Tuna Baya: SAI YAUSHE LAUYA BAYERO DARI ZAI TUBA YA DENA KARE KARYA!?

 Tuna Baya: SAI YAUSHE LAUYA BAYERO DARI ZAI TUBA YA DENA KARE KARYA!? 


Ranar: 2-3 November, 1998 (13-14 Rajab, 1419H)


KOMAWA DA SU SHAIKH ZAKZAKY KOTU A KARO NA GOMA:


Ranar litini 2 ga Nuwambar 1998 ya kamata a cigaba da shari’ar su Shaikh Zakzaky tare da yan uwa uku; Alhaji Hamid Dallami, Malam Abubakar Almizan da Malam Shittu Muhammad wadanda gwamnatin Abacha ta kai kara tana zarginsu da laifin sun ce "Babu Hukuma Sai Ta Allah." amma sai ya zama ba a kai su kotun ba, ba a kuma yi zaman ba, sannan ba a fadi dalilin hakan ba.

 

Washegari Talata, 3/11/1998 sai aka kai su Malam din kotu da misalin karfe 11 na safe, amma sai 12:30 na rana Alkali Adamu Kafaranti ya shigo kotun. Nan mai gabatar da kara a ranar, Lauya Bayero Dari ya mike yace su ba a shirye suke da su cigaba da gabatar da karar ba, saboda babbar lauyar Gwamnati, Ann Ishaku ta bukaci ita ce za ta gabatar da karar ba shi ba, kuma wai bata da lafiya.


Bayero Dari yace, shi a matsayinsa na karamin lauya bai kamata ya cigaba da gabatar da wannan karan mai muhimmanci ba tunda akwai wacce ta fi shi. Don haka ya bukaci kotun ta sanya wata rana domin babbar lauyar ta samu zuwa ta cigaba da gabatarwa. 


Da Alkali ya waiwayi Shaikh Zakzaky don ya ji ko yana da abin cewa? Sai Malam (H) yace: “Da shi Bayero Dari, da matar da yace yana wakilta da wadanda suke ingiza su wadanda ba ma ganin fuskokinsu, duk suna wawaitar kawunansu ne!” 

 

Shaikh ya cigaba da cewa: “Ai farkon wannan shari’ar shi Bayero Dari ne ya rika gabatarwa, kuma idan yanzu bata nan ko kuma ta mutu shikenan sai a jira sai ta tashi ko ya za a yi?” Yace: “A tuna fa, wannan shari’ar ba wata mata ce take yi da mu ba, gwamnati ce take yi da mu, ba dole ne sai ita wannan matar ce kadai za ta wakilci gwamnati ba.”

 

Sai Alkali yace, ai ita ce babbar lauyar gwamnati. Sai Malam yace masa “To idan ta mutu fa ko ta cigaba da ciwon!?” Shaikh yaci gaba da cewa: “Idan su masu gabatar da karar ba su shirya ba, to su barmu a kurkuku sannan su zo da mu kotu a lokacin da suka shirya. Mu dama shekarunmu biyu da wata biyu a kurkuku.”


Jin wannan bayanan na Malam (H), sai jojin ya shiga rubuce-rubuce. Bayan ya kammala sai ya fara karanta abin da ke rubucen, yake cewa, wannan shari’ar an dade ana gabatar da ita, kuma duk lokacin da aka daga ta to an yi hakan ne bias bukatar masu gabatar da karar. Wannan ba daidai bane a bisa ma’aunin adalci saboda haka ya basu damar karshe daga wannan dagawar.


Sai Alkalin ya dage zuwa wata uku, ya sanya ranar 27 ga Junairun 1999 a matsayin ranar da za a komo kotun. A nan ma Malam Zakzaky y ace masa: “Wannan an yi rashin adalci domin kuwa mun dade muna hakurin sauraron kowane shirme da sakarci da suka gabatar a gaban wannan kotun, amma da lokaci ya zo d azan gabatar da nawa bayanin sai ya zama basu shirya sauraro ba? Sauraro ne kawai fa nasu, ni kuwa na riga na shirya abin da zan fada.”

 

Sai Alkalin yace “To ai za ka gabatar da naka jawabin kuma za su ji.”


Sai Shaikh Zakzaky yace “to ai ba lallai ne sai nan da wata uku ba, yana iya zama gobe.”


Alkali yace, “Ai gobe ina da shari’u da yawa.”


Shaikh yace “Jibi fa.”


Alkali yace “Shima ina da shari’u”


Shaikh yace “Gata.”


Alkali yace, “Ai gata Juma’a ce, kuma gajeruwar rana ce.”


Sai Shaikh ya kuma cewa: “Litinin.”


Alkali yace “ai zan koma sabuwar kotu ne.”


Sai Shaikh yace masa “Ai ba lallai bane, kana iya zama ka gama wannan shari’ar tunda kasa kakewa aiki.”

 

A nan sai Alkalin ya yi shiru. Sannan sai yacewa Malam Zakzaky, indai yana da wata rana wacce yake so shikenan, amma ba zai yiwu a wannan shekarar ta 1998 ba. Sai Malam yace masa “To ai wannan ya nuna al’amarin naku ne, mu bamu da ta cewa. Kana iya sa duk ranar da ka ga dama.”

 

Nan Alkalin ya tashi ba tare da ayyana wata ranar da za a dawo din ba.


A ranar Juma'a, 18 ga December, 1998 (29 Sha'aban 1419H), su Shaikh Zakzaky na zaune a kurkukun Kaduna suna shirin shiga watan Ramadan mai alfarma, sai ga shi an zo an nemi su shirya ba shiri za a je kotu. Ana zuwa kotu aka shiga Chambar Alkali aka sanar da su cewa gwamnati tace ta janye karar da take musu don haka an sallame su.


Malam Zakzaky yace ta janye? Aka ce? Yace me yasa? Alkali yace sun dai janye. Sai Malam yace ai da an cigaba don ya so ya ga karshen shari'ar, me zai sa su janye haka? 


Wani abin lura shine a tsawon lokacin da ake shari'ar Shaikh Zakzaky a lokacin Abacha, an shiga kotu ya fi sau 10, har sai da lauyoyin gwamnati suka gama gabatar da shedunsu kaf. A yayin da Shaikh Zakzaky za su fara gabatar da nasu bayanan na warware shedun gwamnati, sai gwamnatin ta ji tsoro ta sa aka rika ɗage-ɗagen shari'ar, a karshe ma ta ce ta janye karar tun bayan ritsawa da mataimakin kwamishinan yan sanda da Shaikh Zakzaky yayi da tambayoyi a kotu, wanda har a lokacin ACP Muktar ya kaɗa baki yace: "Malam Ibraheem in na amsa maka tambayin nan naka zan kafirta."


Ko kun san wannan Bayero Dari din da shi ke jan ragamar lauyoyin gwamnati wajen tuhumar Shaikh Zakzaky a kotu yanzu a 2020, shine wancan Bayero din da ke cikin lauyoyin da suke tuhumar Shaikh Zakzaky a lokacin Abacha a shekarar 1998?


— Yanki daga littafin "Muhimman Abubuwa 400 A Tarihin Harkar Musulunci Da Jagoranta." Na Cibiyar Wallafa Da Yada Ayyukan Shaikh Zakzaky (H).


Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky