NASIHAR SHEIKH ZAKZAKY GA 'YAN UWA MASU AMFANI DA KAFAR SADA ZUMUNTA

 


NASIHAR SHAIKH ZAKZAKY GA ‘YAN UWA MASU AMFANI DA SOCIAL MEDIA


Wannan wata nasiha ce da Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya yiwa ma’abota amfani da shafukan sada zumunta (social media) musamman ‘yan uwa Musulmi almajiransa, da cewa; yanzu lokaci ne na Hujja, ba zagi ba. Karatu a bakin masu abin ya fi saurin ganewa. Ga nasiharnan kamar yadda take:


“Idan wani ya zana Malaminka, ya sa a ‘internet’, ya sa shi a sifar Biri ko Kare, ba kai kuma sai ka zana nashi Malamin ka ce; kai ma ka ce Malaminshi kaza ba ne, sai ka bar shi da abokanansa (masu zana Annabi a mummunan kama), ya nuna inda ya kwana. Duk wanda zai zana wani Malami, ko da wane ne Malamin, idan ba ka da ra’ayin Ibn Taimiyyah, ba za ka nuna shi a mummunan kama ba ne, za ka ce; Ibn Taimiyyah ya ce kaza, amma ba haka ba ne. Amma ba zagin shi za ka yi ba. Kowane ya ce kaza, ko ya fadi kaza, amma ba haka ba ne. Amma idan su wadannan suka zana Malaminku, a mummunan kama, ko suka zana Ayatullah suka yi mishi wani abu, kai kuma ba sai ka zana musu nasu Malamin haka ba, ka ga ka shiga sahunsu ke nan.”


 “wanda duk ya zana wani alamin addini a mummunan kama, to yana koyi da su Charlie ne (masu zana Annabi a mummunan kama) da wadanda suka ce; duk su Charlie ne, masu zana mutum su ce Manzon Allah ne, kuma su nuna shi a mummunar kama, koyi da su yake yi. Wannan ba lokaci ne na dan wane, mu ‘yan kaza ne, mu ba ‘yan kaza ba ne. 


Na’am ra’ayi na iya bambanta, amma mun yi ‘ittifa}i’ a kan cewa sunanmu Musulmi, sunan addininmu Musulunci. Idan wani ya fadi wata magana cikin addini, wadda kake ganin ba haka ba ne, kamar misalin da nake ba ku na yadda a cikin gida an kirkiro abubuwa a cikin addini, to ba zage-zage za mu yi ba. Idan na fadi magana, alal misali, na ce; Mu’awiyyah ya ce kaza, idan ba haka ba ne, sai ka kawo ‘proof’ ka ce; ba haka ba ne, ba ka zage ni ba. Ina da ‘proof’ dina ne. Na san cewa; su wadannan mulkin duniya suka kafa ba addini ba. Kuma sun san ma’abota addini na zamaninsu, kuma sun yi fada da su ne. Sun yi amfani da addini ne wajen kafa mulki. Su siyasa suka kafa dasisa a cikin addini. Kuma muna da ‘proof’ ne.” 


Ammar Muhammad Rajab ya nakalto muku daga jawabin da Shaikh Ibraheem Zakzaky ya gabatar a taron Maulidin Manzon Allah (saww) wanda ‘yan uwa na ‘Resource Forum’ suka shirya, kuma ya gudana a Husainiyyah Bakiyyatullah, Zariya. A ranar wata Asabar din 26 ga watan Rabi’ul Awwal, 1436.

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky