don gobe insha Allah.

Darasin da musulmi za su koya shi ne lokaci ya zo na rage kaifin kiyayyar da ke tsakanin su. Kiyayyar da ta kai har kafiri ya samu lasisin wasa da addinmu madaukaki. Watakila wani wawa ya bi sahun gwamnatin Buhari da ta dauki nauyin wannan kazantaccen fim wajen zaton batanci ne ga Shi’a da Sayyid Zakzaky kawai. Ya kamata mai irin wannan tunani ya amsa wadannan tambayoyi. Shin kalmar LA ILAHA ILLALLAH ta 'yan Shi’a ce kadai? ALLAHU AKBAR ta ’yan Shi’a ce kadai? RAWANI na ’yan Shi’a ne kadai? ABAYA ta ’yan Shi’a ce kadai? Amsa dai ita ce, A'A!

In haka ne don me kiyayya ga Shi’a za ta sa a jaza wa kafirai bata Musulunci? Wani abu da na fada wa Kingsley shi ne wannan fim ba wai na bata Shi’a kadai ba ne, na bata Musulunci ne baki dayan sa. Akwai lokacin da na ce masa shin akwai bambanci tsakanin bata shaksiyar Papa Roma da bata addinin Kirista? Sai ya ce ba zai amsa wannan tambaya mai sarkakiya ba. Wani abu game da wannan fim shi ne ya kamata ’yan’uwa su yi taka tsantsan, su bar ahlin abin su yi magana. Ji da cewa suna da goyon bayan gwamnati dubu bisa dubu.

Wannan shi ma wani tarko ne na kokarin mai da Liman dan fashi. Abin da ita gwamnati ke nema da wannan fim shi ne ta da hankalin ’yan’uwa su yi hatsaniya don su samu hujjar kara rike Sayyid in har kotu ta sake shi a ranar ashirin da tara ga wannan watan. Dole mu nuna wa gwamnati ta yi kadan, wayonta ya gaza tsawon Wada. Lokaci ya yi da ya kamata gwamnati ta fahimci cewa Inyamurai ba za su iya yin abin da Salafawa suka kasa yi shekaru aru-aru ba. Gwamnati a cikin Villa take. Shi kuma yaki ana yin sa a dawa ne. Su kuma MAZA SUNA DAWA, SAI NISA.

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky